HotBreaking News
Fetching data...

MATSAYIN MALAMAI A CIKIN AL'UMMA

MATSAYIN MALAMAI A CIKIN AL'UMMA

Dr. Aliyu Muh'd Sani

Lallai kamar yadda kowa ya sani; Malamai suna da matsayi mai girma a cikin al'umma, su ne magada Annabawa, masana Addini, masu dauke da shi, kuma masu isar da shi da bayaninsa ga mutane, saboda haka wajibi ne mutane su so su, su girmama su, su jibince su, su taimake su a kan mabarnata masu kokarin rusa Addini da wasa da shi, da masu sukansu da aibanta su balle kuma zaginsu.

Allah Madaukaki ya ce:

{ ﻗُﻞْ ﻫَﻞْ ﻳَﺴْﺘَﻮِﻱ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻟَﺎ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ { ‏[ ﺍﻟﺰﻣﺮ : 9 ]

"Ka ce: Shin wadanda suke da ilimi za su daidaita da wadanda ba su da ilimi?".

Kuma ya ce:

{ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻳَﺨْﺸَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻣِﻦْ ﻋِﺒَﺎﺩِﻩِ ﺍﻟْﻌُﻠَﻤَﺎﺀُ { ‏[ ﻓﺎﻃﺮ : 28 ]

"Malamai ne kawai suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa".

Annabi (s.a.w) ya ce:

ﺇﻥ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﻭﺭﺛﺔ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ

"Lallai Malamai magada Annabawa ne".

Shaihul Islami yana bayanin matsayin Malamai da hakkinsu a kan Musulmai sai ya ce:

ﻳﺠﺐ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺑﻌﺪ ﻣﻮﺍﻻﺓ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻣﻮﺍﻻﺓ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻛﻤﺎ ﻧﻄﻖ ﺑﻪ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺧﺼﻮﺻﺎ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻫﻢ ﻭﺭﺛﺔ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ، ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺟﻌﻠﻬﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻤﻨﺰﻟﺔ ﺍﻟﻨﺠﻮﻡ ﻳﻬﺘﺪﻯ ﺑﻬﻢ ﻓﻲ ﻇﻠﻤﺎﺕ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺒﺤﺮ ﻭﻗﺪ ﺃﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﻫﺪﺍﻳﺘﻬﻢ ﻭﺩﺭﺍﻳﺘﻬﻢ ﺇﺫ ﻛﻞ ﺃﻣﺔ ﻗﺒﻞ ﻣﺒﻌﺚ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻌﻠﻤﺎﺅﻫﺎ ﺷﺮﺍﺭﻫﺎ ﺇﻻ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻓﺈﻥ ﻋﻠﻤﺎﺀﻫﻢ ﺧﻴﺎﺭﻫﻢ؛ ﻓﺈﻧﻬﻢ ﺧﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻓﻲ ﺃﻣﺘﻪ ﻭﺍﻟﻤﺤﻴﻮﻥ ﻟﻤﺎ ﻣﺎﺕ ﻣﻦ ﺳﻨﺘﻪ ﺑﻬﻢ ﻗﺎﻡ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺑﻪ ﻗﺎﻣﻮﺍ ﻭﺑﻬﻢ ﻧﻄﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺑﻪ ﻧﻄﻘﻮﺍ .

ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /20 231 - 232 )

"Ya wajaba a kan Musulmai su jibinci Muminai bayan jibintar Allah da Manzonsa kamar yadda Al- Qur'ani ya fada, MUSAMMAN MALAMAI WADANDA SU NE MAGADA ANNABAWA, wadanda Allah ya sanyasu a matsayin taurari da ake shiryuwa da su a cikin duhun doron kasa da cikin teku. Hakika Musulmai sun yi Ijma'i a kan shiriyarsu da iliminsu, saboda kowace al'umma kafin aiko Annabi Muhammad (s.a.w) malamanta su ne mafi sharrinta sai al'ummar Musulmai kawai, su kam Malamansu su ne zababbunsu, saboda su ne halifofin Manzon Allah a cikin al'ummarsa, masu raya abin da ya mutu na Sunnarsa, da su Al-Qur'ani ya tsayu kuma da shi suka tsaya, da su Al-Qur'a ya yi furuci kuma da shi suka yi furuci".

Saboda haka abin da muke gani na sukan Malamai masu raya Sunnar Manzon Allah (s.a.w) da zaginsu da aibanta su, musamman in ya zama daga wajen jahilai to ya fita daga fagen hankali.

Saboda haka, lallai hakkin malamai a kanmu shi ne; girmamawa da soyayya da jibinta tare da kare hakkinsu da matsayinsu daga mabarnata, masu nufin rusa Addini ta hanyar zubar da wadanda suke dauke da shi wato Malamai.

Allah ya kara daukaka Malamanmu na Addini, halifofin Manzon Allah wajen raya Sunnarsa.

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *