HotBreaking News
Fetching data...

WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA

*_WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA_*
*Tambaya*
Akaramakallah na ji an ce haramun ne a saki mace mai haila, to amma wani lokacin za ka ga kun samu rashin jituwa da matarka ta yadda baza ka iya jiran lokacin tsarkinta ba, to malam akwai wasu lokuta ne da aka halattawa mutum ya saki matarsa ko da tana haila?
*Amsa*
To dan'uwa tabbas Allah ya yi umarni da kar asaki mace sai tana da tsarki kamar yadda yake cewa "Idan za ku saki mata to Ku sake su afarkon iddarsu) ma'ana a tsarkin da baku take su ba, Addalak aya ta: (1) saidai akwai wurare guda uku da ya halattta a saki mace mai haila:
*1*. Idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila.
*2*. Idan ta yi hailar ne tana da ciki.
*3*. Idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, to anan ya halatta ko da tana haila, saboda Annabi (S.A.W) bai tambayi matar Thabit ba shin tana haila ne ko tana da tsarki, lokacin da zata yiwa mijinta kul'i, kamar yadda Bhukari ya rawaito ahadisi mai lamba ta: 5273.
Duba: Dima'uddaabi'iyya shafi na: 33.
In ban da wadannan wurare, to bai halatta a saki mai haila ba, kuma in har an sake ta, to sakin bai auku ba a wajen wasu malaman.
Allah shine mafi sani.
21/04/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

SHIN YA HALATTA NA TAIMAKAWA CRISTER DA JINI?

*_SHIN YA HALATTA NA TAIMAKAWA CRISTER DA JINI?_*
*Tambaya*
Assalamu alaekum! Malam dan girman Allah ko ya halatta mutum ya baiwa christa jini a asibiti, ganin cewar christan ya shiga wani hali kuma akwai sanayyah tsakanina da shi?
*Amsa*
To malam wannan mas'alar tana daga cikin mas'aloli sababbi wadan da ba'a san su ba a can baya, amma kuma Mujamma'u fiqhul-islamy da ke Makka a saminarsu ta takwas wacce aka yi a ranar 19-28 na janairun shekarar 1985, sun tabbatar da halaccin taimakawa crista da jini idan yana rashin lafiyar da ake bukatar hakan, mutukar ana zaman lafiya da shi, saboda hakan yana daga cikin tamakekeniyar da Allah ya yi umarni da ita, kamar yadda Allah yake cewa a cikin suratul-Mumtahanah aya ta: 8, "Allah ba ya hana ku ku kyautatawa kafiran da ba su yake ku ba" sannan hakan zai kara fito da alkairin da yake cikin musulunci, ta yadda wasu za su yi sha'awarsa.
Amma idan akwai yaki tsakaninsa da musulmai to bai wajaba a ba shi ba, sai in ya kasance ribatacce ne a tsakanin musulmai, ko kuma ana tunanin hakan zai iya jawowa ya shiga musulunci.
Allah ne mafi sani.
Don neman Karin bayani duba Fatawaa Nurun Aladdarb: 1/376.
10/02/2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

SUNAN ALLAH AKE SO KAFARA AMBATA LOKACIN DA KA TASHI DAGA BARCI

SUNAN ALLAH AKE SO KAFARA AMBATA LOKACIN DA KA TASHI DAGA BARCI

Babban guri da alfaharin Shaidhan da masu taimaka masa shine suga sun halaka dan Adam ya mutu ya shiga wuta kamar yadda suma suka halaka,Shiyasa yake bibiyayyar lokuta mafi tsada dan halaka dan Adam,kamar lokacin kwanciya barci ko lokacin tashi daga barci.

*SHAIDHAN YANA YIN KWALLI GUDA UKKU LOKACIN BARCINKA*

Annabi SAW yana cewa: *(Shaidhan yana yin kwalli guda ukku a daidai kan dan Adam lokacin da yake kwance yake barci,ko wane dauri yana rudarka da cewa akwai sauran dare mai yawa, amma idan ka ambci Allah lokacin tashi daga barci sai dauri daya ya since,idan kayi alwala sai wani daurin ya since, idan kayi sallah sai sauran dayan ya sinci sai ka wayi gari cikin nishadi da walwala da jin dadi, amma idan bakayi haka ba sai ka wayi gari cikin damuwa da kasala da bakin ciki)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ.

Imam Nawawy Allah yayi masa rahama yana cewa: "Abinda zahirin wannan hadisi yake nuna mana dukkan wanda bai hada wadan nan abubuwa guda ukku wato ambaton Allah sannan alwala sannan Sallah lokacin tashi daga barci, to yana cikin wadanda zasu wayi gari cikin bacin rai da damuwa da kasala".
 @ﺷﺮﺡ ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ( ٦٧ /  ).


Allah ka bamu ikon aiki da wannan sunnah.

Continue reading...

YA WAJABA CANJI YA ZAMA HANNU DA HANNU

*_YA WAJABA CANJI YA ZAMA HANNU DA HANNU_*
*Tambaya:*
Me ne ne matsayin kasuwancin da muke yi, zamu karbi dalar mutum bayan mun daidaita farashi, amma ba zamu bashi kudi ba har sai mun je mun sayar wa da namu customan kuma mun dora namu riban kuma mu zare ribar mu, sannan mu kawo wa mai dala kudin sa a kan farashin da muka daidaita da shi?
*Amsa*
To dan'uwa wannan nau'i na canji bai halatta ba a musulunci, saboda yana daga çıkın sharudan canji ya zama hannu-da-hannu, tsakanin abin da za'a canza da wanda za'a canzar, kamar yadda hadisin Ubadah mai lamba ta : 2978 a sahihi Müslim yake nuni zuwa hakan.
Don haka bai halatta ka amshi dalar mutum ba, in har ka san ba ka da nairar da za ka ba shi a lokacin, Bin shari'ar Allah yana sanya albarka a Kasuwanci.
Allah ne mafi sani
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.


Continue reading...

SUNNONI GUDA BIYAR A LOKACIN KIRAN SALLAH

*_SUNNONI GUDA BIYAR A LOKACIN KIRAN SALLAH_*

Mai gaskiya Yar' mai Gaskiya Nana Aisha Matar Annabi s.a.w Allah ya kara mata yarda tana cewa:
*"Yana cikin babbar Asara mutum yaji Ladan yana kiran Sallah,amma bai bi amsawa mai kiran Sallarba"*.

Ibn Qaiyim Allah yayi masa Rahama yana cewa:
*"Akwai sunnoni guda biyar tabbatattu lokacin kiran Sallah"*.

1-SUNNA TA FARKO-(1).
*"Amsawa mai kiran Sallah wato ka riqa fadar abinda mai kiran Sallah yake fada lokacin kiran Sallah"*.

DALILI AKAN HAKA
Fadar Annabi s.a.w:
(Idan Ladan yace
"الله أكبر الله أكبر".
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,sai dayanku yace:الله أكبر الله أكبر".
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,sannan idan Ladan yace:
"أشهد أن لا إله إلا الله"
"ASH'HADU AN LAA ILAHA ILLALLAH",sai yace
أشهد أن لا إله إلا الله"
"ASH'HADU AN LAA ILAHA ILLALLAH",idan ladan yace:
"أشهد أن محمدا رسول الله"
"ASH'HADU ANNA MUHAMMADAR RASULILLAH" Sai yace:
"أشهد أن محمدا رسول الله"
"ASH'HADU ANNA MUHAMMADAR RASULILLAH" idan Ladan yace:
"حي على الصلاة"
"HAYYA ALAS SALLAH" sai yace:
"لاحول ولا قوة إلا بالله"
"LAA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH",idan yace:
"حي على الفلاح"
"HAYYA ALAL FALAH" sai yace
لاحول ولا قوة إلا بالله"
_"LAA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH"_
 idan yace:
"الله أكبر الله أكبر".
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,sai dayanku yace:الله أكبر الله أكبر".
ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR,idan yace:
لا إله إلا الله"
"LAA ILAHA ILLALLAH",sai yace
لا إله إلا الله"
"LAA ILAHA ILLALLAH" wanda yace LAA ILAHA ILLALLAH" azuciyarsa ya shiga aljanna).
@رواه مسلم .

2-SUNNA TA BIYU-(2)
*"Yin Salati ga Annbi s.a.w bayan kare kiran Sallah"*.

DALILI AKAN HAKAN.
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(idan Dayanku yaji kiran Sallah to yafadi irin abinda mai kiran Sallah yake fada,sannan yayi Salati agareni,domin wanda yayi min salati guda daya Allah zai yi masa guda goma)*.
@رواه مسلم.

3-SUNNATA TA UKKU-(3)
*"Roqawa Annabi s.a.w WASIILA a wajan Allah ta hanyar karanta adduar da Annabi s.a.w ya koyar dan roqa masa WASIILA"*

DALILI AKAN HAKA
Annabi s. a.w yana cewa:
*(idan Dayanku yaji kiran Sallah to yafadi irin abinda mai kiran Sallah yake fada,sannan yayi Salati agareni,domin wanda yayi min salati guda daya Allah zai yi masa guda goma, Sannan ya roqa min WASIILA domin ita wani matsayine acikin aljanna,bata dacewa da kowa sai ga wani bawa daga cikin bayin Allah kuma ina Sa ran nine mai wannan matsayi Dukkan wanda ya roqa min wannan matsayin to cetona ya tabbata agareshi)*.
@رواه مسلم .

ADDUAR ROQAWA ANNABI S.A.W :-
(اللهم رب هذه الدعوة التامة ، والصلاة القائمة . آت محمدا الوسيلة ، والفضيلة ، وابعثه مقاما محمودا الذي وعدته)
*Wanda ya karanta bayan kiran Sallah citon Annabi s.a.w ya Tabbata agareshi ranar alqiyama)*.
@Muslim.

4-SUNNA TA HUDU-(4)
"Fadar:
"رضيت بالله ربا وبالإسلام دينا وبمحمد صل الله عليه وسلم رسولا ".
*"RADHEETU BILLAHI RABBAN WABIL ISLAMU DINAN WABI MUHAMMAD S.A.W RASULAN"*

DALILI AKAN HAKA
Manzon Allah s.a.w yace:
'(Wanda ya fada alokacin da yagama jin mai kiran Sallah:-*
(وأنا أشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له ، وأن محمدا عبده ورسوله . رضيت بالله ربا ، وبالإسلام دينا ، وبمحمد صل الله عليه وسلم رسولا).
*Wanda ya fadin wannann Allah ya gafarta masa zunubansa)*.
@رواه مسلم .

5-SUNNA TA BIYAR-(5)
"Mutum ya roqawa kansa Abinda ya so"

DALILI AKAN HAKA
Daga Abdillahi Dan Amru R.A yace:"Ya Manzon Allah Lallai Ladanai suna samun fifikon lada akan mu,Sai Annabi s.a.w ya ce:
*(Kuriqa fadar abinda yake fada lokacin kiran Sallah,idan angama kiran Sallah sai ku roki Allah za'a amsa maku)*.
@سنن أبي داود.

Annabi s.a.w yana cewa:
*(Adduar da akayi tsakanin kiran Sallah da Iqama ba'a mayar da ita"wato karbabbiya")*.
@الترمذي

Yan uwana muyi kokari wajan koyi da wannan Sunnoni da kiran yan uwa akan suyi aiki da ita dan mu kasance cikin masu koyi da bin Sunnar Annabi s.a.w na gaskiya.
@الوابل الصيب من الكلم الطيب ... ص 188


    Allah ne mafi sani


Continue reading...

