*_SHIN JA'AFAR ASSADIQ DAN SHI'A NE?_*
*Tambaya*
Assalamu alaikum Don Allah malam wai Imamussadiq dan shi'a ne, kuma ba zan dau wani abu daga iliminsa, wanda nake da tabbacin gaskiya ne, na yi amfani da shi ba, dan yana dan shi'a?
*Amsa*
Wa'alaikum assalam To 'yar'uwa Ja'afar Assadiq ba shi da alaka da shi'a, yana cikin Ahlul-baiti, ya barranta kansa daga ayyukan shi'a a wurare da dama, ga abin da yake cewa akan mutu'a, "Ba wanda yake aikata mutu'a a cikinmu sai fajirai" duba biharul anwar shafi na 318 saidai yana daga cikin limaman shi'a guda goma sha biyu, wadanda suke riyawa, duk a cikin limaman guda goma sha biyu, babu wanda suka yiwa karya kuma suka kirkiri hadisai suka danganta masa kamar shi, wannan yasa sai manyan manazarta ne za su iya gano hadisan gaskiya daga na karya a cikin littattafan shi'a wadanda suke dangantawa wannan babban malami kuma jinin anabta, kuma hatta malaman shi'a sun tabbatar da hakan a maganganunsu, kamar yadda ahlussunnah suka tabbatar, ga wasu daga cikin bayanai akan haka:
*1.* Kisshi ya rawaito hadisi daga Yunus yana cewa: Na je Irak sai naga sahabban Ja'afar Assadiq sun taru, sai na ji hadisai daga wajansu bayan na gama ji sai na dauki littatafansu na je na nunawa Aliyu Arridha, (daya daga cikin Ahlul-baiti) sai ya musa da yawa daga cikin hadisan, ya ce ba zai yiwu ace Ja'afar assadiq ne ya fade su ba, sannan ya ce Abul-kaddab ya yiwa Ja'afar Assadiq karya, Allah ya tsinewa Abul-khaddab, kamar yadda ka gani haka almajiran Abul-khaddab suke shigar da karya a cikin littattafanmu, suna cewa Ja'afar Assadiq ne ya fada, don haka duk abin da suka gaya muku daga wajanmu kar ku amsa in har ba Qur'ani ba ne" Rijalu- Alkishhi 3\298.
*2.* Sannan Majlisi ya fada a cikin Bihar Al'anwar cewa "Abu-abdillah –wato Ja'afar Assadiq- yana cewa : Mutane sun zurfafa wajan yi mana karya" Bihar Al'anwar :2\246.
*3.* Ja'afar Assadiq yana cewa: "Allah ya jikan wanda ya sanyawa mutane son mu, bai yi abin da mutane za su ki mu ba, amma za ka ga daya daga cikinsu zai ji kalma daya a wajanmu, sai ka ji ya kara guda goma na karya" Al-kafy 8\192.
*WADANNAN DALILAI NE DAGA MANYAN LITTATTAFAN 'YAN SHIA WADANDA SUKE NUNA CEWA: 'YAN SHIA SUNA YIWA JA'AFAR ASSADIQ KARYA..*
Wannan yasa Ibnu Taimiyya yake cewa: "Babu wanda aka yiwa karya kamar Ja'afar Assadiq" Duba Minhaj assunnah 7\391
Saboda dalilan da suka gabata ina baki shawarar cewa kada ki dauki maganar da kika gani daga Ja'afar Assadiq a cikin littattafan shi'a ko kuma kananan littatafan Ahlussunah wadanda ake siyarwa a kasuwa, mutukar ba ki tabbatar da tabbatuwar malamin a ilimin sunna da sanin isnadi ba, saboda yawan karyar aka yi masa.
Allah ne mafi sani
12/12/2014
Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa
0 Comments