Hali ne na 'Yan Bidi'a ka kirkiri abin da babu shi a cikin Alkur'ani, babu shi cikin Hadisan Annabi (saw) amma kuma ka zo ka kakaba shi wa mutane, wanda ya bi shi ne Ahlus Sunna Salafiy, wanda kuma ya saba ya zama Hizbiy Dan Bidi'a.
Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya ce:
ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺷﻌﺎﺭ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺇﺣﺪﺍﺙ ﻗﻮﻝ ﺃﻭ ﻓﻌﻞ، ﻭﺇﻟﺰﺍﻡ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻪ ﻭﺇﻛﺮﺍﻫﻬﻢ ﻋﻠﻴﻪ ﺃﻭ ﺍﻟﻤﻮﺍﻻﺓ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﻤﻌﺎﺩﺍﺓ ﻋﻠﻰ ﺗﺮﻛﻪ، ﻛﻤﺎ ﺍﺑﺘﺪﻋﺖ ﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺝ ﺭﺃﻳﻬﺎ ﻭﺃﻟﺰﻣﺖ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻪ، ﻭﻭﺍﻟﺖ ﻭﻋﺎﺩﺕ ﻋﻠﻴﻪ ...
ﻭﺍﺑﺘﺪﻋﺖ ﺍﻟﺠﻬﻤﻴﺔ ﺭﺃﻳﻬﺎ ﻭﺃﻟﺰﻣﺖ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻪ ﻭﻭﺍﻟﺖ ﻭﻋﺎﺩﺕ ﻋﻠﻴﻪ، ﻟﻤﺎ ﻛﺎﻧﺖ ﻟﻬﻢ ﻗﻮﺓ ﻓﻲ ﺩﻭﻟﺔ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺜﻼﺛﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﻣﺘﺤﻦ ﻓﻲ ﺯﻣﺎﻧﻬﻢ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﻟﻴﻮﺍﻓﻘﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺭﺃﻱ ﺟﻬﻢ ﺍﻟﺬﻱ ﻣﺒﺪﺅﻩ ﺃﻥ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻣﺨﻠﻮﻕ، ﻭﻋﺎﻗﺒﻮﺍ ﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﻮﺍﻓﻘﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ .
ﺍﻟﺘﺴﻌﻴﻨﻴﺔ ( /1 176 - 177 )
"Ya kasance yana daga cikin tambarin 'Yan Bidi'a akwai kirkiran magana ko aiki da lazimta wa mutane da tilasta musu binsa, da kulla soyayya a kansa, da kulla kiyayya ga wanda ya ki bi, kamar yadda Khawarijawa suka kirkiri ra'ayinsu, kuma suka lazimta shi ga mutane, suka kulla soyayya da kiyayya a kansa. Haka Rafidha...
Haka Jahamiyya ma, suka kirkiri ra'ayinsu, kuma suka lazimta shi ga mutane, suka kulla soyayya da kiyayya a kansa, musamman lokacin da suke da karfi a Daular Khalifofi guda uku, wadanda suka yi Jarabawa (Imihani) wa Manyan Malaman Sunna a zamaninsu, don su bi ra'ayin Jaham, wanda ya kirkira na cewa; Alkur'ani Halittacce ne, suka yi ta yin ukuba ga wanda bai bi su a kan haka ba".
Sabanin halin Malaman Sunna, su ba sa yin Ijtihadi su fitar da abu amma kuma su lazimta shi ga mutane.
Ya ce:
ﻛﺎﻥ ﺃﺋﻤﺔ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻻ ﻳﻠﺰﻣﻮﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻤﺎ ﻳﻘﻮﻟﻮﻧﻪ ﻣﻦ ﻣﻮﺍﺭﺩ ﺍﻻﺟﺘﻬﺎﺩ ﻭﻻ ﻳﻜﺮﻫﻮﻥ ﺃﺣﺪﺍ ﻋﻠﻴﻪ، ﻭﻟﻬﺬﺍ ﻟﻤﺎ ﺍﺳﺘﺸﺎﺭ ﻫﺎﺭﻭﻥ ﺍﻟﺮﺷﻴﺪ ﻣﺎﻟﻚ ﺑﻦ ﺃﻧﺲ ﻓﻲ ﺣﻤﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻋﻠﻰ ﻣﻮﻃﺌﻪ، ﻗﺎﻝ ﻟﻪ : ﻻ ﺗﻔﻌﻞ ﻳﺎ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ...
ﺍﻟﺘﺴﻌﻴﻨﻴﺔ ( /1 177 - 178 )
"Manyan Malaman Sunna da Jama'a sun kasance ba sa lazimta wa mutane ra'ayoyinsu da yake cikin mas'alolin Ijtihadi, ba sa tilasta ma wani bin ra'ayin nasu. Saboda haka ne lokacin da Khalifa Harunar Rasheed ya shawarci Imamu Malik bn Anas a kan dora mutane bisa "Mawadda" sai ya ce masa: Kar ka yi haka ya Amirul Muminina...".
Imamu Malik ya ki yarda a lazimta wa mutane aiki da Littafinsa "Mawadda", ina kuma ga mai da'awar bin Malik, mai neman lazimta wa mutanen Nigeria bin Risala da Mazhabar Malikiyya?!
Saboda haka, babu wanda ya isa ya lazimta wa mutane bin wani abun da babu shi a cikin Alkur'ani ko Hadisi ko Ijma'i. Sawa'un mas'ala ce ta Fiqhu ko wani abu ne na Manhaji, ko da an kira shi ne da sunan Manhajin Salafiyya.
0 Comments