TAMBAYA
========
👇
Assalamu alaikum Malam, Dafatan kana lafiya, Tambayata itace menene ingancin koyar da 'yan mata daku ma matan aure ? Saboda wasu suna cecekuce akai. Allah ya'karama malam fasaha.
AMSA
======
👇
Koyar da matan Aure da wadanda ma ba matan aure ba, wannan wajibi ne, Sabida mata suna da bukatar ilimummuka ta fannoni da yawa, kamar hukunce-hukuncen jinin haila da jinin Haihuwa da ka'i'dojin zamantakewar Aure, da dai sauransu. Sabida idan bata San dokar aure ba a ilimance, kaima mijinta sai abinda ka gani.
Domin wata rana zaka iya samun wani namijin a tsakanin gidanka, idan kayi magana sai tace bata San cewar babu kyau ba, har ta bashi dama ya shigo cikin gidanka ba. Ko kaga ta fita da shigar banza, tab yadd wani zai iya tsaida ta a kan titi yana tsammanin ko Bazawara ce, domin tayi shigar da bata da bambanci da Bazawara ko budurwa, idan kayi magana sai tace bata San babu kyau ba.
Sannan manzon Allah saw shine wanda ya fara bude makarantar mata a gidan Ummu Waraka, Anan ne yake koyar da matan sahabbai irin abinda Allah madaukakin sarki ya sanar dashi.
Sabida haka, Namiji xai iya koyar da matan Aure da wadanda ma ba matan aure ba, hatta a irin wannan zamanin, indai An yarda da Kiyayewarsa da muru'arsa, da tsoron Allah da yake dashi, da kuma iliminsa, babu lefi ya koyar da matan Aure da wadanda ma ba matan Aure ba. Amma dai idan da Ace Akwai mata yan uwansu masu ilimin da bazasu Rena Su ba, kuma Su wadannan Malamai matan zasu iya jajircewa wajen koyar dasu, to anan sai muce, Wannan matar itace tafi chanchanta ta koyar da wadannan yan uwanta matan. Idan kuma babu, to anan ya zama larura Namiji ya koyar dasu. Kamar yadda ya zama Larura Likita Namiji Yasa hannunsa a farjin matarka, idan aka kaita Asibiti zaiyi mata wankin ciki.
Idan kuma shi Mijinta yana da Ilimin addini da kuma irin wannan jajircewar, to shine yafi chanchanta ya ware lokaci, ya zauna a gida ya koyar da matarsa, ta iya karanta Alqur'ani dai dai, tasan hukunce-hukunce, Wanda ya zama wajibi Akanta ta Sansu. Idan kuma baxai iya yin hakan ba, to ya zama wajibi ya kaita inda xa'a koya mata, Amma dai kar ya barta a cikin jahilci.
Allah shine masani.
1 Comments: