HotBreaking News
Fetching data...

ZAN IYA SALLAR NAFILA A LOKACIN TAFIYA?

*_ZAN IYA SALLAR NAFILA A LOKACIN TAFIYA?_*



                        *Tambaya:*

Assalamu alaikum, malam tambaya ta ita ce yaya hukuncin yin nafila yayin da mutum a halin tafiya wato yanayin kasaru, naji wasu malaman suna cewa ba'ayin nafila a yanayin kasaru don Allah malam ina bukatar amsa da gaggawa, nagode.



                           *Amsa:*

To dan'uwa abin da aka rawaito idan Annabi ﷺ ya yi tafiya, yana barin nafiloli, in ba wutiri da raka'atanil fijr ba, kamar yadda Ibnul-kayyim ya ambata a littafinsa na Zadul-ma'ad 1\456.


Wasu malaman suna ganin nafilolin da suke da alaka da sallolin farilla su ake bari, amma wadanda ba su da alaka da sallolin farilla kamar tsayuwar dare an iya yinta, an samu halaccin hakan daga Imamu Ahmad. Zadul-ma'ad 1\457.


Allah ne mafi sani


Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *