KADA KAYI SUJADA HAR SAI LIMAN YAYI SUJADA
Manzon Allah ﷺ yayi mana umarni akan koyi da liman akan a dukkan aiyukan sallah,kuma kada ka riga liman yin wani aiki na sallah,ko kuyi tare sai dai kayi bayan liman yayi.
Malamai sun kasan mabiya liman acikin aiyukan Sallah zuwa kaso ukku-
*_1-Akwai Yayayin Liman,wato wanda yake riga liman yin wani aiki na sallah,shi wannan baya da sallah,saboda ya saba umarnin da Manzon Allah ﷺ ya bada ga mai bin liman_*.
*_2-Sa'an liman,shine wanda suke aikata wani aikin sallah tare da liman,kamar sujada da ruku'u,mai wannan hali wani lokacin yana rasa ladar sallah koda sallar tasa bata baciba_*
*_3-Kanan liman,shine wanda yake aikata dukkan wani aikin sallah bayan liman yayi,wannan shine mai cikakken koyi da liman kuma mai bin umarnin Manzon Allah ﷺ,wannan shine mafi samun ladar sallah_*.
_KADA KAYAYI SUJADA DA DUKKAN AIYUKAN SALLAH SAI LIMAN YAYI_
Daga Barra'a bn Azib رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ yana cewa:
"Mun kasance muna yin sallah a bayan Annabi ﷺ idan yace:
[سمع الله لمن حمده]
babu daya daga cikin mu da yake sunkuyar da bayansa har sai Annabi ﷺ ya dora goshin a kasan da sujada".
@رواه البخاري رحمه الله في صحيحه.
Daga Muhaarib Bn disaar yana cewa;naji Abdullahi bn Yazid yana fada akan minbari:Barra'a رضي الله عنه yana cewa:
*_"Lallai su Sahabban Annabi ﷺ sun kasance suna Sallah tare da Annabi ﷺ,idan yayi Ruku'u sai muyi ruku'u,idan ya dago daga ruku'u sai yace_*:
_[سمع الله لمن حمده]_
*Bama gushewa muna tsaye har sai Manzon Allah ﷺ ya dora goshinsa a kasa yayi sujada,sannan muyi sujada a bayansa"*.
@مسلم
A wata riwayar yana cewa:
*"Mun kasance tare da Annabi ﷺ acikin sallah,dayan mu baya motsa bayansa dan tafiya sujada har sai munga Manzon Allah ﷺ ya riga yayi Sujada"*.
A wata riwayar daga Abi Hurairata رضي الله عنه yace:Manzon Allah ﷺ yace:
*(Kada kuyi ruku'u har sai liman yayi ruku'u,kuma kada kuyi sujada har sai yayi sujada....)*.
Allah ne mafi sani
_Allah ka bamu ikon koyi da bin umarnin Manzon Allah ﷺ a dukkan rayuwar mu baki daya_.

0 Comments