HotBreaking News
Fetching data...

DUK SABANIN DA YA KAI GA RABUWA DAGA JAMA'AR AHLUS SUNNA SABANI NE DA BA YA CIKIN ADDININ MUSLUNCI

DUK SABANIN DA YA KAI GA RABUWA DAGA JAMA'AR AHLUS SUNNA SABANI NE DA BA YA CIKIN ADDININ MUSLUNCI

Lallai idan muka nazarci nassoshin Shari'a za mu ga cewa; sabani a tsakanin mutane abu ne kaddararre, ba zai gushe a cikin 'yan Adam ba, Allah ya kaddara shi ne don ya jarabi bayinsa, don a tantance shaqiyyai 'yan wuta da masu rabo.

{ ﻭَﻟَﻮْ ﺷَﺎﺀَ ﺭَﺑُّﻚَ ﻟَﺠَﻌَﻞَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﺃُﻣَّﺔً ﻭَﺍﺣِﺪَﺓً ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺰَﺍﻟُﻮﻥَ ﻣُﺨْﺘَﻠِﻔِﻴﻦَ ‏( 118 ‏) ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﻦْ ﺭَﺣِﻢَ ﺭَﺑُّﻚَ ﻭَﻟِﺬَﻟِﻚَ ﺧَﻠَﻘَﻬُﻢْ ﻭَﺗَﻤَّﺖْ ﻛَﻠِﻤَﺔُ ﺭَﺑِّﻚَ ﻟَﺄَﻣْﻠَﺄَﻥَّ ﺟَﻬَﻨَّﻢَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺠِﻨَّﺔِ ﻭَﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﺃَﺟْﻤَﻌِﻴﻦَ { ‏[ ﻫﻮﺩ : 118 ، 119 ]

Sai Allah ya bayyana cewa; mutane ba za su gushe suna sabani ba, amma kuma sai ya kasa mutanen kashi biyu a bayan sabanin; wadanda Allah ya yi musu rahama, masu rabo kenan, da kuma wadanda zai cika Jahannama da su.

To amma Allah saboda rahamarsa bai sanya nau'in sabanin ya zama kashi daya kawai ba, saboda dabi'ar da ya halicci mutane a kanta tun asali, na ba za su gushe suna masu sabani a tsakaninsu ba, saboda haka ya sanya sabanin ya kasu kashi biyu;

1- Sabani da yake cikin Addini, wanda ba ya kaiwa ga gaba da kiyayya da kaurace ma juna da rabuwar kai, shi ne wanda ake komawa ga Qur'ani da Sunna don warware shi, kuma shi ne irin sabanin da ya faru a tsakanin Sahabbai.

Allah ya ce:

{ ﻭَﻣَﺎ ﺍﺧْﺘَﻠَﻔْﺘُﻢْ ﻓِﻴﻪِ ﻣِﻦْ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﺤُﻜْﻤُﻪُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ { ‏[ ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ : 10 ]

"Dukkan wani abu da kuka yi sabani a cikinsa to hukuncinsa yana wajen Allah".

Kuma ya ce:

{ ﻓَﺈِﻥْ ﺗَﻨَﺎﺯَﻋْﺘُﻢْ ﻓِﻲ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﺮُﺩُّﻭﻩُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝِ ﺇِﻥْ ﻛُﻨْﺘُﻢْ ﺗُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮِ ﺫَﻟِﻚَ ﺧَﻴْﺮٌ ﻭَﺃَﺣْﺴَﻦُ ﺗَﺄْﻭِﻳﻠًﺎ { ‏[ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 59 ]

"Idan kun yi jayayya a kan wani abu to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa in kun kasance kuna imani da Allah da ranar Lahira, hakan shi ne mafi alheri kuma mafi kyaun fassara".

2- Sabani da ba ya cikin Addini, wanda yake kaiwa ga gaba da kiyayya da kaurace ma juna da rabuwar kai, shi ne wanda yake abin zargi a cikin nassoshin Shari'a, wanda ake yinsa a bisa wata manufa ta daban, ba don Allah ba, sai don bin son rai ko neman biyan wata bukata ta abin duniya, ko biyan wata sha'awa da take cikin zuciya.

Allah ya ce:

{ ﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻓَﺮَّﻗُﻮﺍ ﺩِﻳﻨَﻬُﻢْ ﻭَﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﺷِﻴَﻌًﺎ ﻟَﺴْﺖَ ﻣِﻨْﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺷَﻲْﺀٍ { ‏[ ﺍﻷﻧﻌﺎﻡ : 159 ]

"Lallai wadanda suka raba Addininsu suka zama kungiya – kungiya ba ka tare da su a komai (Annabi (saw) ba ya daga cikin kowane bangare da ya rabe daga Jama'a, Annabi (saw) ba ya tare da su a komai)".

Al- Imamus Shatibiy ya naqalto wata magana daga wani malami inda ya ce:

ﻛﻞ ﻣﺴﺄﻟﺔ ﺣﺪﺛﺖ ﻓﻲ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺍﺧﺘﻠﻒ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻬﺎ ﻭﻟﻢ ﻳﻮﺭﺙ ﺫﻟﻚ ﺍﻻﺧﺘﻼﻑ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﻋﺪﺍﻭﺓ ﻭﻻ ﺑﻐﻀﺎﺀ ﻭﻻ ﻓﺮﻗﺔ، ﻋﻠﻤﻨﺎ ﺃﻧﻬﺎ ﻣﻦ ﻣﺴﺎﺋﻞ ﺍﻹﺳﻼﻡ، ﻭﻛﻞ ﻣﺴﺄﻟﺔ ﺣﺪﺛﺖ ﻭﻃﺮﺃﺕ ﻓﺄﻭﺟﺒﺖ ﺍﻟﻌﺪﺍﻭﺓ ﻭﺍﻟﺒﻐﻀﺎﺀ ﻭﺍﻟﺘﺪﺍﺑﺮ ﻭﺍﻟﻘﻄﻴﻌﺔ ﻋﻠﻤﻨﺎ ﺃﻧﻬﺎ ﻟﻴﺴﺖ ﻣﻦ ﺃﻣﺮ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻓﻲ ﺷﻲﺀ، ﻭﺃﻧﻬﺎ ﺍﻟﺘﻲ ﻋﻨﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﺘﻔﺴﻴﺮ ﺍﻵﻳﺔ .

ﻭﺫﻟﻚ ﻣﺎ ﺭﻭﻱ ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﻗﺎﻟﺖ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ " : ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺸﺔ، ﺇﻥ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻓﺮﻗﻮﺍ ﺩﻳﻨﻬﻢ ﻭﻛﺎﻧﻮﺍ ﺷﻴﻌﺎ، ﻣﻦ ﻫﻢ؟ ﻗﻠﺖ : ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﺃﻋﻠﻢ . ﻗﺎﻝ : ﻫﻢ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻷﻫﻮﺍﺀ ﻭﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﻀﻼﻟﺔ ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﻣﺔ " ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻭﻗﺪ ﺗﻘﺪﻡ ﺫﻛﺮﻩ .

ﻗﺎﻝ : ﻓﻴﺠﺐ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺫﻱ ﻋﻘﻞ ﻭﺩﻳﻦ ﺃﻥ ﻳﺠﺘﻨﺒﻬﺎ، ﻭﺩﻟﻴﻞ ﺫﻟﻚ ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ : } ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﻧﻌﻤﺖ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺇﺫ ﻛﻨﺘﻢ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﻓﺄﻟﻒ ﺑﻴﻦ ﻗﻠﻮﺑﻜﻢ ﻓﺄﺻﺒﺤﺘﻢ ﺑﻨﻌﻤﺘﻪ ﺇﺧﻮﺍﻧﺎ { ، ﻓﺈﺫﺍ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﻭﺗﻘﺎﻃﻌﻮﺍ ﻛﺎﻥ ﺫﻟﻚ ﻟﺤﺪﺙ ﺃﺣﺪﺛﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﻬﻮﻯ ..

ﻫﺬﺍ ﻣﺎ ﻗﺎﻟﻪ، ﻭﻫﻮ ﻇﺎﻫﺮ ﻓﻲ ﺃﻥ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻳﺪﻋﻮ ﺇﻟﻰ ﺍﻷﻟﻔﺔ ﻭﺍﻟﺘﺤﺎﺏ ﻭﺍﻟﺘﺮﺍﺣﻢ ﻭﺍﻟﺘﻌﺎﻃﻒ، ﻓﻜﻞ ﺭﺃﻱ ﺃﺩﻯ ﺇﻟﻰ ﺧﻼﻑ ﺫﻟﻚ ﻓﺨﺎﺭﺝ ﻋﻦ ﺍﻟﺪﻳﻦ

ﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ﻟﻠﺸﺎﻃﺒﻲ ‏( /3 169 – 170 ‏) ، ﺍﻟﻤﻮﺍﻓﻘﺎﺕ ‏( /5 163 - 164 )

"Dukkan wata mas'alar da ta faru a cikin muslunci sai mutane suka yi sabani a cikinta, amma kuma wannan sabani bai gadar da gaba da kiyayya da rabuwar kai a tsakaninsu ba, to mun san cewa; tana cikin mas'alolin Muslunci.

Dukkan wata mas'alar da ta faru ta bijiro sai ta samar da gaba da kiyayya da juya baya ma juna (kauracewa) da yanke alaka, to mun san cewa; ba ta cikin lamarin Addini a komai, kuma ita ce wacce Annabi (saw) yake nufinta a tafsirin ayar, a hadisin da aka ruwaito daga A'isha (ra) ta ce: Manzon Allah (saw) ya ce:

"Ya ke A'isha, wadanda suka raba Addininsu suka zama kungiya – kungiya su wanene su?".

Sai ta ce: Allah da Manzonsa ne suka sani.

Sai ya ce:

"Su ne ma'abota son rai, da ma'abota bidi'a, da ma'abota bata daga wannar al'umma". Hadisin ya gabata (sai dai bai inganta ba).

Ya ce: Don haka ya wajaba a kan kowane mai hankali mai riko da Addini ya nisancesu, dalili a kan haka shi ne fadin Allah (T):

{ ﻭَﺍﺫْﻛُﺮُﻭﺍ ﻧِﻌْﻤَﺖَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﺇِﺫْ ﻛُﻨْﺘُﻢْ ﺃَﻋْﺪَﺍﺀً ﻓَﺄَﻟَّﻒَ ﺑَﻴْﻦَ ﻗُﻠُﻮﺑِﻜُﻢْ ﻓَﺄَﺻْﺒَﺤْﺘُﻢْ ﺑِﻨِﻌْﻤَﺘِﻪِ ﺇِﺧْﻮَﺍﻧًﺎ { ‏[ ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ : 103 ]

"Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lokacin da kuka kasance abokan gaba, sai ya hada zukatanku, sai kuka wayi gari kuna 'yan uwan juna da ni'imarsa".

Saboda haka idan suka yi sabani suka yanke alaka hakan ya kasance ne a dalilin bin son rai da suka kirkira.

Wannan shi ne abin da malamin ya fada, kuma a bayyane yake cewa; Muslunci yana kira ne zuwa ga hadin kai da soyayya da tausayi da tausasawa, saboda haka duk ra'ayin da ya kai ga sabanin haka to ya fita daga cikin Addinin Muslunci".

Duba Al- li'itisam 3/ 169 – 170, da Al- Muwafaqat 5/ 163 – 164.

Saboda haka dukkan sabani da ya kai ga fitina da rabuwar kai sabani ne abin zargi, kuma ba ya cikin Addini, saboda da yana cikin Addini da bai kai ga rabuwar kai ba, saboda sabani na cikin Addini ba ya kaiwa ga raba kai, da gaba da kiyayya, shi ya sa aka samu Salaf; Sahabbai da Tabi'ai da A'imma sun yi sabani amma bai kai ga gaba da kauracewa da rabuwar kai ba.

Saboda haka, dukkan sabanin da za ayi a kan mas'aloli na Ijtihadi ko a kan Sunnoni Mustahabbai amma har ya kai ga rabuwar kai to ba ya cikin Addini, saboda an yi sabanin ne saboda bin son rai, ko neman abin duniya, ko neman biyan wata bukata da take cikin zuciya, in da don Allah aka yi da ba za a taba samun rabuwar kai da gaba da kaurace masallaci da makamancin haka ba.

Allah ya shiryar da mu ya yi mana afuwa.

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *