MUHIMMANCIN LOKACI A GURIN DAN ADAM
LABARIN WANI BAKAUYE MAI YIN SUU DA MATARSA
@ Wani bawan Allah ne yake rayuwa da matarsa a wani Kauye su biyu, Bashi da arziki wato talaka ne sosai kuma sana'arsa itace yin SUU, (wato kamo kifi).
@ Ranar nan ya tashi da safe matarsa take ce masa babu komai a gidan da zasu ci, shikenan yace mata bari yaje ya ga ko za'a samo wani abun. Ya dauki kayan SUU dinshi ya fita yaje yana kamo kifi, akayi rashin sa'a kifi
daya kawai samo a wannan rana, haka ya dawo gida ya bawa matar yace ta dafa musu shi su ci, tana cikin aikinsa sai ta ga wani abu mai sheki acikin kifi, ai kuwa sai ta sanar da mijinta. Da zuwansa sai yaga ashe Diamond ne suka tsinta acikin Kifin nan. Ai kuwa sai murna saboda kakarsu ta yanke saka.
@ Daga nan sai ya tafi cikin gari don ya sayar da wannan Diamond ko Gwal da suka tsinta acikin kifi shi da matarshi, duk inda yaje sai a rasa mai siya saboda kowa bashi da kudin da zai iya siyan wannan abu mai girma da daraja. Daga karshe aka kaishi gurin wani Attajiri wanda yafi kowa kudi a garin, shi ma dai yace masa bazai iya siya ba, sai dai a kaiwa sarki ko zai iya siya.
@ A kaje fada, aka nunawa Sarki, shima sarki yace ba zai iya biyan kudin wannan Diamond din ba ko Gwal, sai dai akwai wani daki na ajiya da ake ajiye duk wata dukiya ko kyauta ta Masarautar tun iyaye da 'ka'kanni kuma ba'a taba dauka ba, kullin dakin a rufe yake sai dai azuba a rufe. Sarki yace za'a bude maka wannan dakin ka shiga na tsawon awa 6 ka shiga ka dibi duk abinda yayi maka, amma sharadin shine idan awa Shida 6 tayi, zaka fito. Malam mai SUU yace ya yarda.
@ Mutumin ya shiga, shigarsa ke da yiwa, sai yaga wani lafiyayyen gado ga abinci kala kala an ajiye a gefen gadon, ai kuwa sai ya zauna yaci ya koshi, sai yace bari ya dan kwanta ya huta na tsawon minti 30 zuwa awa 1.
Idan ya tashi ai yana da sauran awa 5 da zai Debi duk abin da yake so. Ai kuwa kwanciyarsa ke da yiwa sai bacci ya kwashe shi, bai tashi farkawa ba sai ji yayi ana buga masa kofa ana cewa Lokaci yayi ya fito, sai ya tashi a firgice yana rokon a taimaka masa koda minti 1 ne a bashi don ya dauki ko da abu daya ne, amma ina fadawa suka ce A'a, ai ba haka akayi dashi ba......
haka ya fito bai dauki komai ba, yayi asarar Diamond dinsa kuma yayi asara bai fito da komai ba daga dakin ajiya .
@ DARASI @
@ Wannan Gwal ko Diamond da mutumin nan ya samu shine matsayin RAYUWA
@ Wannan Dakin da ya shiga shine matsayin DUNIYA
Wannan Kayan alato da gado da kayan mure rayuwa da ya gani sune KYALE KYALEN DUNIYA
@ Wannan Awa shida (6) da aka bashi shine ADADIN LOKACIN SA DUNIYA wanda ya nemi A kara masa koda minti 1 amma aka ce masa sam babu wannan zancen, to haka idan kazo mutuwa babu karin lokaci Allah yace: فإذا جاء أجلهم لا يستأخرون ساعة
@ wannan mutanen kuwa da suka zo fitar dashi daga wannan dakin sune MALA'IKU
@Kwankwasa kofa da yaji ana yi masa wannan MUTUWA CE
0 Comments