*FALALA GUDA 10 GA WANDA YA HARDACE ALQURANI MAI GIRMA.*
Hakika babu wani abu da zuciya zata hardace mafi falala da daukaka ta sami matsayi mafi girma kamar hardace maganar Allah ,alqurani shine yake raya zuciya ya sanya ta samu nitsuwa da rabauta anan duniya da lahira,hardace alqurani ba karamar falala bace da matsayi wanda babu wanda yashan iyakar falalar da matsayinsa sai Allah,amma ga kadan daga cikin falalar guda goma;-
*1-Allah yayi yabo na musamman ga bayinsa masu hardace littafinsa alqur'ani,sai Allah yace:*
( ﺑﻞ ﻫﻮ ﺁﻳﺎﺕ ﺑﻴﻨﺎﺕ ﻓﻲ ﺻﺪﻭﺭ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﻭﺗﻮﺍ ﺍﻟﻌﻠﻢ ).
*2-Ana daukaka daraja da matsayin wanda ya hardace alqurani acikin aljanna.*
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
((Za'ace ga ma'abucin alqurani karanta ka rera kamar yadda kake karantawa a duniya,domin matsayinka a aljanna yana tsayawa akan ayar karshe da ka karanta).*
@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .
*3-Ana sanyawa Mahardacin alqurani kayan ado na karama da yardar Allah agareshi.*
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Alqur'ani zaizo a ranar alqiyama,sai yace: ya Ubangiji kayi masa ado wanda ya hardaceni, sai a sanya masa kambi na Karama,sannan sai Alqurani yace,ya Ubangiji ka kara yi masa ado,sai a sanya masa kayan ado na karama,sai Alqurani yace ya Ubangiji ka yarda da shi,sai ace da mahardacin alquranin karanta ka rera kana da kyakkyawan aiki ga kowace aya).*
@ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .
*4-Mahardacin Alqurani yana tare da tawaga ta Mala'iku ma'abuta karamci da daukaka.*
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Misalin wanda yake karanta alqurani yana mai hardacesa, yana tare da tawagar Mala'iku Ma'abuta karamci da daukaka awajan Allah).*
@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .
*5-Wadanda sukayi kowa hardar Alqurani su sukafi cancanta da limanci a cikin al'umma.*
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Wanda zai limanci mutane shine wanda yafi so karatun littafin Allah......).*
@Muslim
*6-Mahardata alqurani sune ma'abuta kwamitin Shura"wato masu tattawa abinda za'a zartar ga al'umma".*
Daga Ibn Abbas R.A yana cewa:
*"Mahardata alqurani sune yan majalissar sayyadina umar kuma sune masu bashi shawara....".*
@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .
*7-Mahardata alqurani su ake fara gabatarwa awajan binnewa a qabari.*
Annabi s a.w ya kasance yana hada tsakanin mutum biyu a qabari ga wadanda sukayi shahada a yakin Uhudu,sai yace:
(Wa yafi yawan hardace surar alqurani?) Sai ya fara gabatar da shi acikin qabari".
@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .
*8-Mahardata alqurani sune mutanan Allah kuma zababbun bayinsa.*
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
(Lallai Allah yana da mutanansa zababbu daga cikin mutane, ma'abuta alqurani sune mutanan Allah zababbansu).
@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .
*9-Ku riqa girmama Mahardata alqurani saboda girmamasu yana cikin girmama Allah.*
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Lallai yana cikin girmama Allah girmama wanda yayi furfura daga cikin musulinci,da mahardacin Alqur'ani,wanda baya karkacewa da alquranin...... da girmama shugaba mai adalci).*
@ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .
*10-Wuta bata qona mahardata alqurani a ranar alqiyama idan sun mutu da imani.*
Manzon Allah s.a.w yana cewa:
*(Da alqurani zai kasance acikin wani abu to da wuta bata kona saba).*
@ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .
*Abinda ake nufi da ace akwai wani abu da yake tare da alqurani da wuta bata konasa ba saboda albarkar alqurani,to ina ga mai imanin da yake jibintar alqurani??.*
@ ﺍﻧﻈﺮ : ﻓﻴﺾ ﺍﻟﻘﺪﻳﺮ .
Wannan shine mafi fatan dukkan wanda ya hardace alqurani a zuciyarsa kuma ya mutu da imani wuta bazata konasaba.
@ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ - ﺍﻵﺩﺍﺏ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ .
Allah ne mafi sani.
*Allah ka sanyamu cikin bayinki ma'abuta alqurani da hardarsa da aiki da shi,kuma ka sanya mu cikin wadanda alqurani zai cece su a gobe alqiyama.*
0 Comments