ASALIN BULLAR KUNGIYAR SALAFIYYUN A TAKAICE
Da'awar Shaikh Muhammad bn AbdilWahhab (r) ta zo ne a matsayin sabunta Da'awar Annabawa ta kira ga Tauhidi da kadaita Allah da bauta shi kadai, da nisantar shirka gaba daya. Kamar yadda Annabi (saw) ya samu Kuraishawa a kan bautar gumaka, ya kira su zuwa ga kadaita Allah da bauta, haka Shaikh Muh'd bn AbdilWahhab ya samu al'umma a Kasar Najadu da Hijaaz a kan shirka da bautar kabarbura, ya kira su zuwa ga Tauhidi da nisantar Shirka.
Don haka Da'awa ce da ta ginu a kan kiran al'umma zuwa ga komawa ga Musluncin farko, wanda Manzon Allah (saw) ya zo da shi; kadaita Allah da bauta da nisantar Shirka. Kuma ta ginu ne a kan Aqidar Ahlus Sunnati wal Jama'a, wato Aqidar da take cikin Alkur'ani da Sunna, wato tafarkin da Annabi (saw) yake kai shi da Sahabbansa, Salaf Magabata cikin Tabi'ai da A'imma suka bi su a kai, suka yi Ijma'i a kansa.
Kuma daga cikin abin da Aqidar Ahlus Sunna ta ginu a kai akwai Da'a wa Shugabannin Musulmai, sawa'un masu adalci ne ko azzalumai, da hakuri a kan zaluncin nasu, da rashin yi musu tawaye, matukar ba su zo da kafirci bayyananne ba.
Daga baya sai aka samu wasu kungiyoyi suka fara bulla a kasashen Larabawa bisa sabuba daban - daban, kamar mamayar Turawan Mulkin Mallaka, yaduwar Ilhadi da Almaniyanci, da mamayar Yahudawa ga Kasar Palasdinu, da Juyin juya halin Ayatullahi Khomaini a Iran, yakukuwan Kasar Afganista, da kuma yakin Saddam Hussaini na Iraq bayan ya mamaye Kasar Kuwait. Sai aka fara kafa kungiyoyin bisa manufofin yakar Turawan Mulkin Mallaka, da yakar Yahudawa da suka mamaye Kasar Palasdinu da nufin kwato Birnin Kudus, da kuma yakar Gomantoci da sunan yakar zalunci, da nufin dawo da Daular Muslunci.
Kungiya mafi girma da aka kafa bisa irin wadannan manufofi ita ce Kungiyar Ikhwanul Muslimuna a Kasar Masar, a karkashin jagorancin Ustaz Hasanul Banna, wanda asalinsa Sufiy ne Dan Dariqa. Ita wannar kungiya, kungiya ce da ba ta damu da kira ga Tauhidi da yakar Shirka da Bidi'o'i ba, kawai manufarta tara jama'a don kafa gomnati da cimma wadancan manufofi. Haka wannar kungiya ta yi tasiri a sauran kasashe, wanda daga baya aka yi ta samun kungiyoyi daban - daban da suka tasirantu da ita bisa munasabobi daban - daban, har aka samu kungiyoyin Khawarijawa masu fita daga al'umma gaba daya.
Duka irin wadannan kungiyoyi sun yi tarayya a manufar yakar Gomantocin kasashen Musulmai da sunan yakar zalunci, da nuna nufin gyara al'umma ta hanyar kawar da Gomnatoci da kafa tasu bisa tsarin Kungiyoyin.
Wannan ya sa aka samu jaddada Da'awa ta Salafiyya mai kalu-balantar irin wadannan Kungiyoyi, da kira ga lazimtar Jama'ar Musulmi da take karkashin shugabanci, da kiran al'umma zuwa ga lazimtar Aqidar Ahlus Sunna da ta kunshi riko da Tauhidi da Sunna da nisantar Shirka da Bidi'o'i da kungiyoyinsu, da hana tawaye wa shugabannin Musulmai, da rashin rarraba kan al'umma ta hanyar kafa kungiyoyi masu manufar Tawaye wa shugaba. Da'awar Salafiyya bisa wannan Manhaji shi ne abin da Malamai suke kai a Saudiyya, tun da ita ce dai Da'awar Shaikh Muhammad bn AbdilWahhab ta kira ga Tauhidi da Sunna da yakar Shirka da Bidi'o'i, da kuma hada kan al'umma a karkashin shugaban Musulmai ba tare da rarrabuwa kungiya - kungiya ba.
Amma sai dai daga baya kuma wasu daga cikin masu Da'awar Salafiyyar suka fara tsanantawa a kan sauran 'yan uwansu Ahlus Sunna mabiya wannar Da'awar ta Salafiyya, suka dawo suna suka da bidi'antar da su da fitar da su daga Sunna da koransu daga Salafiyya bisa kurakuran da ba su kai ga haka ba, da takaice Salafiyya da wani sabon manhaji, da mayar da ita kungiya ta Malami guda daya. Duka da sunan aiki da ilimin "Jarhi da Ta'adili" wanda Malaman Hadisi suke amfani da shi wajen tantance Hadisan Annabi (saw). Wannan Manhaji ya jawo rarrabuwar kan Ahlus Sunna masu Da'awar Salafiyya.
Wannan ya sa Manyan Malamai suka shagala wajen Nasiha da fadakarwa ga masu irin wannan sabon Manhaji, musamman Manyan Malaman nan uku:
1- Samahatus Shaikh AbdulAzeez Ibnu Baaz.
2- Babban Malamin Fiqhu Shaikh Muhammad Ibnul Uthaimeen.
3- Babban Malamin Hadisi Shaikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy.
Daga cikinsu har aka samu wadanda suka wallafa littatafai don kashe wutar wannar fitina da ta kunnu tsakanin masu Da'awar Salafiyya. Daga cikinsu akwai;
1- Babban Malamin Hadisi a Madina Shaikh AbdulMuhsin Al-Abbad Al- Badar, wanda ya wallafa littatafai har guda uku a kan wannar matsala:
(a) ﺭﻓﻘﺎ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺑﺄﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ
(b) ﻭﻣﺮﺓ ﺃﺧﺮﻯ ﺭﻓﻘﺎ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺑﺄﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ
(c) ﺍﻟﺤﺚ ﻋﻠﻰ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺘﺤﺬﻳﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﺑﻴﺎﻥ ﺧﻄﺮﻫﺎ
Wadannan littatafai ba su yi dadi ga masu Guluwwi a bidi'antarwa ba, wadanda suka mayar da Salafiyya a matsayin wata Kungiya ta wani Malami guda daya. Har yau suna matukar jin haushin littafi na farkon.
2- Babban Malami Muhaqqiq Shaikh Bakar Abu Zaid, wanda ya wallafa littafi mai suna:
ﺗﺼﻨﻴﻒ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻈﻦ ﻭﺍﻟﻴﻘﻴﻦ
Shi ma wannan littafi bai yi musu dadi ba.
Haka aka cigaba da samun littatafai da suke yakar wannan Manhaji na Kungiyanci da raba kan Ahlus Sunna da guluwwi a bidi'antarwa da sunan Salafiyya.
Sai aka samu:
3- Shaikh Muhammad bn Abdallah Al-Imam, wanda ya wallafa:
ﺍﻹﺑﺎﻧﺔ ﻋﻦ ﻛﻴﻔﻴﺔ ﺍﻟﺘﻌﺎﻣﻞ ﻣﻊ ﺍﻟﺨﻼﻑ ﺑﻴﻦ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ
Wannan littafi ya samu yabo daga Manyan Malamanmu, daga cikinsu akwai Shaikh Saleh Al- Suhaimiy, wanda ya ce: a wannan zamani ba a wallafa littafi kamarsa ba.
4- Shaikh Ibrahim Al-Ruhailiy, wanda ya wallafa:
ﺍﻟﻨﺼﻴﺤﺔ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺠﺐ ﻣﺮﺍﻋﺎﺗﻪ ﻋﻨﺪ ﺍﻻﺧﺘﻼﻑ ﻭﺿﻮﺍﺑﻂ ﻫﺠﺮ ﺍﻟﻤﺨﺎﻟﻒ ﻭﺍﻟﺮﺩ ﻋﻠﻴﻪ
Malaminmu ne a Jami'ar Madina da Masallacin Annabi (saw), amma sai da ta kai suna mu'amalantarsa mu'amala ta kafirai saboda tsananin guluwwi.
5- Daga karshe an samu Babban Malaminmu Shaikh Saleh Al-Suhaimiy ya wallafa littafi mai suna:
ﺗﻨﺒﻴﻪ ﺫﻭﻱ ﺍﻷﻓﻬﺎﻡ ﻋﻠﻰ ﺭﺃﺏ ﺍﻟﺼﺪﻉ ﻭﺍﻟﻮﺋﺎﻡ ﻋﻠﻰ ﻣﻨﻬﺞ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﻜﺮﺍﻡ
6- Kafinsa akwai littafin Shaikh Aliy Al-Halabiy Almajirin Shaikh Albaniy, wanda ya wallafa:
ﻣﻨﻬﺞ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ ﻓﻲ ﺗﺮﺟﻴﺢ ﺍﻟﻤﺼﺎﻟﺢ ﻭﺗﻄﻮﻳﺢ ﺍﻟﻤﻔﺎﺳﺪ ﻭﺍﻟﻘﺒﺎﺋﺢ ﻓﻲ ﺃﺻﻮﻝ ﺍﻟﻨﻘﺪ ﻭﺍﻟﺠﺮﺡ ﻭﺍﻟﻨﺼﺎﺋﺢ
To kasancewar wadannan littatafai da ire - irensu sun yi bayanin bacin Manhajin Kungiyar Salafiyyun shi ya sa 'Yan kungiyar suke matukar fada da kwadaitar da dalibai a kan karanta su.
Alhali duk wanda ya karanta wadannan littatafai zai fahimci bacin wannan Manhaji na Guluwwi a Bidi'antarwa da raba kan Ahlus Sunna da kungiyanci da sunan Salafiyya. Kuma duk wanda ya yi aiki da abin da yake cikinsu na bayanin gaskiya to ya rabu da Manhajin Kungiyar Salafiyyun tun daga farkonsa har karshensa.
Kuma har yau manyan Malaman Saudiyya tun daga kan "Hai'atu Kibaril Ulama'i" har kasa, suna gargadin Daliban ilimi da tsoratar da su ga wannan Manhaji na Kungiyanci da Guluwwi da raba kan Ahlus Sunna.
0 Comments