HotBreaking News
Fetching data...

KOWA ANA MAGANAR SA A BAYAN IDON SA:

KOWA ANA MAGANAR SA A BAYAN IDON SA:

Yana daga dabi'ar dan adam yawan gaza gani, wato komi ya gani sai ya samu ta cewa. Wani ya fadi mai dadi, wani ko ya furta sharri.

Lallai akwai bukatar ka kiyaye daga yin abin dabai dace ba, kuma ka tsare harshen ka wajen aibata mutane da yiwa mutane mummunan ambato da mugun zato.

Ka sani kowane mutum da irin kallon da yake yi maka a rayuwa, wani na fadin alheri akan ka yana maka zaton alheri, wani ko akasin haka ne tunanin sa da ambaton sa akan ka.

Wata rana wassu mutane 3 suna tafiya a hanya, sai suka hango wani mutum a gefen hanayar  yana tona rami:

1. Na farko yace " wancan fa ina tunanin kisan kai yayi (wani ya kashe) shine yake haqa rami zai rufe shi.

2. Na biyun  yace a'a " kudi ya tara, yazo zai gina rami ya 6oye .

3. Na ukun ya ce " duk kunyi kuskure " rijiya yake ginawa domin asha ruwa sadaka.

To kamar haka rayuwa take kowa da irin dubin da yake maka, da irin ambaton da yake yi akan ka. Komi nagartar ka wani yana dubin ka mutumin banza, wani ko ya dauke ka na kirki.

Dan uwa kada ka manta Allah shi kadai yasan haqiqanin yanda kake, don haka kar ka damu da zato, ambato ko tunanin da mutane za suyi maka, kai dai nemi yardar Allah.

Ka sani mutane basu iya amfanarwa basu iya  cutarwa, don haka yi qoqari ka gyara tsakanin ka da ubangiji. Wanda ya sami yardar Allah... Allah YANA gyara tsakanin sa da mutane.

Shi dan adam ba'a iyam-masa, ba'a iya burgeshi din-din, kai dai ka yi kokarin zama na Allah sai ka samu taimakon Allah da kariyar SA.

Alllah ya tsare mana imanin mu da mutumcin mu YASA mu gama lafiya, amin.

Sheikh  Aliyu Said Gamawa.

Load disqus comments

1 Comments:

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *