HotBreaking News
Fetching data...

KYAKKYAWAN KARSHE

KYAKKYAWAN KARSHE

Kyakkyawan karshen dan adam shine mutum ya samu dacewa da aikata aiki mai kyau gab da karshen rayuwarsa sannan sai Allah ya karbi rayuwarsa bayan gama wannan aikin,ko yayi tuba ingantacce gab da rasuwarsa ko ya mutu yana aikata wani aiki mai kyau.

Daga Abi Umamah رضي الله عنه yana cewa,Manzon Allah ﷺya ce:-
*(Idan Allah yana nufin bawasa da alkhairi,sai Allah ya tsarkake shi kafin mutuwarsa)* Sai muka tambayi Manzon Allah ﷺ Minene tsarkake shi??? Sai yace:-
*(Sai ya datar da shi akan wani aiki mai kyau har zuwa ya karbi ransa akansa)*
@صححه_الألباني

        Allah ne mafi sani

*Allah ka sanya muyi kyakkyawan karshe ka sanya mu hadu da babban Masoyin mu Annabi Muhammad ﷺ a cikin aljanna,AMIN*.

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *