HotBreaking News
Fetching data...

ZAN IYA BADA KUDI SABODA A DAUKE NI AIKIN GWAMNATI ?

*ZAN IYA BADA KUDI SABODA A DAUKE NI AIKIN GWAMNATI ?*

*Tambaya*

Assalamualaikum, Malam barka da rana, Dan Allah ina da tambaya ne kamar haka: Malam ya halasta mutum ya bada kudi Dan aba shi aikin Gwamnati?

*Amsa*

Wa alaikum assalam, bai halatta ba, saboda irin wannan kudin ana bayar da shi ne saboda daya daga cikin abubuwa guda biyu:

*1*. Ya zamanto mai Neman aikin ya cancanta a dauke shi, sai kudin da ya bayar su zama kyauta ce ga jagororin daukar aikin, hakan kuma haramun ne kamar yadda hadisin Ibnul-lutbiyya wanda Bukhari da Muslim suka rawaito ya tabbatar.

*2*. Ya zama bai cancanta ba, sai kudin da ya bayar su zamo rashawa da kuma hanyar ha'inci da danne hakkin wadanda ya kamata a dauka, ha'inci da danniya kuma haramun ne.

Duk wanda ya kiyaye hakkin Allah, tabbas zai azurta shi ta inda ba ya zato, wanda kuma ya saba masa zai same shi a Madakata.

Allah ne mafi sani.

Amsawa *Dr. Jamilu Zarewa*

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *