HotBreaking News
Fetching data...

Wani Irin Maciji, Aka Hana Kashewa?

TAMBAYA 

=========

👇

Asslam alkm,  Mallam barka da rana,  tambaya na shine,  dangane da hadithin da yayi magana akan in maciji ya shiga gidan mutum kar ya kasheshi a rokeshi ya fita,  har zuwa kwana uku,  idan yaki sai a kashe shi,  

Shine nake son mallam ya mana karin bayani, ko akwai irin macicin da za'ayiwa hakan, dangane da yadda maciji yake da illah ga mutum. Allah ya saka da alkhairi. 




AMSA 

=====

👇

Tabbas hadisi ingantacce ya Nuna cewar manzon Allah saw yace. Idan dayanku yaga maciji a gidansa, kar ya kashe shi dan da nan, har sai yayi masa Wa'azi kamar Sau ukku, idan Anyi masa Wa'azi zai bar wajen, idan kuma bai bar gidan ba, to anan zaku iya kashe she. 

 Amma dai sai Anyi Bismillah kafin a kashe wannan macijin, Sabida Aljanu suna shiga jikin wannan macijin. Abubuwa guda hudu, ba'a kashe Su har sai anyi bismillah, Sabida Aljanu suna Rikida Su shiga jikinsu wadanan Abubuwan. 

 Wannan Abubuwan Sune maciji, Jaba, Bera da kuma Tsaka. 

 Sabida ya taba faruwa wani, sahabi a lokacin da ake Tonon KANDAK tare da manzon Allah saw, Sai wani sahabi ya nemi izinin manzon Allah saw cewar zaije gida ya dawo, sai manzon Allah saw yace dashi, ya dauki makami ya tafi dashi, yana zuwa gida sai yaga maciji ya fasa kai a cikin gidansa, yayi danin Saran mutum, sai wannan sahabi yasa wannan makamin da yake hannunsa, ya kashe wannan macijin, Ashe Akwai wasu macijan a gefensa, Dan da nan sai suma suka Kashe wannan sahabin, da labari yazo wajen manzon Allah saw akan Abinda ya faru, sai manzon Allah saw yace, Idan mutum yaga maciji a gidansa, kar ya kashe shi har sai yayi masa wa'azi sau ukku, idan bai bar gidan ba, Anan kuma zai iya kashe shi, sai manzon Allah saw yaci gaba da cewar, Shi wannan macijin, Asalin Aljani ne, Tinda ya kashe shi sai Yan uwansa shaidanu sukaji Haushin Abinda yayi na kashe musu Dan uwa, Dan da nan, shima suka kashe shi. 

 Sabida haka, anan ba'a ce Ga irin Macijin da za'a wa'azi ba, kowanne ma Ana masa Wa'azi kafin a kashe shi. 


Allah shine masani. 

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *