WANENE AL-HASAN IBN ALIY?
Al-Hasan Ibn Aliy Ibn Abi Dalib, Abu Muhammad, kuma jikan annabi (SAW), sannan kuma dan gaban goshinsa, kuma shine karshen khalifofi shiryayyu.
Ibnu Sa'ad yayi riwaya a cikin littafinsa "Addabaqat" daga Imran Ibn Sulaiman yana cewa: ﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ﺍﺳﻤﺎﻥ ﻣﻦ ﺃﺳﻤﺎﺀ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺠﻨﺔ، ﻣﺎ ﺳﻤﺖ ﺍﻟﻌﺮﺏ ﺑﻬﻤﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺠﺎﻫﻠﻴﺔ.
(Alhasan da Alhusain sunaye ne guda biyu cikin sunayen yan aljannah , larabawa basu taba saka wannan sunayen ba a jahiliyyah).
An haifi Imam Alhasan a tsakiyar watan Ramadan na shekara ta uku bayan hijirar ma'aiki (SAW). Yayi riwayah da yawa, kuma da yawa cikin sahabbai da tabi'ai sunyi riwayah daga gare shi, cikinsu akwai Nana Aisha(RA) da dansa -takwaransa- Alhasan, da Abul Haura'i, Rabi'ah bin Sunan, da Ash-sha'biy, da Abu Wa'il, da kuma Muhammad bin Siyrin.
Alhasan yana kama da Manzon Allah (SAW), kuma annabin ne da kansa ya rada masa wannan sunan, kuma ya yanka masa akikarsa ranar bakwansa, kuma ya aske masa gashin kansa, sannan yayi umarni da ayi sadaqah da azirfa gwargwadon nauyin gashin kansa, kuma shine mutum na biyar cikin Ahlul kisa'i.
Al'Askariy yana cewa: "sunan Alhasan ba'a san shi na a zamanim jahiliyyah".
Almufaddhil yana cewa: "Allah ya boye sunayen Alhasan da Alhusaini daga barin mutane (Basu iya sanin sunayen ba) har sai da Allah ya turo annabi sannan ya rada ma jikokinsa". Imamul Bukhariy yayi riwayah daga Ana's yana cewa: " Babu wani mutum da yafi kama da annabi cikin mutane kamar Alhasan bin Aliy".
Haka nan Bukhariy da Muslim sunyi riwayah da Nufai' Ibnul Harith (Abu Bakrah) yace: "Naji ma'aiki (SAW) yana kan minbari yana kallon Alhasan yana cewa:" Lallai wannan dan nawa shugaba ne, ta yiwu Allah ya sulhunta wasu jama'ah guda biyu masu girma cikin musulmi".
Imamul Bukhariy yayi riwayah daga Ibnu Umar yana cewa:" Annabi (SAW) yace:" Wadannan sune furanni na masu kamshi a nan duniya" (Ababan kauna) yana nufin Alhasan da Alhusain.
Imam Attirmiziy da Alhakim sunyi riwayah daga Abu Sa'id Alkhudriy yana cewa: "Manzon Allah (SAW) yace: " Alhasan da Alhusain sune shuwagabannin matasan aljannah ".
Imam Attirmiziy ya ruwaito daga Usamah dan Zaid yace: " Naga Annabi (SAW) a lokacin Alhasan da Alhusain suna kan cinyarsa yana nuna su yana cewa: "wadannan yayana ne guda biyu kuma yayan diya ta, ya Ubangiji tabbas ina sonsu ina rokonka ka sosu kuma ka kaunaci masoyinsu".
Haka nan Attirmiziy ya ruwaito daga Anas cewa an tambayi ma'aiki (AS) cewa:" wadanne kafi so cikin iyalanka? Sai yace:"Alhassan da Alhusain ".
Haka nan Alhakim yayi riwayah daga Ibnu Abbas yana cewa:" wata rana Manzon Allah (SAW) ya taho yana dauke da Alhasan akan kafadarsa, sai wani mutum ya hadu da annabi, sannan ya kalli Alhasan yace dashi :" Madallah da wanda kake kan kafadarsa. Sai Annabi yace da mutumin:"kuma madallah da shi da ya hau kafadar".
Ibnu Sa'ad ya kawo a cikin Addabaqat dinsa daga Abdullahi Ibnu Azzubair yana cewa:" wanda yafi kama da annabi cikin mutane kuma yafi soyuwa a wajen sa shine Alhasan dan Aliy, na ganshi yana zuwa a lokacin annabi yana cikin sujjadah sai ya hau bayan sa ko kafadarsa, ba zai daukar dashi daga kai ba, sai in shi ya ga damar sauka, hakika na taba ganin shi a lokacin Annabi yana ruku'i zai ware masa kafafun sa ya futo ta bayansa".
Kadan daga littafina mai taken (Ahlul baiti da matsayinsu)
Bunyaminu Ibrahim Abubakar
2nd Rabiul Auwal 1440 AH - 11st November 2018.
2 Comments