HotBreaking News
Fetching data...

ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI, AMMA INA TSORON CIN HARAM ?

*ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI, AMMA INA TSORON CIN HARAM ?*

*Tambaya:*


Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani ma'aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu'amalarsa za mu ce Alhamdulillah, to shi ne take neman menene halarcin auransa a shari'a? Saboda tana tsoron kar ya rika ciyar da ita da dukiyar haramun.   


*Amsa*


Wa alaikum assalam To dan'uwa Annabi  s.a.w.  yana cewa : "Allah ya la'anci mai cin riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka" Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598. 

Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke mu'amala da riba, saboda ma'aikacin banki zai rubuta ko kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan aike . .

Duba fatawaa Allajanah adda'imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401.


Idan ya zama abin da ma'aikacin banki yake amsa haramun ne, kuma ba shi da wata sana'a sai wannan, akwai hadari a auransa, saboda zai ciyar da matarsa da haramun

 Malamai suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin halal da haram, idan ya maka kyauta za ka iya amsa,  saboda Annabi s.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa, kuma a dukiyarsu akwai halal da haram, amma in ba shi da wata sana'a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin dukiyarsa  ba.  

Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.  


*Allah ne mafi sani.*


*Amsawa*✍🏻


*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

10\4\2015

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *