HotBreaking News
Fetching data...

AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA BARRISTER BULAMA BUKARTI YA AIKEWA DA KUNGIYAR IZALA TA JIHAR KANO (3)

AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA BARRISTER BULAMA BUKARTI YA AIKEWA DA KUNGIYAR IZALA TA JIHAR KANO (3)


(Wanda bai karanta rubutu na 1 da na 2 ba, yanada kyau ya koma ya karanta, rashin karantawar zai hana shi ÿancin yance hukunci).


TAMBAYA TA BIYU: Annabi SAW ya kauracewa Nana A'isha a lokacin da ake tuhumarta, to a ina su Mallam suka samo sunnar kusantar Ganduje a lokacin da ake tuhumarsa?


AMSA: Gaskiya ne, Annabi SAW ya kauracewa Ummuna A'isha R.A a lokacin da munafukai suka jefeta da aikata alfasha, amma wannan ba zai zama dalili akan cewa dukkan mai lefi ne shari'ah ta wajabta a kaurace masa ba, na fadi hakan ne saboda dalilai kamar haka:


1. Ita Nana A'isha mata ce ga Annabi SAW, sai ake tuhumarta da aikata alfasha 'Wal Iyazu Billah', to a matsayinsa na mijinta wanda bai san gaibu ba, dole ne zai kaurace mata, saboda kusantarta zai zamanto matsala, koda wata mu'amala ta auratayya ta gudana tsakaninsu, kuma Allah ya kadarci samun wani rabo, to wannan rabon zai zamanto abin yiwa zargi da yar da magana, musamman a wajen munafukai...


2. Abinda zaisa mu fahimci cewa kauracewar da yayi mata yayi ne a matsayinsa na mijinta shine: bai yiwa kowane musulmi umarnin ya kaurace mata ba. Shiyasa a hadisin bamu samu mahaifiyarta da mahaifinta da sauran mutane sun kaurace mata ba.


3. Inda ace kaurace mata hukunci ne gamamme, da mahaifinta, wanda yake shine mutum mafi girma a duniyar musulunci bayan Annabi SAW, da ya kaurace mata, saboda yafi kaunar Annabi SAW fiye da ita.


4. An saukar da hukuncin kauracewa akan sahabbai guda uku da suka ki zuwa yaqi, KA'AB BN MALIK, HILALU BN UMAYYATA da MURARATU BN RABI'E, amma dayake su nasu hukuncin gamamme ne, daga kan Annabi SAW har zuwa kasa, babu wani mahalukin da yake kusantarsu, koda kuwa ta hanyar cinikayya ne. Don har daga karshe ma akayi umarnin matansu su fice sukoma gidajensu. Saboda nasu hukuncin gamamme ne.


5. Ta yadda zamu kara gane cewa ba akan kowanne abu yake zama wajibi a kauracewa mutum ba, ai idan muka tuna, zamu ga cewa an samu wasu cikin wadanda suka rayu da Annabi SAW, wasu sunyi zina, wasu sun sha giya, wasu sunyi sata, da makamantansu, toh Barista ai kaga wannan ba tuhuma bace, tabbas ne ma, amma ba'a yiwa al'umma umarnin su kaurace musu ba.


In short, ba akan kowanne laifi ake kauracewa mutum ba.


A NAN INASO NACE WANI ABU...


A fahimtarmu har yanzu muna a level ne na TUHUMA, koda a yaren su Barista, sai de ace 'ana tuhumar Gwamna...' ita kuma tuhuma a musulunci ma umarni akayi mana da yiwa masu imani kyakkyawan zato akanta, mu guji saurin yarda da ita. Duk wanda ya nazarci ma'anonin ayoyin da suka sauka domin Wanke Nana A'isha, zai fahimci hakan. (a duba farkon Suratun-nur).


Sannan wani abu da ya bani mamaki, Dr. Pakistan acikin jawabinsa yake cewa ai dama an tuhumci Nana Aisha da kuma Annabi Musa, sai Barista yake ganin kamar Dr. Ya kamanta Nana Aisha da Annabi Musa da Ganduje, amma kuma sai ga Barista yana hada alaka ta hanyar basa misali da kauracewar Annabi SAw ga Nana A'isha da kuma rashin kauracewar Izala ga Ganduje. Toh muma muna da tambaya: 


Menene hikimar hada wannan misalin?


Shin Barista yana kamanta Manzon tsira ne da Pakistan?


Zamu cigaba nan ba da dadewa ba insha Allah.


Awaisu Al'arabee Fagge

Chairman, Jibwis

Social Media

Kano State.

28-11-2018

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *