HotBreaking News
Fetching data...

SHIN WANDA YA YI SALLAH BABU ALWALA KAFIRI NE ?

*SHIN  WANDA YA YI SALLAH BABU ALWALA KAFIRI NE ?*


*Tambaya*


Assalamu Alaikum  dan'uwa kuma malamina ga tambaya naji wata fatawa wacce ba ni da ilimi akanta, wai idan mutun ya yi sallah babu Alwala wai hukuncinsa sai ya sake kalmar shahada ta shiga musulunci,  menene ingancin wannan maganar ? Allah ya taimaka Amiin.


*Amsa* 


Wa alaikum Assalam To malam wannan maganar ta shahara a  wajan mutane, saidai a wajan malamai yin sallah babu alwala ya kasu kashi biyu : 

Idan ya aikata, amma bai halatta hakan ba, ya san ba daidai ba ne, kamar ya aikata saboda  kasala, wannan kam bai kafirta ba, saidai ya aikata babban zunubi.

idan ya aikata yana mai halatta hakan, ko kuma saboda izgilanci ga addini,  sannan  ba jahili ba ne, ba shi kuma da wani ta'awili, tabbas wannan aikin kafirci ne, har ma malamai da yawa sun hakaito ijma'i akan kafircin wanda ya yi hakan, saboda akwai karyata shari'a  a ciki, da kuma wulakantata .

Allah ne mafi sani


Duba : Almajmu'u na Nawawi 2\84  da Minhajussunah 5\204.


*Amsawa*✍🏻


*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*


11/12/2014

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *