HotBreaking News
Fetching data...

SIHIRUL MAHABBA

MA'ANAR SIHIRUL MAHABBA:-

       Wani nau'i ne na sihiri da ake yi domin soyayya a :-

   1)- Saka soyayya tsakanin mutane guda biyu,misali tsakanin namiji da mace.

   2)- Saka soyayya tsakanin mutane da wasu abubuwa dabam wadanda ba mutane ba,

 

GAMAMMUN ALAMOMIN SIHIRI

   1)- Yawan ciwon kai 

   2)- Yawan ciwon mara(mafi yawancii bayan sallar la'asar ko cikin dare)

   3)- Yawan Yin Munanan Mafarkai(Kamar macizai,namun daji)

 

 

ALAMOMIN SIHIRIN MAHABBA(YAYA ZA'A GANE SIHIRUL MAHABBA)   

      1)- Tsananin soyayya,wadda ta faru kwatsam,wato asali ba soyayya tsakanin mutum ko mutane sai a ga sun fara soyayya,(Yana da kyau a ban-bance soyayya ta dan adam,)

      

      2)- Tsananin son saduwa zuwa ga abokin auraatayya(Wannan zai iya faruwa a dabi'ance sai dai sauran alamomi ne zasu banbance)

 

    3)- Gajen Haquri na rashin ganin masoyi/ya.

 

   4)- Yawan Mafarke mafarke akan dayan masoyi,(wanda ya wuce ka'ida)

   5)- Tsananin Biyayya ga daya daga cikin masoya(mutum kan sabawa iyayensa/ta don biyayya gareta/shi)

   6)- Tsananin kishi akansa/ta(Wanda hakan kansa mutum bazai iya nisantar ta/shi ba)

    

 

MATSALOLIN DA KAN AFKU WAJEN HADA SIHIRIN DAGA WURIN                                                     BOKA 

 

     1)- Zai iya juyawa zuwa ga tsananin kiyayya idan bokan yayi kuskuren hadawa.

     2)-Yakan shiga da karfi wanda hakan yakan sawa wanda akayiwa cuta ko ma ya karshi(domin wannan sihiri yakan canza zuciya daga kiyayya zuwa soyayya ne cikin kankanen lokaci)

    3)- Yakan juye zuwa son ko wane namiji/mace(mutum yaso ko wace mace har mahaifiyarsa/namiji har mahaifinta)

 

     HANYOYIN KARYA SIHIRUL MAHABBA

 

1- GAMAMMUN HANYOYI NA KARYA SIHIRUL MAHABBA

A)- Tsakake akida daga tsafi,layu ko guraye ,dolene mutum ya cire duk wani guri ko laya dake tare dashi.

B)- Mutum ya fahimci cewar duk abinda ya faru a gareshi daga Allah(SWT) ne da izninsa ya faru kuma yaso hakan ya faru shiyasa ya faru, Fadin Allah Q 2 Ch 102

C)- Kawar da duk wasu hotuna daga jikin bangon daki da kuma duk wani abu da yake da sura a jikinsa kamar posta d.s

D)- Dolene mace idan wanda zaiyi mata Ruqya Namijine ta sutuce jikinta da kaya masu rufe jiki gaba daya.

E)- Haqikance Labarin wanda abin ya afku akansa domin fara magani.

 

2)- HANYOYIN KARYA SIHIRUL MAHABBA ZABABBUN HANYOYI

RUQA

KAMAR HAKA:-

  KARANTA AL'QURANI MAI GIRMA

KA'IDA:

    A)- Dolene mutum wanda zaiyi ya kasance yana da tsarki kafin ya fara

    B)- Dukkan wadanda zasu kasance a gurin yana da kyau su kasance cikin tsarki saboda kar shi aljanin ya fita ya shiga jikin daya daga cikin mahalartan.

   C)- Allah ne ke bayar da Lafiya ba mai karatun ba.

GABA DAYAN AL'QURANI KARIYA NE , Amma wadannan suna daga cikin surori da Ayoyin da aka fiya amfani dasu:-

a)- Suratul Baqara : Ayata 1-4,Aya 102,Ayata 164,Ayata 256, Ayata 285-286.

b)- Suratul Al-imran :- Ayata 17-18.

c)- Suratul A'araf :54-56, Ayata 117-122(ana maimaita wadannan ayoyi)

d)- Suratul Yunus :- Ayata 80-82(Ana maimaita wannan aya)

e)- Suratul Mu'uminun :- Ayata 115-118

f)- Suratul Saffat :- Ayata 1-10

g)-Suratul Daha :- Ayata 69(Ana maimaita wannan aya)

h)- Suratul sajadah: Gaba dayanta

i)- Suratul Ahqaf :- Ayata 29-32

j)- Suratu:- Rahman :Ayata 33-36

h)- Suratu Hashar :- Ayata 21-24

k)- Suratul Jinn :Ayata 1-9

l)- Suratul Nas,Falaq,Ikhlas.

 

WASU KA'IDOJI YAYIN KARATUN

1- Mai yin karatun zaisa Hannunsa akan goshin maras lapiyan,ko kuma ya riqe jijiyoyin hannunsa don kada aljanun su gudu.

2-Idan Kuna cikin yin RUQA sai shi maras lapiyan yafara qaqarin yin amai(Haraswa) to zaku tsaya da yin karatun ku karanta su wadannan ayoyin a cikin ruwa (za'a iya sa magarya a cikin ruwan) abawa maras lapiyar ya sha,Cikin Ikon Allah zai iya amayar da sihirin idan ya cine a cikin abinci/ko abin sha.

3-Idan kuma jikinsa yayi zafi matuqa sai a riqa shafa masa ruwan wannan addu'a wato ayoyin da aka karanta a cikin ruwan +/- Magarya.

4-Idan Aljanin yazo kuyi kokarin magana da shi kamar haka:

  @@ Ya ya sunanka/ki?

 @@ Addininka/ki

 @@ Yaya akayi ka shiga jikin ta/shi

@@ A ina aka binne sihirin d.s

5- Yana Da kyau mu fahimci cewar mafiyawancin aljanu suna da karya don haka ko da sun fadi sunan wani mutum cewar "wane ko wance ce/ne tayi ko yayi sihirin kada a dauki maganar sa ,ko rinjayar da maganar kawai akan inda aka binne sihirin don a toneshi domin karyashi.

 

YAYA ZA'AYI IDAN ALJANIN BAI FADI GURIN DA AKA BINNE SHI BA

1-Sai shi mai RUQA din da kuma Yan'uwan maras lapiyan su yanki wani lokaci cikin yini ko dare(hala ma kashi uku cikin dare) domin su roki Allah akan ya nuna musu gurin da aka binne wannan sihirin.

2-Yawan Karanta Aya 255, wato AYATUL KURSIYY Na kashe aljani da kuma tilasta musu fita daga jikin mutum.

 

WASU DOKOKI DA MUTUM ZAI KIYAYE BAYAN KARYA SIHIRIN

Haqiqa Yin Shiru wato kada mutum yayi ta fadi cewar an karya masa/ta sihiri na daga cikin abubuwan dake taimakawa ,domin fadiwa mutane zai iya kaiwa kunnen wanda yayi sihirin kuma zai iya Komawa ya sake maimaita wa.

1-Riko da sunnar Annabi(SAW)

2-Tsaftace abinci da abin sha(nema da cin halas)

3- Daina Jin kade-kade da wake-wake.

4-Daina sa matsatstsun kaya da kiyaye tsiraici.

5- Riko da Azkar na safiya da yamma.

6- Kwnaciya da Alwala.

7- Karanta Surori ko Ayoyin neman tsari a yayin kwanciya,

8-Nisantar Duk wasu hanyoyin sabon Allah(SWT)

9-Fara Cin Abinci da bismillah wannan kan karya sihiri idan an sakashi cikin abinci

10- Addu'oin fita da kuma shiga gida

11- Addu'oin Sa kaya ko kuma cre kaya

12- Addu'ar shiga bayan daki

 


 

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *