HotBreaking News
Fetching data...

YA SAKE MU SAKI DAYA, SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADONSA?

*YA SAKE MU SAKI DAYA, SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADONSA?* 

*Tambaya:*


Malam mutum ne yana cikin halin rashin lafiya, ya saki matansa har guda biyu saki daya, kuma bai dawo da su  ba har ya mutu, kuma ba su gama iddah ba, yaya za'a yi ? za su yi masa takaba, kuma suna da gadonsa, ko ko a'a ?


*Amsa:*


To dan'uwa mutukar yadda ka sifanta, haka abin yake, to za su bar iddar saki, su koma iddar mutuwa, kuma za su ci gadonsa, saboda suna nan a matansa, tun da saki daya ne, Ibnu-khudamah  ya hakaito ijma'in malamai akan  haka.


Don neman Karin bayani duba : Al-mugni 8\94.


Allah ne mafi sani .


9\5\2015

Amsawa: Dr Jamilu zarewa.

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *