HotBreaking News
Fetching data...

KI ZAMO MAI TSAFTA

KIZAMO MAI TSAFTA


ﺑِﺴْﻢِ ﺍﻟﻠّﻪِ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِ ﺍﻟﺮَّﺣِﻴﻢِ

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ،

 ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ


السلام عليكم ورحمة الله وبركاته

KI ZAMO MAI TSAfta 

Mijinki yanason matarsa takasance mai tsafta kuma kyakkyawa,


 domoin shi (mijin)

idan ya fita yana ganin wasu al'amura na fitina da rudu awajen wasu mata.

kada shaidan ya rinjayeki er uwa matar aure game da mijinki ya hanaki kula dashi da tsaftar tsafta da kwalliya.


Ki zamo a gidanki ko da yaushe kamar amarya ta hanyar tsaftace gidanki da kawar da duk wani gashi da akeso ki kawar ta tsaftace jiki da ruwa domin Ruwa shine mafi kamshin turare,


 Abin rasawa kamar yadda wata Balarabiya tace da erta kafin ita kuma Allah ya sanar damu(Hakika Allah yana son masu tuba da masu tsarki)

qur'an(2:222.)


Daga nan Allah ya umarci mace tayi wanka bayanta gama jinin Al'ada kona haihuwa da gusar da warin  jini ta yadda mijinta bazai cutu da itaba,

barima inace miki er uwa:

Mala'iku ma suna cutuwa da abinda mijinki yake cutuwa dashi.


Saboda haka kiyi kwadayin abinda zaixo👇

@Kiyi wanka  na musamman musamman kafin ki kwanta.


@Ki kamsasa gurin baccinku.


@Kiyi amfani da abubuwan da mijinki yake so na daga kwalliya.


@Ki tsaftace tufadinki ki kuma kamsasa kayan.


@Lura da baki da kuma kamshinsa kiyi amfani da asuwaki ko man goge baki.


@Kawar da duk wani gashi na jiki kibar gurin da fitowar gashi agurin yake Ado.


@Ki ware turaren baccinki daban da sauran wanda zakisa ba lokacin bacciba ki zama mai sanyin kamshi ba mai hawa kaiba.


Sai dai ni er'uwa ba ina nufin ki nauyaya kafadar mijinki da abubuwa masu tsada bane ki daura masa abinda bazai' iyaba,

 awajen siyan kayan kwalliya da tufafi da kayan ado.


Barima kiyi kokarima ki zamo kyakkyawa kuma mai tsafta batare da kin dorawa mijinki avinda baxai'iyaba. 


KISSA DA KUMA ABIN LURA

Wani daga cikin malamai yana cewa:

Wani mutum yazo wajena yana so ya saki matarsa sai na tambatayeshi meye dalili da yasa xai saketa na ringa lallashinsa akan yayi hakuri kar ya saketa shi kuma yana kawo min dalilai masu yawa da yasa yake son sakinta dana takura mishima sai yace mini warin Jininta baya tafiya🙊

 ma'ana ko da yaushe yananan ko bayan ta gama al'ada.


Er uwa!Dazaki kamsasa jikinki da kuma kyawunki na zahiri (tsafta)suna tasiri a zuciyar mijinki kiyi kwadayi akan haka zaki mallaki zuciyar mijinki Insha Allah 😊.


سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.


Zamu ci gaba insha Allahu


Rubutawa✍🏼

{-Aysha mika'il-Idris Bichi-}

Ummu Ammarah,

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *