HotBreaking News
Fetching data...

MATSAYIN CIN HANTA GA WANDA YAYI LAYYA

MATSAYIN CIN HANTA GA WANDA YAYI LAYYA. 

Abune sananne cewa an sunnantar ga duk wanda zaiyi layya da ya kame bakinsa tundaga fitowar ranar idi har zuwa yadawo daga idi sannan yaci wani abu daga naman layyarsa. Sai dai dayawa mutane suna daukan cewa sunna shine kawai cin HANTA na dabbar layyarsa, amma ahakikanin gaskiya ba haka al'amarin yakeba, abune take sunnah shine cin kowace irin tsoka ko gaba daga jikin dabbar layyar. 

      Wasu daga cikin malamai kamar Imam Shafi'i yana ganin mustahabbine cin hanta din saboda hadisin buraida da yake cewa 

"كان رسول الله صلى الله عليه وسلم إذا كان يوم الفطر لم يخرج حتى يأكل شيئا، وإذا كان الأضحى لم يأكل شيئا حتى يرجع، وكان إذا رجع أكل من كبد أضحيته"

 (manzon Allah ya kasance idan ranar idin azumine baya fita har sai yaci wani abu, amma idan ranar idin layyane to bayacin komai har sai ya dawo, idan ya dawo kuma yana cine daga hantar abun layyarsa).  Wannan shine hadisin da imam shafi'i yayi hujja dashi sai dai hadisine mai rauni (da'ifi). 

        Da wannan jumhur  na malamai suka tafi akan cewa kebance hanta da ci ga mai layya al'adace ba sunnah ba. Abunda yasa kuma ake yawaita cinta shine saboda saurin dafuwanta da nunanta.


TAMBIHI 


bawai ina nufin cewa duk wanda yaci hanta ya aikata bidi'a bane ko yayi laifi, a'a babu dayan biyu, domin itama gabace daga cikin gabobin dabbar. Abunda nake nufi da wannan rubutun shine wayar da kan yan uwa musamman wadanda ke ganin idan ba hanta yaciba tamkar baiyi layyaba, ko kuma duk wanda baici hanta ba kamar bayyi layyaba, wannan shine manufar rubutun. 



Julaibeeb 

20/8/2018

Continue reading...

MENENE HASSADA

*MINENE HASSADA, KUMA YA AKE HASSADA, KUMA SU WANENE MASU YIN HASSADA.*


1- Hassada wani mugun ciwo ne da ke Nukurkusar mai yinta a cikin zuciyarsa shi kadai. 


Hassada shine Jin Zafi, Daci, ko Bacin Rai a yayin da kaga wani Dan'uwanka, Makwabci, Aboki ko ma wani kawai da ka sani a duniya ya samu daukaka, ko wani iri.


Hassada kala uku ce (3)


A- Akwai jin kyashi, shine mutum yaji a zuciyarsa don me wani zai fishi wani abu a rayuwa. Kudi, Mulki ko kuma Baiwa ko Mukami. 


B- Mutum yaji shi bayason kowa ya samu wani abun alkhairi ko karuwa sai shi kadai.


C- Wannan shine yafi kowanne muni, wato mutum yaji cewa idan dai shi bazai samu abu ba to gara kar kowa ya samu.  Irinsu sune suke yin a fasa kowa ya rasa


2- Mutane da yawa suna fadawa cikin aikata Hassada ba tare da sun ankara ba misali:


A- Yawan yin magana akan ci gaban wani ko wata e.g 1- oh su wane an haye, sai kace da ba teburin mu daya ba a wajen aiki, lokacin nan kuwa kayansa basu wuce kala biyar ba.


2-  Mutum ya rinka gamin wane an samu shiga, ji wai yanzu shine kaza, sai kace ba tare aka daukemu aiki ba.


3- Dubi daga malami ya shigo aji sai ya fara wani iyayi wai shi a dole ga mai kwakwalwa


*YA ZA'AYI MUTUM YA GANE CIWON HASSADA YA FARA SHIGARSA*


Yanda mutum zai gane idan ya fara koyon Hassada shine:


A- Yawan damuwa da al'amarin wani ko wata, wanda kwata kwata bai shafeka ba ta ko wani hanya.

 

B- Damuwa da son sanin halin da wata ko wani yake ciki, idan kaji mummunar labari game da wani kaji dadi a ranka ko ma kayi dariya ko shewa, idan kuma kaji labari mai dadi game da mutum sai kaji ranka ya baci, ka kasa yi masa fatan alkhairi, ka fara jin tsoron kar ya wuceka a level na rayuwa. Sai ka fara kokarin kai sukarsa a wajen abokan arzikinsa, ko kokarin fadin miyagun maganganu game dashi, ko kuma fadin kalamai na batanci game dashi. Musamman ma idan ba'a tambayeka labarinsa ba, shine Hassada


4- lllolin Hassada suna da yawa amma ga kadan daga ciki:-


1- Hassada tana cinye kyawawan ayyukan mai yinta kamar yanda wuta take cinye karmami(Kirare/kara).


2- Hassada tana haifar da ciwon Zuciya da kuma Muni ga mai yinta.


3- Hassada tana hana mai yinta samun cigaba a cikin rayuwarsa da kuma duk abunda yasa gaba ba zaiga nasara bayyanan ne akai ba.


4- Hassada tana rage lmani kuma tana taimakawa wajen aikata Shirka da fita ma daga addini ba tare da mai yin Hassadar ma ya ankara ba.


5- Hassada shine kofa na aikata mafi yawancin manya manyan kaba'irai, kamar:


A- Gulma 

B- Munafunci

C- Makirci 

D- Rashin yadda da Kaddara 

E- Rashin hakuri 

F- Karya 

G- Yaudara e.t.c


*YA ZA'AYI KA KARE KANKA DAGA CUTAR HASSADA*


Yanda zaka kare kai daga Hassada shine yafi komai sauki, saboda ai yin Hassadar tafi wuya, takurawa kanmu mukeyi sai munyi Hassadar duk da mun san illarta da kuma nauyin Zunubinta.

 

1- Mutum yayi kokarin cire kansa akan duk wani al'amurran da basu shafeshi ba.


2- Mutum yayi kokari yayi focusing akan inganta rayuwarsa.


3- Kiyayewa daga kananan Gulmace-Gulmace. 


4- Son iyawa ko son bada shawara a inda ba'a nemi taimakonka ba.


5- Addua da yima zuciyarka addu'ar tsarkakuwa daga dukkanin miyagun ayyukan da ka iya gurbata ta.


Mutane da dama sukan tsinci kansu a cikin wani yanayi mai ban al'ajabi, za kaga mutum yana yawaita Azumi, Nafilfili, tsayuwar dare, Sallolin Farilla sam basa wuceshi amma sam baya cigaba a rayuwarsa, kodai yaci baya ko kuma kullum yana nan a inda yake, babban dalilin haka shine *"Zuciyarsa Baka ce"* sam babu alkhairi a mu'amalarsa da mutane, kullum ya bude bakinsa sai dai ya fadi Sharri ko ya kulla Makirci, ko kuma zargi akan abinda ba damuwarsa bace.


Sau da yawa za kaga mutumin Banza, Mashayi ko Mazinaci amma duk abunda yasa a gabansa zai samu, wani ma sam ko Sallah ba kullum yakeyi ba, amma da ya fara neman abu sai kaga ya samu, ba komai Allah ya keso ya nuna mana anan ba, illa, mu fahimci cewa shi Allah da Zuciyoyinmu yake aiki


Saboda haka da zarar mutum yayi Addu'a yayi Addu'a yaga ba'a amsa masa ba, to ya fara bincikar Zuciyarsa, Sannan kuma sai ya binciki Ayyukansa lallai  akwai inda yake da matsala.

Allah ya shiryar da mu.

Continue reading...

YAWAN ISTIGHFARI YANA MAGANIN MUNAFINCI

YAWAN ISTIGHFARI YANA MAGANIN MUNAFINCI


Wani mutun ya zo ga Huzaifata ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ,sai yace da shi;"Ya Baban Abdillah,ina tsoran kada na zama munafiki".

Sai Huzaifah yace dashi;

*"Shin kanayin sallar nafila idan ka kebe ka kadai babu wanda yake ganinka??kuma kuma kana yin Istighfar da tuba idan kayi zunbi??"*

Sai yace da shi;Eh.

Sai Huzaifa yace da shi

*"Ka tafi matuqar kana haka Allah bazai sanyaka ba cikin muna fukai ba"*

@ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ ‏( 1/167 )


Wani daga cikin magabata ya fadawa Malaminsa cewa;

"Ni ina yawan zunubi" sai yace masa to;

*"Ka riqa tuba idan kayi laifi"*

Sai yace"Sannan na sake komawa bayan na tuba"sai yace masa:

*"ka tuba*

Sai yace"Sannan na sake komawa bayan na tuba"sai yace masa:

*"ka tuba*

Sai yace"Sannan na sake komawa bayan na tuba"sai yace masa:

*"ka tuba*

Sai yace"Sannan na sake komawa bayan na tuba"sai yace masa:

*"ka tuba*

Sai yace duk lokacin da kayi zunubi to ka tuba,hakan yana sanya shaidhan baki ciki saboda zaka sami rahama Allah ta hanyar tubanka.

@ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ 492/7



Wani Mutum ya kai koke zuwa ga Imam Mujaahid ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ,sai yace;Ina yawan zunubi da aikata sabon Allah,wani magani zaka bani??

Sai yace da shi;

*"Ina ka manta da abinda yake wanke zunubai baki daya,ka yawaita tuba da istighfari*.

@ﺍﻟﺰﻫﺪ ﻟﻸﻣﺎﻡ ﺍﺣﻤﺪ 455



Imam Sa'ady ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ yana cewa:

*(Idan Allah ya yarda da bawa,sai ya karbi aikinsa duk kankantarsa,sai ya gafarta masa da gafara mai yawa saboda yawan istighfarinsa...."*

@ﺗﻴﺴﻴﺮ ﺍﻟﻠﻄﻴﻒ ﺍﻟﻤﻨﺎﻥ 48/1


Ibn Qayyim ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ yace:

*"Dukkan wanda yake da himma wajan yawan tuba da istighfari,hakika ya sami shiriya mai girma"*

@ﺍﻏﺎﺛﺔ ﺍﻟﻠﻬﻔﺎﻥ ‏( 954/2 )



Ibn Taimiya ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ yana cewa;

*"Sha'awa da fishi sune ma buden sabon Allah,amma istighfari da tuba sune kofar alkhairi duniya da lahira"*.

@ﺍﻻﻳﻤﺎﻥ 192



Ibn Aunin ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ yana cewa;

*"Yawan aiki baya nuna ka sami kubuta domin baka sani ba ko Allah ya karbi aiyukan ko bai karba,kuma kada ka kayi sakaci da zunubanka baka sani an gafarta maka ko ba'a gafarta maka ba,ka riqe ikhlasy a cikin aiyukan ka da Tuba da istighfari"*

@ﺍﻟﺘﻮﺑﻪ ﻷﺑﻦ ﺍﺑﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ‏( 73 )



*Allah ka bamu ikon tuba daga dukkan laifukanka tare da yawaita neman gafara wato istighfari*

Continue reading...
 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *