HotBreaking News
Fetching data...

ZA MU IYA FATAUCIN FATUN JAKUNA!!

ZA MU IYA FATAUCIN FATUN JAKUNA!!

 Tambaya:
Assalamu Alaikum. Sheikh don Allah menene hukuncin siyar da FATUN JAKI a musulunci???
Ina da 'yan uwa da suke sayen fatun jaki ne a Taraba,suna kaiwa China. Shine nake son nasan hukuncin cinikin don nice mai bada jarin.
'Yar uwarku a Musulunci UMMU FATIMAH DARMA.
Amsa:
Wa'alaikum as salam, akwai zantuttukan malaman fiqhu da yawa game fatar dabbar da ba'a cin namanta idan ta mutu, saidai abin da yafi zama daidai shi ne: Duk fatar da aka jemeta to tabbas ta tsarkaka, kamar yadda hadisin da Muslim ya rawaito ya ambata hakan, don haka fatar jaki ana iya amfana da ita, kuma a sayar da ita mutukar an jeme ta jemewar da sharia ta yarda da ita.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *