HotBreaking News
Fetching data...

Tambaya: Kudina Suna karuwa A jakata Alhali basu Kai Hakaba?

TAMBAYA
========
👇
Assalamu alaikum
Mlm y gida y aeki
: Daman tambayace zanyi ta wani abu da yake daure min kai ako dayaushe: Wato nakasance idan nasa kudi a jaka ta sai inga sun karu ko koma idan an bani canji sai inga ya qaru alhalin acan wurin da aka bani dai dai,ne ko kuma idan naje siyan abu bani da ishashshen kudin amma ina bude jaka ta sai inga kudin m harda saura: Abun tun baya damuna har y dawo yake damuna shine nake so inji y abun yake. Allah sakawa mlm d alkhairi




AMSA
=====
👇
 Tabbas hakan yana faruwa.
  Aljanu suna yiwa mutum irin wannan. Musamman ma mata.
 Mun taba samun case din wata mata da suke ajiye mata kudi, sai take dauka tana Amfanin gabanta dasu. Da tazo aure sai abin ya gagara, Aljanin yake cewa Wannan kudin da yake kawo mata ae sadakinta ne ya bata, kuma a yanzu haka ya Aureta Sannan babu mai rabata dashi, tinda ta amince ta zama matarsa, da taci Sadakinsa da baya amince ba, bazataci Sadakinsa ba.
 Sannan ya taba faruwa wani lokaci, wata Daliba ta, take gaya min cewar, taga kudi a cikin Akwatin kayan Sawarta, sai Nace ta kawo min kudin, da ta kawo, sai Mukaga kudin sababbi kakar, Muka sayi tabarmi da butochi muka Raba masallatai.
 Sabida haka, ki dena taba wannan kudin, ki sami wani malami mai Amana kina bashi kudin yana hidimar Addini dashi. Su masu kudin sai Allah yake kai musu ladan abinda aka Aiwatar, Sabida kudin ba nasu bane, dakkowa sukeyi a banki ko idan wani ya ajiye sai da dakko.

Allah shine masani.


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876
Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *