HotBreaking News
Fetching data...

ILIMI BABBAR KYAUTA.

ILIMI BABBAR KYAUTA.


Minene Ilimi??

Ilimi a yaren Larabci yana nufin;-

*Sanin abu a yanda yake wanda ya kore jahilci da shakka,ilimi shine sanin abu na hakika wanda babu shakka ko jahilci,ilimi shine sanin abu wanda yake kore jahilci*.


Ilimi a ma'anar Shari'a shine:-

*Sanin Allah da Sanin Manzon Allah s.a.w da Sanin Addinin musulinci da dalilai*.


Ilimi shine gadon Annabawa,da Ilimine Allah ya daukaka Annabi Adam A.S da zuri'arsa akan Mala'ikun Allah da sauaran Halittun Allah baki daya.


*Ilimi shine farkon wahayen Allah ga Manzon Allah s.a.w sannan ilimi Shine gadon Manzon Allah s.a.w bayan rasuwarsa*.


♧الإمـام ابن الـقـيم رحمه الله:

Yana cewa;-

*"Ilimi gadone na Annabawan Allah,mafi girman wanda za'a gada sune Annabawa kuma mafi girman gado shine Ilimi domin shine abin gado daga Annabawan Allah*.


"Dukiya kuma gadone na masu kudi da masu mulki".


*Ilimi shi yake baima mi shi kariya,amma ita dukiya mai ita yake bata kariya,dan haka ilimi yana baka kariya,amma dukiya kai kake bata kariya*.


*Dukiya tana raguwa ne ta hanya bayar da ita da ciyar da ita,amma shi Ilimi duk lokacin da ake bayar da shi yake karuwa da daukaka da girma*.


*Mai dukiya idan ya mutu ya rabu da wannan dukiya domin ya bar wannan dukiya ga magada,amma ilimi yana bin mai shi zuwa karabi kuma yana nan yana ci gaba da gudana a bayana kasa har zuwa gobe alqiyama sannan ana ci gaba da rubuta masa ladar iliminsa*.


"Ilimi shi yake hukunci akan dukiya yanda za'a sarrafa amma dukiya bata hukunta ilimi".


*Allah yana bayar da dukiya ga kafiri da mai imani da wanda yake so da wanda ba ya so,amma Allah baya bayar da Ilimi sai ga wanda yake so kadai,da kuma mai imani da shi*.


*Da mai dukiya da mai milki da dukkan kowa yana zuwa ga Ilimi kuma yana buqatar ilimi fiye da dukkan komai,amma ita dukiya babu mai zuwa gareta sai mabuqata da masu karamin karfi*.

@مفتاح دار السعادة (٤١٣/١) ]


   Allah ne mafi sani.


*Allah ka bamu ilimi mai amfani*.

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *