GANIN ALLAH A LAHIRA
Al-Imamu Muslim da wasunsa sun ruwaito hadisi daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “An tambayi Manzon Allah (SAW) cewa ko za mu ga Ubangijinmu a ranar tashin alqiyama? Sai ya ce: Shin kuna yin turereniya wajen kallon rana da rana tsaka sanda ba girgije? Sai suka ce: A’ah. Sai ya ce: Ko kuna turereniya wajen kallon farin wata a daren haskensa sanda babu girgije?. Sai suka ce: A’ah. Sai ya ce: “Na rantse da Allah wanda raina ke hannunsa ba za ku yi turereniya ba a wajen ganin Allah ba sai gwargwadon turereniyar da kuke yi wajen kallon wata ko rana. Sannan ya ce: [Ranar alqiyama] Allah zai gana da bawa, sai ya ce masa: Kai wane! Ashe ban girmama ka ba? Ashe ban ba ka shugabanci ba? Ashe ban ba iyali ba? Ashe ban ba ka damar sarrafa dawaki da raquma ba? Ashe ban ba ka damar zama jagora ba? Ashe ba kai ne ka ke dauke daya bisa hudun ganima ba? Sai [bawa] ya amsa da cewa: An yi haka. Sai [Allah] ya ce masa: To dama kana tsammanin gamuwa da ni? Sai [bawa] ya ce: A’ah! Sai [Allah] ya ce masa: ba ruwana da kai kamar yadda ka yi halin ko-in-kula da ni.
Sannan sai Allah ya gana da [mutum] na biyu, sai ya ce masa: Kai wane! Ashe ban girmama ka ba? Ashe ban ba ka shugabanci ba? Ashe ban ba iyali ba? Ashe ban ba ka damar sarrafa dawaki da raquma ba? Ashe ban ba ka damar zama jagora ba? Ashe ba kai ne ka ke dauke daya bisa hudun ganima ba? Sai [bawa] ya amsa da cewa: An yi haka. Sai [Allah] ya ce masa: To dama kana tsammanin gamuwa da ni? Sai [bawa] ya ce: A’ah. Sai [Allah] ya ce masa: ba ruwana da kai kamar yadda ka yi halin ko-in-kula da ni.
Sannan kuma sai Allah ya gana da [mutum] na uku, sai yai masa tambayoyi irin wadanda suka gabata. Sai ya ce: Ya Ubangiji! Na yi imani da kai, na yi imani da littafinka, na yi imani da manzanninka, na yi Sallah da Azumi da Sadaka. [haka] zai ta bayyana alherinsa gwargwadon iyawarsa. Sai [Allah] y ace: Anan ma karyar za ka yi?. [Sai Manzon Allah (SAW)] ya ce: Sa’annan sai a ce da shi: yanzun za a kawo shaidan da zai yi bayani akan ayyukanka. Sai [mutumin] ya fara tunani a zuciyarsa yana cewa: Oh! Ko waye zai zo ya ba shaida kaina? Daga nan sai a rufe bakinsa, kuma a ce da cinyarsa da namansa da qasusuwansa ku yi magana. Sai cinyarsa da namansa da qasusuwansa su yi magana su bayyana ayyukansa, [an yi hakan ne] don a kafa masa hujja. Wannan shine munafiki, wancan kuwa shine wanda Allah yai fushi da shi”.
Rubutawa: Dr. Kabir Asgar
0 Comments