*_TAYA ZAKI MALLAKI ZUCIYAR MIJINKI_*?
ﺑِﺴْﻢِ ﺍﻟﻠّﻪِ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِ ﺍﻟﺮَّﺣِﻴﻢِ
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ،
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ
السلام عليكم ورحمة الله وبركاته,
Baza ka samu macen da tafi dacewa ba acikin aduniya sama da macen da ta mallaki xuciyar mijinta Wanda hakan ya bayyana a idonsa idon yana kallonta, ko idan yana magana _agane hakan_ hakan shi yke nuna tabbas ta mallake shi ta kuma mantar dashi ko wacce mace wadda ba ita ba,ta zamo sarauniya wadda take kai kawo tsakanin gidanta da zuciyar mijinta. _TAYA YA ZAKI ZAMA WANNAN SARAUNIYA_? TAYA ZAKI MALLAKE ZUCIYAR MIJINKI?
*_KI ZO MU TATTAUNA GAME DA YANDA ZAKI MALLAKI ZUCIYAR MIJINKI CIKIN SAURI_*
1⃣Ki tarbe shi yayin da ya dawo gida da murmushi mai daukar hankali, domin shi yafi cancanta daki yiwa murmushin. Hakika manzo (S.A.W)yace: _"yin murmushinka ga fuskar Dan uwanka sadaqa ne."_
2⃣Ki sa tufafin da mijinki yake so kiyi ado ki fesa turare( _kada idonsa yaga mummuna agurinki,kada ya ji daga gareki sai mafi kamshin turare)_.
3⃣Kada ki daga muryarki agabansa, ki tuna _(mafi munin sauti shine kukan jaki sbd da kararsa)_.
4⃣Kiyi kokari kuna tashi sallar dare lokaci zuwa lokaci,domin da hakan Allah zai haskaka rayuwar aurenku ya kuma infant at a da kauna da nutsuwa " _Ku saurara da ambaton Allah zuciya take samun nutsuwa_ 28:13
5⃣Kiyi kwadayin sabunta komai nki tunda ga kan kwalliyarki shigarki da magna _ba kullum kiyi ta magana DA salo daya😞ba_ domin yin hanka zaisa mijinki yaji kin ginshesa.
6⃣Ki yawaita rokon Allah (S.W.A) da yasa miki soyayyar mijinki,ya kuma sanya soyayyarki a zuciyar mijinki,domin zukata a hannu Allah suke _{Ya ubangijinmu ka bamu daga mazajenmu da zuri'armu sanyi idaniya_}.
7⃣Ki zamo masa kamar amarya ako wanne dare,kuma kada ki Riga sa bacci sai da larura.
8⃣Kada kiyi gangacin cewa a ko da yaushe shi zai fara nemanki _yin hkn kskure ne babba_.
9⃣ Ki kula masa da kayansa,ko da shi baya kulawa da hakan, ki taimaka masa gurin shiryawa , ta yadda zaki taimakesa gurin smun yabon mutane game da iya kwalliyarsa.
🔟Ki tsaya agabansa yayin da yake cire kayansa,da yi masa rakiya yayin fita daga gida.
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
Zamu ci gaba insha Allahu
Rubutawa✍🏼
{-Aysha mika'il-Idris Bichi-}
Ummu Ammar
0 Comments