ﺑِﺴْﻢِ ﺍﻟﻠّﻪِ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِ ﺍﻟﺮَّﺣِﻴﻢِ
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ،
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته,
*KI SO MIJINKI*
_'YAR UWA MATAR AURE_:
Ina so ki fahimci *_SO_* arayuwar aure,shine tsarkake niyyah,biyayyah da kuma nuna kauna,sannan gabatar da hakkin mijinki kafin naki, yin hakan ne zai sa shi ya girmamaki,kuma yayin da kuka samu sabani,sai kauna da fahimtar juna su maye gurbin sabanin.
Ki sani _er uwa_ hakika shi so dan musaya ne, _Ya nuna miki ki Nina masa_,kuma zuciyar mutum tana karkata zuwa Wanda ya nuna mata so yke kuma kulawa da ita,hakika Bawa miji kyauta _kamar ki sai masa agogo,hula etc_
da kiransa da sunan da yafi so, ko na soyayyah,bugu da kari da yawan yi masa murmushi,duk wadannan Abu buwan suna samar da soyayyar mace a wurin mijin ta.da kololuwar girma mawa,dadin da dawa su taimaka mata wajen dacewa arayuwar aurenta.
Ya kama ta miji ya zamo shine mafi soyuwa azuciyar matarsa,kuma ita ma macen ta zamo itace mafi soyuwa agurin mijnta,
An tambayi Manzo(S.A.W) wa yafi so sai yace: " _AISHAH_".
So shine dadin zama, Nuna kaunah ga mosoyi.jin kan juna,Rangwame, da yafiya, ba _S0_ bane kamar yadda masu wason kwaikwayo suke siffantashi a yanzu, da kuma marubuta littatafan soyayyah ,kaji ana siffanta saurayi kamar wani annabi daga cikin annabawa,ko wani mala'ika maku sanci, _sune basu da aibu_ har hakan yasa idan mace taga wani abu na aibu da bata so daga mijinta tayi tunanin lalata aurenta.....
Hakika wannan misalin ba abun samuwa bane aruyuwar duniya, ko wanne mutum yana da aibu amma ya ishi mutum abin alfahari a iya kididdige aibunsa,
Hakika duk matar da take so taso mijinta ta rinka yin bincike game da halayensa da siffofinsa kyawawa da kuma dabi'unsa abin yabo,domin Manzo(S.A.W)yayi mana nuni da hakan: _"Mumini bazai kyamaci mumuni ba,idan ya kyamaci wata dabi'arsa to zai so wata dabi'ar tashi"_.
Haka yake,yake wannan matar aure idan kin kyamaci wata dabi'ar mijinki to tabbas adabi'un nasa kuma akwai wadda kike SO,ki Kuma tuna abin da masu hikima suka ce: "```Yabar iyayensa da danginsa da abokansa bai yarda da wani a matsayin abokin rayuwa ba,ko mai debe masa kewa bayan ke Matar ```sa.
Kiyi bincike game da abinda zaisa ki so mijinki,
Har wa yau yana da kyau ki rika bashi labarin irin yadda kike sonshi, kina fada masa babu gurin waninsa a zuciyarki, kiyi tunani game da hanyar da zaki nuna masa yadda kike sonsa, Sai Allah Ya Taimaki Rayuwar Aurenku ki zamo masa nutsuwa kuma mai debe masa kewa kamar yadda *ALLAH*(S.W.A) ya siffanta: _"Yana daga cikin ayoyinsa ya halittar muku matayenku daga kawunannku domin kusa mu nutsuwa agare su ya kuma sanya kauna da jin kai atsakaninku hakika cikin haka akwai ayoyinsa ga mutane masu tunani"_ 30:21.
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
Zamu ci gaba insha Allahu
Rubutawa✍🏼
{-Aysha mika'il-Idris Bichi-}
Ummu Ammarah,
0 Comments