HotBreaking News
Fetching data...

TAMBAYA DA AMSA

TAMBAYA

=========

👇

Salama alaikumu 


mal abokina sunce in tambayi ka ka basu amsa 1 a cikin azumi na Ramadan ɗin nan da ya wuce yayi wasa da gaban sa da safe sau 2 har maniyyi ya fito masa amma ya kame baice komai ba, har saida aka sha ruwa. yanzu kuma yayi nadamar hakan ya zai yi idan yayi niyar ramuwar su 




Diriba ne shi yana ɗaukar mutane zuwa wani gari ya kai su, kasuwa ko kuma garuruwan su da aka haifi su = wata rana ya tsanci kansa a halin babu. a cikin wan nan tafitafiyin da suke. daga cikin fasinjan da ya ɗauka a kan hanya sai suka buƙace su huta suka sauqo daga muta suka zauna = sai wani ya zuɓda kuɗin sa a cikin su . Shi kuma diriban yaga kuɗin ya ɗauka ya ɓuye kuma yaji mai kuɗin yana cigiya yanzu shima yayi nadamar hakan kuma abun ya faru ne a Nigeria yanzu kuma muna tare da shi a nan ƙasar Saudia yanzu yana so ya sauqi wan nan haƙƙin ya zai yi.




AMSA

======

👇

1. Abinda yake kansa anan shine, Zaiyi Ramuwar wannan Azumin guda daya, sannan yaci gaba da istigfari, domin Manzon Allah saw yace koda yayi Azumin shekara bazai biya masa wannan gibin Azumin da ya karya ba, tinda ba ta hanyar saduwa bane.

 Idan Allah ya gadama ya yafe masa, idan kuma ya gadama ya kama shi da lefin abinda ya aikata, domin akwai malaman da suke ganin ma ba wani Azumi da zakayi, suna ganin Wanda kaffara take kansa shine, wanda ya sadu da matarsa Da rana kuma da gangan Alhali yana Azumi. Domin shine aka sami Nassi sarihi daga Manzon Allah saw. 

 Wanda yake son Karin bayani ya duba littafin صحيه فقه السنة، zai sami karin bayani.

  

2. Yana faruwa Wani lokacin mutum ya aikata wani Abunda zaizo daga baya idan imani ya dawo masa yayi Nadama,  domin Barawo bashi da imani inji manzon Allah saw. Manzon Allah saw yace لايسرق السارف حين يسرق وهو مئمن، Wato Barawo bazaiyi sata ba A lokacin da yayi sata Alhalin yana da Imani, domin sai an cire masa rigar Imani zai aikata wannan Aika-Aikar. Idan Allah ya taimakeshi daga baya a dawmasa da rigar imaninsa, idan kuma ba haka ba, to a haka Zai mutu a matsayin maras imani.

   A yanzu Abinda yake kansa, dole ne kamar yadda imamunnawawiy yace, Zaiyi ردالمظالم، wato zai maida Zalinci ga wanda ya zalunta. 

  Zai maida wannan hakkin ne ga mai shi ta fuskar da ta dace.

  Ko dai ya nemi mai hakki ya maida masa hakkinsa (Zallar kudinsa), ko kuma yayi masa sadaka da Adadin kudin da ya dauka, Da niyyar Allah ya maidawa mai hakki hakkinsa. Nan gaba kuma kar ya sake.


Allah Shine Masani 


Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *