HotBreaking News
Fetching data...

AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA BARRISTER BULAMA BUKARTI YA AIKEWA DA KUNGIYAR IZALA TA JIHAR KANO (1)

AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA BARRISTER BULAMA BUKARTI YA AIKEWA DA KUNGIYAR IZALA TA JIHAR KANO (1)


Daga: Awaisu Al'arabee Fagge.

Shugaban Jibwis Social Media

Na jihar Kano.


Bismillahirrahmanirrahim.


Bayan haka, mun saurari wadansu tambayoyi guda 16 da Bar. Bulama Bukarti ya aikewa kungiyar Izala ta jihar Kano, da shugabanta, Dr. Abdullahi Saleh Pakistan, akan ziyarar da Kungiyar ta kaiwa Mai girma Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Hakan yasa muka dauki haramar mayar da amsoshi ga Bulama, domin ya waraka, kuma al'umar da suke da bukatar amsoshin da yayi suma su waraka.


 Amma kafin mu shiga bayar da amsa; muna da wadansu bayanai masu muhimmanci kamar haka:


1. Muna yabawa da godewa Bulama Bukarti, musamman yadda yayi amfani da usulubi da mai cike da girmamawa da mutuntawa ga shugabanmu, duk dayake baristan baya goyon bayan abinda shugaban namu yayi. Wannan abin a yaba ne. Mun gode.


2. Kasancewar Barista Bulama yace yayi tambayoyinsa ne ga Dr. Pakistan da kuma Kungiyar Izala Ta jihar Kano,  sai muka ga rashin dacewar shigowar Dr. Pakistan domin bayarda amsar, domin dalilai kamar haka:


  A) Barista bulama ya shigo ne bayan musayar sakonni tsakanin Dr. Pakistan da Dr. Gumi, kenan ba da shi akeyi ba, to bai dace ace Dr. Pakistan ne zai bashi amsa ba.


  B) Barista Bulama ya tura sakonsa ne a Social Media, Mu kuma mune muke magana da yawun kungiyar Izala a social media, kenan hurumin mu ne mayar da martani akan wannan batu, musamman dayake ni shugaban Social media din, da ni akaje waccan ziyara.


C) Dayake Bulama Bukarti lauya ne, nasan yana da masaniya akan cewa 'wani yakan iya kare hakkin wani, ya kan iya amsa tambayoyi a madadin wani, koda kuwa a fanni shari'a ne kotu'. Toh bukatar amsoshi ake, ko da daga bakin wanene, ba lallai sai Dr. Pakistan ba.


D) Ko da kasancewarmu ÿan social media bai bamu hurumin amsa wadannan tambayoyi ba, duk da haka akwai lemar da zamu iya fakewa, domin kuwa ni da nake rubutu, ina cikin EXCO na kungiyar izala a matakin jihar Kano, kuma tambayoyin da Barista yayi, yayisu ne ga Dr. Pakistan da kuma kungiyar Izala baki daya.


Da dan wannan tanbihi nake neman taimakon Allah wajen fara amsa tambayoyin Barista.


TAMBAYA TA FARKO DA KUMA AMSAR TA........


(Zamu tsaya anan, amma zamu cigaba anan gaba kadan, domin gudun yin rubutu mai yawan da zai wahalar da mai karantawa)


Awaisu Al'arabee Fagge.

Jibwis Social Media

Kano State.

26-11-2018

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *