*YA FURTA SAKI AMMA MATARSA BA TA JI BA?*
*Tambaya:*
Assalamu Alaikum; Mallam shin idan mutum ya furta saki ga matarsa ba ta jiba, ta saku?
*Amsa:*
To dan'uwa matar ta saku, saboda sanin an sake ta, ba shi daga cikin sharudan saki, mutukar miji ya furta saki, mace ta saku koda ba ta ji ba, yana daga cikin ka'idoji a wajen malaman fiqhun musulunci: Duk wanda ba a damu da yardarsa ba wajen tabbatuwar abu, ba a damuwa da saninsa, yardar mace ba sharadi ba ce wajen zartuwar saki, haka ma saninta an yi sakın ba sharadi ba ne wajen tabbatuwarsa.
Allah ne mafi sani.
*Amsawa:*
Dr Jamilu Zarewa
31/10/2015
0 Comments