HotBreaking News
Fetching data...

AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA BARRISTER BULAMA BUKARTI YA AIKEWA DA KUNGIYAR IZALA TA JIHAR KANO (2)

AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA BARRISTER  BULAMA BUKARTI YA AIKEWA DA KUNGIYAR IZALA TA JIHAR KANO (2)


Tanbihi:

1- Duk wanda bai karanta rubutun farko ba, to zaiyi kyau ya koma ya bibiya. Rashin bibiyar zai hanaka fahimtar sakon yadda yakamata.


2- Ban shardantawa kaina amsa tambayoyin Barista kamar yadda yayisu ba, saide zan fara dauko mafi muhimmanci daga cikinsu ne, koda ba dasu ya fara ba.


TAMBAYA TA DAYA: Menene hikimar kawo misalin Kazafin da aka yiwa Nana A'isha RA da Annabi Musa AS? Ko malam yana kamanta Nana A'isha  da Annabi Musa ne da Ganduje? Sannan hakan bai yi kama da abinda Malam Jafar yayiwa raddi ba a lokacin da aka kamanta jifan da aka yiwa Annabi SAW a Da'ef; da kuma wanda aka yiwa Atiku a Kano???


Amsa: Da farko dai muna cewa: أعوذ بالله من الشيطان الرجيم,  Allah ya tsari Dr. Pakistan da kamanta Annabi Musa da Nana A'isha da ganduje, nisan dake tsakaninsu yafi nisan sama da kasa. Haba mal. Bukarti! Ai koda an saba da Dr. akan ra'ayin siyasa ai ya kamata ayi masa kyakkyawan zato...


Sanannen abu ne cewar mutane sukan bawa junansu hakuri ta hanyoyi daban-daban, daga ciki, akan tunawa mutum wani abin damuwa ko matsala da ya samu wadanda suka fishi girma da matsayi.


Misali, Idan wani malamin yaje yayi wa'azi mutane suka ki karba, sai a bashi hakuri ace masa ka tuna cewa Annabi Nuhu ma yayi shekara 950 yana wa'azi amma mutane ÿan kalilan ne suka karba. Yayin da kake wannan misalin; babu wani mutum mai adalci da zai jefeka da cewar ka kamanta wannan malamin da Annabi Nuhu AS. (هذه بتلك ).


Wannan shi yasa ake yiwa wadanda suka gamu da bala'in rashin lafiya wa'azi da abinda ya sami Annabi Ayyuba,  ake yiwa wanda ya hadu da bala'in batan d'ansa wa'azi da abinda ya sami Annabi yaqub, ko ayi wa'azi ga wanda ya hadu da bala'in hassadar yan uwa da abinda ya sami Annabi yusuf... 


Bawai dan a kamantasu da wadannan manyan bayin Allah ba a'a saide don a rage musu radadin musifar da ta same su ta hanyar nuna musu hakan ya taba samun wadanda sukafi su daraja da alkhairi.


Shi yasa ko a lokacin da malam yake magana ya ce ai an tuhumci wadanda sukafi gomna daraja a wajan Allah da kuma wajan  duk wani musulmin kirki, dan haka kirkinka, ko tsoron Allahn ka bai iya hana a jefa maka tuhuma ko ta gaskiya ko ba ta gaskiya ba, dan haka babu laifi a musulunci idan wani abin damuwa ya sami mutun a bashi hakuri ta hanyar tuna masa abinda ya taba samun wanda ya fishi daraja mai kama da abinda ya sameshi.


Dangane da amsar Marigayi Sheikh Ja'afar Allah yayi masa rahama, ga wadanda suka fadi abinda suka fada gameda abinda aka yiwa Atiku, in Barista zai tuna abinda aka dinga fada wanda kuma Sheikh Ja'afar ya bada amsa a kai, abinda akace shine 'an jefi Atiku kamar yanda aka jefi Annabi, shine malam ya yi tir da waccan kamancceceiya da ya fahimta ana kokarin yi, tsakanin Annabi SAW da Atiku , wal-iyazu billah. Ala kulli halin, misalan da muka bayar sun isa su fayyace niyyar Dr. Pakistan a jawabin da yayi.


Zamu tashi a tambaya ta biyu nan ba da jimawa ba insha Allah.


Awaisu Al'arabee Fagge

Chairman Jibwis Social

Media, Kano State.

27-11-2018

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *