HotBreaking News
Fetching data...

BAYANIN JAHILCIN MASU SUKAN MALAMAN SUNNA DA CEWA; SU KHAWARIJAWA NE QA'ADIYYA

BAYANIN JAHILCIN MASU SUKAN MALAMAN SUNNA DA CEWA; SU KHAWARIJAWA NE QA'ADIYYA

'Yan Kungiyar Salafiyyun Masu guluwwi a Bidi'antarwa suna sukan Malaman Sunna suna Bidi'anar da su bisa shubuhar -wai- su Khawarijawa ne Qa'adiyya, wato Khawarijawa na zaune.

To abin da wadannan suke fada suke rubutawa kuma suke yadawa jahilci ne da shubuhohi ba ilimi da hujjoji ba. Saboda asali su ba su san menene hakikanin Khawarijanci ba!

A baya na taba yin posting na yi tambaya don a tattauna a kan mas'alar a Facebook, amma saboda su ba sa iya tattauna mas'aloli a ilmance, saboda rashin abin tattaunawar da rashin fahimtar maganganun Malamai, da rashin sanin Usul na mas'alolin Addini, da kuma abin da suke da shi na zafin kai da ruduwa shi ya sa ba a cimma buri ba.

Abun da suke zargin Malaman Sunna da shi shi ne inkarin munanan aiyuka ga shugabanni a bainar jama'a. To lallai wannan kuskure ne, saboda an samu Hadisi da Annabi (saw) yake umurni da yin Nasiha wa shugaba a sirrance. Saboda in ana yi musu Nasiha a bainar jama'a, to jama'a za su rena su, in kuma suka rena su to jama'a za su iya yi musu tawaye su ki bin dokokinsu, to sai a samu matsala da rashin zaman lafiya. Wannan kuwa zai sa a rasa Maslahar shugabanci, na haduwar al'umma karkashin shugabancin jagora guda daya, wanda zai daidaita lamura a samu zaman lafiya, don a zauna lafiya a samu damar bautar Allah Madaukaki.

To amma shin wannan shi ne Khawarijanci?!

A'a, ba shi ne hakikanin Khawarijanci ba, saboda Khawarijanci shi ne fita daga al'umma gaba daya da halasta jininta, da kuma daukan makami a kanta da kashe mutane.

Duk wanda ba shi da wannar Aqida to shi ba Bakhawarije ba ne.

Annabi (saw) ne da kansa ya yi bayanin Khawarijanci inda ya ce:

" ﻭﻣﻦ ﺧﺮﺝ ﻋﻠﻰ ﺃﻣﺘﻲ، ﻳﻀﺮﺏ ﺑﺮﻫﺎ ﻭﻓﺎﺟﺮﻫﺎ "

"Duk wanda ya fita daga al'ummata, ya dauki makami a kanta yana kashe mutanen kirki da mutanen banza...".

Kuma ya ce:

" ﻳﻘﺘﻠﻮﻥ ﺃﻫﻞ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﻳﺪﻋﻮﻥ ﺃﻫﻞ ﺍﻷﻭﺛﺎﻥ ".

"Suna kashe Musulmai suna barin kafirai".

Shaikhul Islam ya ce:

" ﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺝ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻓﺎﺭﻗﻮﺍ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻭﺍﺳﺘﺤﻠﻮﺍ ﺩﻣﺎﺀ ﻣﻦ ﺧﺎﻟﻔﻬﻢ ."

ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /3 420 )

"Khawarijawa wadanda suke rabuwa da Jama'ar Musulmai, kuma suka halasta jinanen wadanda suka saba musu".

A wani wajen ya ce:

" ﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺝ ﺩﻳﻨﻬﻢ ﺍﻟﻤﻌﻈﻢ ﻣﻔﺎﺭﻗﺔ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻭﺍﺳﺘﺤﻼﻝ ﺩﻣﺎﺋﻬﻢ ﻭﺃﻣﻮﺍﻟﻬﻢ ."

ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /13 209 )

"Khawarijawa tushen Addininsu mafi girma shi ne rabuwa da Jama'ar Musulmai, da halasta jinanensu da dukiyoyinsu".

Saboda haka yaushe mutum zai yi zaton irin wannar Aqida ta halasta jinanen Musulmai gaba daya ga Malaman Sunna in ban da jahili dan zafin kai ba?!

To kasancewar su Khawarijawa masu irin wannar Aqida ta FITA DAGA AL'UMMA DA DAUKAR MAKAMI A KANTA DA HALASTA JININTA DA KASHE MUTANE BA JI BA GANI, SU KASHE MUTUMIN KIRKI SU KASHE MUTUMIN BANZA BABU BANBANCEWA, suna da Aqidar cewa; su ne kawai Musulmai, don haka garuruwa ko dazukan da suke zaune a cikinsu su ne KASAR MUSLUNCI (ﺩﺍﺭ ﺍﻹﺳﻼﻡ ), don haka garuruwan sauran Musulmai kuma garuruwan kafirai ne, sai suke kiransu da suna KASAR KAFIRCI ( ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻜﻔﺮ ), wannan ya sa suke wajabta wa mabiyansu hijira zuwa gare su, kuma suke haramta zama a cikin sauran al'umma da suka kafirta suka halasta jinanensu, to wannan ya sa mabiyansu suke yin hijira su bar cikin sauran al'umma su koma cikin 'yan uwansu Khawarijawa a garuruwa ko dazukan da suke zaune su kadai, - kamar dai yadda Boko Haram suka yi -. To duk wanda bai yi hijira ya koma cikinsu daga cikin masu irin Aqidarsu ba, wato wadanda suka ki yin hijira daga cikin mabiyansu, sukan zauna cikin mutane sauran al'umma suna da'awa da yada ra'ayoyinsu na Khawarijanci da Kafirta Musulmai gaba daya, to wadannan su ake kira KHAWARIJAWA QA'ADIYYA, ma'ana; wadanda suka zauna cikin al'umma ba su yi hijira sun koma cikin 'yan uwansu Khawarijawa a can inda suke zaune ba.

To Khawarijawa masu irin waccar Aqida da muka ambata ta halasta jinanen al'umma gaba daya, da daukan makami a kanta suna kashe kowa da kowa, amma kuma su ba su yi Hijira sun koma garuruwan 'yan uwansu Khawarijawa ko inda suke zaune a dazuka ba, su ake kira KHAWARIJAWA QA'ADIYYA.

To in ban da guluwwi da zafin kai na Kungiyar Salafiyyun ba, yaushe Malaman Sunnan da suke Bidi'antarwa suka kulla Aqida irin ta su Shekau a cikin zukatansu, amma ba su tattare sun koma Sambisa ba, kawai sun zauna ne a cikin al'umma suna kiran mutane ga Aqidar Boko Haram, balle har a kira su da Khawarijawa Qa'adiyya?!

Wannan wane irin jahilci da zalunci ne haka?!

Sa'annan in ban da jahilci ba, wa ya gaya musu Tawaye wa shugaba shi ne Khawarijanci?

Tawaye wa shugaba yana cikin Aqidun Khawarijawa amma ba shi ne hakikanin Khawarijanci ba. Na yi maka bayanin hakikanin Khawarijanci a sama.

Tawaye wa shugaba ba Khawarijanci ba ne kai tsaye, shi ya sa ake samun wadanda Malamai suke kira da BUGAAT, wato 'yan tawaye da suke da Tawili a kan Tawayensu wa shugaba.

Irinsu ne wadanda suka yaki Sayyidina Aliyu (ra) cikin Sahabbai, irin su A'isha (ra), Dalhat (ra), Zubair (ra), Mu'awiya (ra) da sauran Sahabban da suke tare da su. Da Hussain (ra) wanda ya yi tawaye wa Yazidu. Duka wadannan babu wanda ya taba kiransu da Khawarijawa, babu wanda ya taba kiransu da Fasikai. Duk da sun yaki Shugaba sun yi masa Tawaye amma su Adilai ne mutanen kirki masu falala.

Kuma hatta Khawarijawa da Aliyu (ra) ya yaka, Sayyidina Aliyu (ra) bai fara yakarsu ya kira su Khawarijawa ba, - duk da ya san sun yi masa Tawaye a matsayinsa na shugaba -, har sai da suka halasta jinanen Musulmai suka kashe Abdullahi bn Khabbab (ra), suka farka cikin matarsa, suka kora dukiyoyin Musulmai.

Da farko sun yi masa Tawaye, amma bai kira su da Khawarijawa da Annabi (saw) ya ba da labarinsu ba har sai da suka halasta jinanen Musulmai gaba daya, suka fita daga cikin al'umma, suka fita daga cikin Musulmai, suka koma wani kauye mai suna Haraura'u, saboda suna ganin ba za su zauna cikin Kafirai ba.

Wadannan fa su ne Khawarijawa!

To yaushe Malaman Sunna suka taba kira ga wannan, da har za a kira su da Khawarijawa Qa'adiyyah, in ban da jahilci ba?!

Wannan ya sa Ibnu Qudama a cikin "Al-Mugniy" ya yi bayanin kasuwan masu Khuruji da tawaye ga Shugaba, ya kasa su kashi Biyar. Na farkonsu Khawarijawa, sai kuma Bugaatu 'Yan tawaye masu Tawili...

Don me ya sa ya banbanta tsakaninsu, inda dukkansu Khawarijawa ne?!

Saboda haka, duk abin da wadannan matasan suke yadawa ba komai ba ne face rudu da jahilci saboda zafin kai da kungiyanci.

Ai yanzu a Nigeria lokaci ya wuce wani ya zo ya jefi wani Malami da Khawarijanci a kasa gane shirmensa, saboda kowa ya ga Khawarijawa a zahiri, wato 'Yan Boko Haram.

Yanzu don Allah wane mai ilimi da adalci ne zai zargi wani daga cikin Malaman Sunna da Khawarijanci a gabanmu, alhali mun ga yadda ake Khawarijanci a wajen 'Yan Boko Haram, wadanda suka halasta jinin kowa in ban da su kadai kawai?!

Abin mamaki, da wannan ne jahilan 'Yan Kungiyar Salafiyyun suke Bidi'antar da Shaikh Ja'afar da Shaikh Albaniy da sauran Malaman Sunna.

Allah ya shiryar da mu gaba daya.

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *