MANHAJIN SHAIKH IBNU BAAZ YANA RADDI GA MANHAJIN KUNGIYAR SALAFIYYUN
Manhajin Shaikh Ibnu Baaz na Nasiha da inkarin Munkari ya banbanta da Manhajin Masu Guluwwi a Bidi'antarwa, saboda nasa Manhajin na Shari'a ne, amma nasu kuma kirkirarren Manhaji ne da aka labe a bayan Ilimin "Jarhi da Ta'adili" ana barna da raba kan Ahlus Sunna da zaluntarsu da shi.
Shaikh Ibnu Baaz ya ce:
ﺍﻟﺒﻴﺎﻥ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﺷﺎﺭ ﺇﻟﻴﻪ ﺍﻟﺴﺎﺋﻞ ﺃﺭﺩﻧﺎ ﻓﻴﻪ ﻧﺼﻴﺤﺔ ﺇﺧﻮﺍﻧﻲ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﻭﺍﻟﺪﻋﺎﺓ ﺑﺄﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻧﻘﺪﻫﻢ ﻹﺧﻮﺍﻧﻬﻢ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺼﺪﺭ ﻣﻦ ﻣﻘﺎﻻﺕ ﺃﻭ ﻧﺪﻭﺍﺕ ﺃﻭ ﻣﺤﺎﺿﺮﺍﺕ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻧﻘﺪﺍ ﺑﻨﺎﺀ ﺑﻌﻴﺪﺍ ﻋﻦ ﺍﻟﺘﺠﺮﻳﺢ ﻭﺗﺴﻤﻴﺔ ﺍﻷﺷﺨﺎﺹ؛ ﻷﻥ ﻫﺬﺍ ﻗﺪ ﻳﺴﺒﺐ ﺷﺤﻨﺎﺀ ﻭﻋﺪﺍﻭﺓ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺠﻤﻴﻊ .
ﻭﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻋﺎﺩﺓ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﻃﺮﻳﻘﺘﻪ ﺇﺫﺍ ﺑﻠﻐﻪ ﻋﻦ ﺑﻌﺾ ﺃﺻﺤﺎﺑﻪ ﺷﻲﺀ ﻻ ﻳﻮﺍﻓﻖ ﺍﻟﺸﺮﻉ ﻧﺒﻪ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ ﺑﻘﻮﻟﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : « ﻣﺎ ﺑﺎﻝ ﺃﻗﻮﺍﻡ ﻗﺎﻟﻮﺍ ﻛﺬﺍ ﻭﻛﺬﺍ » ﺛﻢ ﻳﺒﻴﻦ ﺍﻷﻣﺮ ﺍﻟﺸﺮﻋﻲ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﻟﺴﻼﻡ ...
ﻓﻤﻘﺼﻮﺩﻱ ﻫﻮ ﻣﺎ ﻗﺎﻟﻪ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺃﻱ ﺃﻥ ﺍﻟﺘﻨﺒﻴﻪ ﻳﻜﻮﻥ ﺑﻤﺜﻞ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻜﻼﻡ، ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻗﺎﻝ ﻛﺬﺍ، ﻭﺑﻌﺾ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻳﻘﻮﻝ ﻛﺬﺍ، ﻭﺍﻟﻤﺸﺮﻭﻉ ﻛﺬﺍ، ﻭﺍﻟﻮﺍﺟﺐ ﻛﺬﺍ ﻓﻴﻜﻮﻥ ﺍﻻﻧﺘﻔﺎﺩ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺗﺠﺮﻳﺢ ﻷﺣﺪ ﻣﻌﻴﻦ، ﻭﻟﻜﻦ ﻣﻦ ﺑﺎﺏ ﺑﻴﺎﻥ ﺍﻷﻣﺮ ﺍﻟﺸﺮﻋﻲ، ﺣﺘﻰ ﺗﺒﻘﻰ ﺍﻟﻤﻮﺩﺓ ﻭﺍﻟﻤﺤﺒﺔ ﺑﻴﻦ ﺍﻹﺧﻮﺍﻥ ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﺪﻋﺎﺓ ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ....
ﻓﻨﺼﻴﺤﺘﻲ ﻟﻠﺠﻤﻴﻊ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﺍﻟﺘﺨﺎﻃﺐ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺘﻌﻠﻖ ﺑﺎﻟﻨﺼﺤﻴﺔ ﻭﺍﻟﻨﻘﺪ ﻣﻦ ﻃﺮﻳﻖ ﺍﻹﺑﻬﺎﻡ ﻻ ﻣﻦ ﻃﺮﻳﻖ ﺍﻟﺘﻌﻴﻴﻦ ﺇﺫ ﺍﻟﻤﻘﺼﻮﺩ ﺍﻟﺘﻨﺒﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺨﻄﺄ ﻭﺍﻟﻐﻠﻂ ﻭﻣﺎ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻣﻦ ﺑﻴﺎﻥ ﺍﻟﺼﻮﺍﺏ ﻭﺍﻟﺤﻖ ﻣﻦ ﺩﻭﻥ ﺣﺎﺟﺔ ﺇﻟﻰ ﺗﺠﺮﻳﺢ ﻓﻼﻥ ﻭﻓﻼﻥ .
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﺑﺎﺯ ( /7 315 - 316 )
"Bayanin da mai tambaya ya yi ishara gare shi Nasiha muka yi nufi a cikinsa ga 'yan uwana Malamai da Masu da'awa, a kan "naqadinsu" (raddi) ga 'yan uwansu a kan abin da yake kasancewa daga gare su a makaloli da "nadawa" (taron kara wa juna sani) da lakcoci da suke yi, ya kasance raddi ne na neman gyara, wanda ya zama NESA DA JARHI (SUKA) da KAMA SUNAYEN MUTANE, saboda wannan yana jawo gaba da kiyayya a tsakanin duka bangarorin.
Ya kasance daga cikin al'adar Annabi (saw) da tafarkinsa idan labarin wani abu ya same shi daga wani Sahabinsa, abin da ya saba Shari'a to zai fadakar a kan haka ne da fadinsa: "Me ya samu wasu mutane suka ce: kaza da kaza?" Sai ya bayyana yadda abin yake a Shari'a (saw)...
Don haka manufata a bayanin da na yi shi ne abin da Annabi (saw) ya fada. Ma'ana; fadakarwa a kan kurakurai ya kasance da irin wannar magana, a ce: wasu mutane sun ce kaza..., wasu mutane suna cewa; kaza..., amma abin da ya dace da Shari'a shi ne kaza..., abin da yake wajibi shi ne kaza..., sai yin raddin ya kasance ba tare da jarhi (suka) ga wani mutum sananne ba, sai dai a yi raddin a bisa babin bayanin abun a shar'ance, har a samu soyayya a tsakanin 'yan uwa, da malamai da masu da'awa...
Nasihata ga kowa da kowa; magana a kan abin da ya shafi Nasiha da raddi ya kasance ta hanyar saye suna ba ta hanyar kama sunan mutum ba, saboda manufar ita ce fadakarwa a kan kuskure, da abin da ya kamata na bayanin dadai da gaskiya, ba tare da bukatuwa ga sukan wane da wane ba".
Wannan shi ne Manhajin Shaikh Ibnu Baaz, wanda ya dace da Sunnar Manzon Allah (saw), sabanin Manhajin Kungiyar Salafiyyun, Manhajin da suka kirkira da sunan aiki da "Jarhi da Ta'adili", alhali ilimi ne da asali ya takaita ne ga maruwaita Hadisi kawai.

0 Comments