GWARGWADON HALAYENMU GWARGWADON SHUGABANNINMU

GWARGWADON HALAYENMU GWARGWADON SHUGABANNINMU
Al-Imam Ibnul Qayyim yana bayanin hikimar Allah a cikin halittarsa da gudanarwarsa sai ya ce:
ﻭﺗﺄﻣﻞ ﺣﻜﻤﺘﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻓﻲ ﺃﻥ ﺟﻌﻞ ﻣﻠﻮﻙ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩ ﻭﺃﻣﺮﺍﺀﻫﻢ ﻭﻭﻻﺗﻬﻢ ﻣﻦ ﺟﻨﺲ ﺃﻋﻤﺎﻟﻬﻢ، ﺑﻞ ﻛﺄﻥ ﺃﻋﻤﺎﻟﻬﻢ ﻇﻬﺮﺕ ﻓﻲ ﺻﻮﺭ ﻭﻻﺗﻬﻢ ﻭﻣﻠﻮﻛﻬﻢ، ﻓﺈﻥ ﺳﺘﻘﺎﻣﻮﺍ ﺍﺳﺘﻘﺎﻣﺖ ﻣﻠﻮﻛﻬﻢ، ﻭﺇﻥ ﻋﺪﻟﻮﺍ ﻋﺪﻟﺖ ﻋﻠﻴﻬﻢ، ﻭﺇﻥ ﺟﺎﺭﻭﺍ ﺟﺎﺭﺕ ﻣﻠﻮﻛﻬﻢ ﻭﻭﻻﺗﻬﻢ، ﻭﺇﻥ ﻇﻬﺮ ﻓﻴﻬﻢ ﺍﻟﻤﻜﺮ ﻭﺍﻟﺨﺪﻳﻌﺔ ﻓﻮﻻﺗﻬﻢ ﻛﺬﻟﻚ، ﻭﺇﻥ ﻣﻨﻌﻮﺍ ﺣﻘﻮﻕ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﺪﻳﻬﻢ ﻭﺑﺨﻠﻮﺍ ﺑﻬﺎ ﻣﻨﻌﺖ ﻣﻠﻮﻛﻬﻢ ﻭﻭﻻﺗﻬﻢ ﻣﺎ ﻟﻬﻢ ﻋﻨﺪﻫﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻖ ﻭﺑﺨﻠﻮﺍ ﺑﻬﺎ ﻋﻠﻴﻬﻢ، ﻭﺇﻥ ﺃﺧﺬﻭﺍ ﻣﻤﻦ ﻳﺴﺘﻀﻌﻔﻮﻧﻪ ﻣﺎ ﻻ ﻳﺴﺘﺤﻘﻮﻧﻪ ﻓﻲ ﻣﻌﺎﻣﻠﺘﻬﻢ ﺃﺧﺬﺕ ﻣﻨﻬﻢ ﺍﻟﻤﻠﻮﻙ ﻣﺎ ﻻ ﻳﺴﺘﺤﻘﻮﻧﻪ، ﻭﺿﺮﺑﺖ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺍﻟﻤﻜﻮﺱ ﻭﺍﻟﻮﻇﺎﺋﻒ، ﻭﻛﻠﻤﺎ ﻳﺴﺘﺨﺮﺟﻮﻧﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﻀﻌﻴﻒ ﻳﺴﺘﺨﺮﺟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻮﻙ ﻣﻨﻬﻢ ﺑﺎﻟﻘﻮﺓ، ﻓﻌﻤﺎﻟﻬﻢ ﻇﻬﺮﺕ ﻓﻲ ﺻﻮﺭ ﺃﻋﻤﺎﻟﻬﻢ .
ﻭﻟﻴﺲ ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻜﻤﺔ ﺍﻹﻟﻬﻴﺔ ﺃﻥ ﻳﻮﻟﻰ ﻋﻠﻰ ﺍﻷﺷﺮﺍﺭ ﺍﻟﻔﺠﺎﺭ ﺇﻻ ﻣﻦ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﻦ ﺟﻨﺴﻬﻢ .
ﻭﻟﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﺼﺪﺭ ﺍﻷﻭﻝ ﺧﻴﺎﺭ ﺍﻟﻘﺮﻭﻥ ﻭﺃﺑﺮﻫﺎ ﻛﺎﻧﺖ ﻭﻻﺗﻬﻢ ﻛﺬﻟﻚ، ﻓﻠﻤﺎ ﺷﺎﺑﻮﺍ ﺷﺎﺑﺖ ﻟﻬﻢ ﺍﻟﻮﻻﺓ . ﻓﺤﻜﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﺄﺑﻰ ﺃﻥ ﻳﻮﻟﻲ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﻓﻲ ﻣﺜﻞ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﺯﻣﺎﻥ ﻣﺜﻞ ﻣﻌﺎﻭﻳﺔ ﻭﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻌﺰﻳﺰ ﻓﻀﻼ ﻋﻦ ﻣﺜﻞ ﺃﺑﻲ ﺑﻜﺮ ﻭﻋﻤﺮ، ﺑﻞ ﻭﻻﺗﻨﺎ ﻋﻠﻰ ﻗﺪﺭﻧﺎ ﻭﻭﻻﺓ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻨﺎ ﻋﻠﻰ ﻗﺪﺭﻫﻢ، ﻭﻛﻞ ﻣﻦ ﺍﻷﻣﺮﻳﻦ ﻣﻮﺟﺐ ﺍﻟﺤﻜﻤﺔ ﻭﻣﻘﺘﻀﺎﻫﺎ
ﻣﻔﺘﺎﺡ ﺩﺍﺭ ﺍﻟﺴﻌﺎﺩﺓ ﻭﻣﻨﺸﻮﺭ ﻭﻻﻳﺔ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭﺍﻹﺭﺍﺩﺓ ‏( /1 253 - 254 )
"Ka lura da hikimar Allah Madaukaki ta sanya Shugabannin talakawa da Sarakunansu da Gomnoninsu gwargwadon halayen talakawan. Kai, kamar ka ce: aiyukan talakawa suna bayyana ne a kamannin Shugabanni da Gomnonin nasu. Idan talakawan sun tsayu a kan Addini sai Shugabannin su tsayu a kan dadai. In talakawan sun zama masu adalci a tsakaninsu sai shugabannin su yi musu adalci a cikin mulkinsu, in talakawan sun zama masu zalunci a tsakaninsu sai Shugabanni da Gomnonin nasu su zama masu zalunci. In makirci da yaudara sun bayyana daga talakawan sai shugabannin ma su zama haka. In talakawan sun ki bayar da hakkokin Allah da yake kansu (kamar Zakka da Sadaka) suka yi rowansu sai Shugabanni da Gomnonin nasu su hana su nasu hakkokin, kuma za su yi rowansu gare su. In talakawan suka yi kwacen abin da ba su cancanta ba daga masu rauni a cikinsu a cikin mu'amalolinsu, sai shugabannin nasu su kwace musu abin da shugabannin ba su cancance shi ba, su dora musu haraji (tax) da aiyukan bautar kasa. Dukkan abin da talakawan za su karba daga masu rauni daga cikinsu haka shugabannin za su karba da karfi daga wajen talakawan. Gomnonin talakawan sun bayyana ne bisa kamannin aiyukan talakawan.
Ba ya daga cikin hikimar Allah ya dora shugabanni ga mutanen banza fajirai face irinsu.
Yayin da farkon Muslunci suka kasance mafiya alherin al'umma mafi biyayya ga Allah sai shugabanninsu suka kasance irinsu. Amma yayin da suka jirkice sai shugabannin suka jirkice tare da su. Saboda haka hikimar Allah ta ki yarda shugabanni irin su Mu'awiya (ra) da Umar bn Abdil'Azeez (r) su zama shugabanninmu a wannan zamani, balle kuma irinsu Abubakar (ra) da Umar (ra)!
Kai, shugabanninmu za su kasance ne gwargwadon yadda muke. Haka shugabannin magabatanmu sun kasance ne gwargwadon yadda magabatan suke, duka wadannan nau'uka biyu shi ne abin da hikimar Allah take hukuntawa".
Da ma Allah ya ce:
{ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻟَﺎ ﻳُﻐَﻴِّﺮُ ﻣَﺎ ﺑِﻘَﻮْﻡٍ ﺣَﺘَّﻰ ﻳُﻐَﻴِّﺮُﻭﺍ ﻣَﺎ ﺑِﺄَﻧْﻔُﺴِﻬِﻢْ { ‏[ ﺍﻟﺮﻋﺪ : 11 ]
"Allah ba ya canza abin da ya samu mutane (na bala'i) har sai sun gyara abin da ke tare da su (na laifuka)".
In muna so shugabanninmu su zama masu adalci to mu ma mu zama masu adalci a tsakaninmu!
In muna so shugabanninmu su zama masu gaskiya da rikon amana to mu ma mu zama haka a cikin mu'amalolinmu na yau da kullum!
In muna so shugabanninmu su zama masu tausayin talakawa to mu ma mu zama masu tausayin raunananmu!
In muna so shugabanninmu su zama masu kyautata talakawa to mu ma mu kyautata wa junanmu!
Sai mun gyara kafin Allah ya canza mana.
Rubutawa: Dr. Aliyu Muhd Sani.

Continue reading...

HASSADA MUGUN CIWO

*_HASSADA MUGUN CIWO_*

   Darasi na Farko-(1)

▪Ma'anar Hassada a yaren larabci.
Hassada A Larabci:
*"Gurin gushewar ni'ima ko wata falala ko daukaka ko mutum yay asarar su ka riqa gurin da fatan hakan wannan shine Hassada a yaren larabci"*.
@[5197] ((القاموس المحيط)) للفيروزآبادي (ص 277)، ((تاج العروس)) للزبيدي (8/25).

*_MA'ANAR HASSADA A SHARI'A_*
1-الجرجاني:
Allah yayi masa Rahama yana cewa:
*"Hassada itace gurin gushewar wata ni'ima da Allah yayiwa wani ta dawo wajanka"*.
@[5198] ((التعريفات)) (ص 87). .


2-الكفوي:
Allah yayi masa Rahama yana cewa:
*"Hassada shine zuciyarka tariqa jin haushi ko damuwa ko kunshi saboda wata ni'ima ta dukiya ko yaya ko ni'ima ko falala da Allah yayiwa wani"*.
@[5199] ((الكليات)) (ص 408). .

3-الطاهر بن عاشور:
Allah yayi masa rahama yana cewa:
*"Kyamatar wata ni'ima da Allah yayiwa wani tare da gurin ni'imar ta gushe zuwa gareka ko zuwa gawaninka ko kuma a rasa baki daya....."*.
@[5200] ((التحرير والتنوير)) (30/629). .

▪BAMBANCI TSAKANIN HASSADA DA GHIBDHA WATO FATA

~الرازي:
Allah yayi masa rahama yana cewa;
*"Idan Allah yayiwa dan uwanka ni'ima, idan kayi guri da fatan wannan ni'imar da Allah yayi masa tq gushe ya yarasa ko ta dawo wajanka,ko kai Mai Hasaadane, amma idan fatan Allah ya baki irinta to kai Mai kyakkyawan fatane ba mai Hassada bane"*.
@[5202] ((مفاتيح الغيب)) (3/646). .

~ابن منظور:
Allah yayi masa rahama yana cewa:
*"Ghibdha wato fata mai kyau,shine mutum yaga wani cikin ni'ima mai kyau, sai yayi fatan Allah ya sanya shima ya sami irin wannan ni'ima,batare da gurin Allah ya gusar da ni'imar dan uwansa ba,idan ya roki Allah ya bashi irin ni'imar da Allah yayiwa waninsa to ya aikata abu  mai kyau kuma ya yarda da Qaddarar Allah,Amma shi mai Hassada yana fatane da guri ni'imar da Allah yayiwa wani ta gushe ko ta lalace ko ta dawo wajansa ko kuma duka su rasa,...."*.
@[5201] ((لسان العرب)) لابن منظور (7/359). .

An ambaci Ghibdha da ma'anar Hassada acikin Hadisi,kamar yadda yazo a Hadisin Abdullahi bn Mas'ud R.A yace Manzon Allah s.a.w yace:
*(Babu Hassada sai ga abu guda biyu, mutumin da Allah ya bashi dukiya sai yake amfani da wannan dukiyar wajan yiwa Allah dh'a da fitar da hakkin Allah acikinta, da mutumin da Allah ya bashi wata hikima ko ilimi sai yake kokari wajan aiki da ita da koyar da ita)*.
@[5203] رواه البخاري (73) ومسلم (316). .

Sai Imam Nawawy R.A ya fassara wannan ma'ana ta Hassada a wannan hadisin da cewa:
_"Shine yana guri da kyakkywan fata akan ni'imar  da Allah yayi waninsa shima Allah yq bashi irinta ba tare da gurin ni'imar da Allah yayiwa wanin ta gushe ba"_.
@شرح النووي على مسلم)) (6/97). .

     Allah ne mafi sani.

*Mu hadu a darasi na biyu insha Allah*

Continue reading...
 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *