HotBreaking News
Fetching data...

KA JE MAHAIFIYARKA TA YI MAKA ADDU'A

*KA JE MAHAIFIYARKA TA YI MAKA ADDU'A*


Al-Imam Sulaim dan Ayyub Ar-Razi, daya daga cikin manyan malaman Mazhabar Shafi’iyya (Ya rasu a shekara ta 447 BH). Yana cewa:

“Lokacin da nake yaro karami dan shekar goma a garinmu (Ar-Rayy) (Cikin kasar Iran a yanzu), sai wani bakon malami ya ziyarci garin yana koya wa yara karatun Alkur’ani. Sai ya ce min: “Matso kai ma ka karanta”. Sai matsa, na yi ta kokarin in karanta Fatiha amma na kasa, domin harshena ya yi nauyi sosai. Sai ya ce min: “Shin kana da mahaifiya a raye?” Sai na ce masa, e, ina da ita. Sai ya ce: “Ka je wurinta ta yi maka addu’a Allah ya arzutaka da karatun Alkura’ni da na ilimi”. Sai na ce, to. Sai na koma gida na roke ta ta yi mini addu’a, sai ta yi min. 


Sai ga shi na girma har na tafi garin Bagdaza na yi karatun harshen Larbaci da na Fikihu, sannan na dawo garinmu Ar-Rayy. 


Wata rana ina zaune a masallacin Juma’a, muna karanta littafin ‘Muhktasar’ na Muzani, sai ga malamin nan mai koyar da karatun Alkur’ani ya shigo masallacin, ya nufo inda muke ya yi mana sallama, muka amsa masa, amma bai gane ni ko wane ne ba, don ya manta abin da ya faru a can baya da jimawa.  Ya ga muna karatun Mukhtasar na Muzani, shi kuma ga shi ba zai iya karantawa ba, sai ya tambaye ni cewa yaushe ne mutum zai iya koyon irin wannan ilimin? Sai na ji kamar in ce masa idan mahaifiyarsa tana nan raye ya je ta yi masa addu’a, to amma sai na ji kunya na kasa fada masa.” 


Kyakkyawar addu’a ta iyaye tana da albarka matuka.


Wannan mashahurin malami Al-Imam Sulaimu ya fara neman ilimi ne bayan ya  haura shekara arbai’in a duniya. Amma ya zama daya daga cikin hamshakan malamai a zamaninsa.


*Rubutawa*: *Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo kano*


[Dubi, Az-Zahabi, Siyar Al-A’lam, Juzi’i na 3, Shafi na 18-19].

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *