HotBreaking News
Fetching data...

YA FURTA SAKI AMMA MATARSA BA TA JI BA?

*YA FURTA SAKI AMMA MATARSA BA TA JI BA?*


*Tambaya:*

Assalamu Alaikum; Mallam shin idan mutum ya furta saki ga matarsa ba ta jiba, ta saku?


*Amsa:*

To dan'uwa matar ta saku, saboda sanin an sake ta, ba shi daga cikin sharudan saki, mutukar miji ya furta saki, mace ta saku koda ba ta ji ba,  yana daga cikin ka'idoji a wajen malaman fiqhun musulunci: Duk wanda ba a damu da yardarsa ba wajen tabbatuwar abu, ba a damuwa da saninsa, yardar mace ba sharadi ba ce wajen zartuwar saki,  haka ma saninta an yi sakın ba sharadi ba ne wajen tabbatuwarsa.  


Allah ne mafi sani.


*Amsawa:*

Dr Jamilu Zarewa 

31/10/2015

Continue reading...

KOWA ANA MAGANAR SA A BAYAN IDON SA:

KOWA ANA MAGANAR SA A BAYAN IDON SA:

Yana daga dabi'ar dan adam yawan gaza gani, wato komi ya gani sai ya samu ta cewa. Wani ya fadi mai dadi, wani ko ya furta sharri.

Lallai akwai bukatar ka kiyaye daga yin abin dabai dace ba, kuma ka tsare harshen ka wajen aibata mutane da yiwa mutane mummunan ambato da mugun zato.

Ka sani kowane mutum da irin kallon da yake yi maka a rayuwa, wani na fadin alheri akan ka yana maka zaton alheri, wani ko akasin haka ne tunanin sa da ambaton sa akan ka.

Wata rana wassu mutane 3 suna tafiya a hanya, sai suka hango wani mutum a gefen hanayar  yana tona rami:

1. Na farko yace " wancan fa ina tunanin kisan kai yayi (wani ya kashe) shine yake haqa rami zai rufe shi.

2. Na biyun  yace a'a " kudi ya tara, yazo zai gina rami ya 6oye .

3. Na ukun ya ce " duk kunyi kuskure " rijiya yake ginawa domin asha ruwa sadaka.

To kamar haka rayuwa take kowa da irin dubin da yake maka, da irin ambaton da yake yi akan ka. Komi nagartar ka wani yana dubin ka mutumin banza, wani ko ya dauke ka na kirki.

Dan uwa kada ka manta Allah shi kadai yasan haqiqanin yanda kake, don haka kar ka damu da zato, ambato ko tunanin da mutane za suyi maka, kai dai nemi yardar Allah.

Ka sani mutane basu iya amfanarwa basu iya  cutarwa, don haka yi qoqari ka gyara tsakanin ka da ubangiji. Wanda ya sami yardar Allah... Allah YANA gyara tsakanin sa da mutane.

Shi dan adam ba'a iyam-masa, ba'a iya burgeshi din-din, kai dai ka yi kokarin zama na Allah sai ka samu taimakon Allah da kariyar SA.

Alllah ya tsare mana imanin mu da mutumcin mu YASA mu gama lafiya, amin.

Sheikh  Aliyu Said Gamawa.

Continue reading...

’YAMMATAN DAJIN SAMBINSA, ZA’A IYA ZUBAR DA CIKIN DA SUKA DAUKO ?

*’YAMMATAN DAJIN SAMBINSA, ZA’A IYA ZUBAR 

DA CIKIN DA SUKA DAUKO ?*

*Tambaya

Assalamu alaikum Don Allah Shehi me za Ku ce game da yanayin mata masu ciki ta hanyar fyaden Yan Boko Haram, wadanda aka Kwato su a Sambisa. MUNA bukatar nusarwa a shariance game da me za a yi da cikkunansu. A zubar Ko a Bari. Idan za mu samu amsa a mafi kusancin lokaci za mu so haka.. Na gode.

*Amsa

Wa alaikum assalam To dan’uwa wannan mas’alar ta kasu kashi biyu :

*1.* Idan ya zama cikin na zina ba’a busa masa rai ba, kamar ya zama bai kai kwanaki 120 ba, to wannan malamai sun yi sabani akansa zuwa maganganu uku :

*A.* Wadanda suka tafi akan halaccin zubar da shi, saboda bai zama mutum ba, kuma in an haife shi zai zama aibi ga uwarsa, shi ma kuma ba zai yi rayuwa mai dadi ba.

*B.* Bai halatta a zubar ba, saboda Annabi s.aw. bai umarci Gamidiyya da ta yi zina ba, ta zubar da cikinta, cewa ya yi da ita : ta je ta haife, sai ta zo a tsayar mata da haddi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1696.

*C.* Akwai malaman da suka tafi cewa : idan fyade aka mata, za’a iya zubarwa, mutukar ba’a busa rai ba.

*2.* Idan ya zama bayan an busa masa rai, wannan kam bai halatta a zubar ba, saboda kashe rai ne, wanda bai ji ba bai gani ba, yana daga cikin manufofin sharia kiyaye rayuwar dan’adam

Zance mafi inganci shi ne bai halatta a zubar da cikin zina ba ko da ba’a busa masa rai ba, saboda hakan zai iya bude hanyar yaiwaita zinace-zinace, tun da za’a iya zubar da cikin ba tare da an shiga cikin kunci da kunyata ba, amma idan Fyade aka yi mata, ko kuma likita ya tabbatar da cewa za ta halakka idan ta cigaba da zama da cikin, to ya halatta a zubar a irin wannan lokacin .

Mutukar an busawa ciki rai bai halatta a zubar ba, ko da kuwa fyade ne .

Don neman Karin bayani duba Ahkamul-janin Fil-fiqhil Islamy na Umar Ganam

Allah ne mafi sani .

*Amsawa*

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Continue reading...
 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *