HotBreaking News
Fetching data...

DA 'DINA DA GOBE SAURIN ZUWA: SHEIKH ALIYU SA'ID GAMAWA ( HAFIZAHULLAH )

DA 'DINA DA GOBE SAURIN ZUWA: SHEIKH ALIYU SA'ID GAMAWA ( HAFIZAHULLAH )

Yau da gobe sannu a hankali sai an iso karshen komi da kowa bisa tsarin da Allah ya hukunta.

Don haka dan uwa da zaka yi hakuri in dai da tsawon kwana komi zai wuce, komi ka gaa ana yi wata rana sai labari. Duk abinda ke baka tsoro yau don kwarjinin sa ko girman sa wata rana shi zai baka tausayi. Haka nan wanda ka raina kake masa kallon kaskanci wata rana shi zai baka tsoro.

Mu sani komi tsawon inuwa rana zai cimmata, don haka kada ka bari wadata, ko malumta, ko mulkin duniya ko duk wata dama da ka samu a rayuwa ta rudeka har ka danne hakkin wani, ko kana cin mutumcin mutane ko uwa-uba kayi watsi da addini ta hanyar bijirewa dokokin Allah. ko kana zaluntar al'umma ko ka ha'inci jama'ar Annabi (ﺹ).

Masu magana na cewa mulki kamar kujerar aski ne, kana zaune ana yi maka ga wani na jira, in ma ba kowa a kusa to dai da an gama askin zaka tashi wani yazo.... in ko haka ne mike jawo dagewa da zakewar mutanen mu cikin son dauwama a mulki, ko kin yarda wani ma yazo ya gwada?

'Yan uwa ina mana nasiha da hakuri, bin abubuwa a hankali, da tawakkali, da tsayawa akan gaskiya. Hakika mulki da ikon komi na hannun Allah, kuma ba wadda naci da dageear sa zata mai iya samar masa abinda ba'a rubuta masa ba.

Mu sani wallahi ba'a yiwa Allah tilas, mulki na Allah ne, kuma yana baiwa wanda yaso a duk lokacin da ya hukunta. Abinso ga al'umma shine mu gyara halayen mu, mu tuba ga Allah, mu roki jinkan sa, mu nemi taimakon Sa, mu yawaita addu'a Allah ya bamu shugabanni na kwarai. Kullum ana samun shugabanni ke dai-dai da halayen jama'ar da akeb shugaban ta.

Tabbas kowa ka gani yau yana mulki to tabbas jiya ba shi bane, kuma yau da gobe  zamanin kowanni mai mulki zai gushe wani yazo. Pls muna hakuri da juriya gobe tana da saurin zuwa...!

Karshen al'amari dai kowa zai koma ga Allah, kuma za'a yi hisabi kan abinda kowa ya gabatar. ALLAH ya yafe mana laifukan mu yasa mu cika da imani, amin

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *