AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA BARRISTER BULAMA BUKARTI YA AIKEWA KUNGIYAR IZALA TA JIHAR KANO (4)
Tanbihi: Ba lallai ka fahimci cikakken sakonmu ba matukar baka karanta rubutu na 1, 2 da 3 ba.
Kafin naje zuwa ga amsa ta gaba, zanso na fadada bayani akan gaba ta kusa da ta karshe acikin rubutun da ya gabata.
A wajenmu, da wajen Barista, har yanzu sunan abinda ake yiwa Ganduje 'TUHUMA', tunda ba'a je karshen bincike ba. Ita kuma tuhuma da ta shafi mai imani, akwai abubuwan da akayi mana umarni dayi a yayinta. Ga su kamar haka:
1. Anyi mana umarnin kai tsaye ma mu karyata duk wata hutuma da aka yiwa masu imani, domin yi musu kyakkyawan zato. Saboda fadin Allah madaukaki:
لَوْلا إِذْ سَمِعْتُمُوهُ ظَنَّ الْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بِأَنفُسِهِمْ خَيْرًا وَقَالُوا هَذَا إِفْكٌ مُّبِينٌ
Ma'ana: Mene yasa lokacin da muminai maza da muminai mata sukaji (tuhumar da ake yiwa daya daga cikinsu) basu yiwa junansu kyakkyawan zato ba? Kamata yayi suce 'tsarki ya tabbata ga Allah, wannan kagaggiyar karya ce mabayyanina'.
2. An umarcemu da kame baki daga yada abinda yake na tuhuma ga masu imani, saboda Fadin Allah madaukaki:
وَلَوْلا إِذْ سَمِعْتُمُوهُ قُلْتُم مَّا يَكُونُ لَنَا أَن نَّتَكَلَّمَ
بِهَذَا سُبْحَانَكَ هَذَا بُهْتَانٌ عَظِيمٌ
Ma'ana: mene yasa lokacin da kukaji tuhumar, ba kuce 'bai kamata muyi magana mu tattauna akan wannan batun ba, tsarki ya tabbata ga Allah, wannan karya ce mai girma.
3. Allah ya umarcemu kada mu kara jifan junanmu da wani abu na tuhuma, a inda yace:
يَعِظُكُمُ اللَّهُ أَن تَعُودُوا لِمِثْلِهِ أَبَدًا إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ
Ma'ana: Allah yana muku wa'azi/gargadi akan kada ku kara komawa zuwa ga jifan juna da abu na tuhuma, IN DAI KU MASU IMANI NE.
In dai sunan abinda ake yiwa gwanma 'tuhuma', toh ga maganar Allah akan tuhumar, ya rage na mutane suyi biyayya ko su saba.
Wani zai iya cewa ai wadannan ayoyin sun sauka ne akan Nana A'isha, saboda haka ba za'a iya kafa hujja dasu a irin wannan mas'alar ba.
Sai muce ko kadan ba haka abin yake ba. Tabbas wadannan ayoyin sun sauka ne akan Nana A'isha, amma kuma zasu cigaba da yin aiki a duk sanda aka samu irin waqi'ar ko makamanciyarta. In kuwa ba haka ba, toh kenan babu wata aya ko daya da zamuyi aiki da ita a yanzu, tunda a asali ba akanmu ayoyin suka sauka ba, ko burbushinmu babu a lokacin.
Na fadi hakan ne bisa dogaro ga wata QA'IDAH USULIYYA da take cewa: العبرة بعموم اللفظ لا بخصوص
السبب
Wato idan nassi yazo, me akace a nassin ake dubawa, ba asalin abinda ya faru nassin ya sauka ba
TAMBAYA TA UKU: Mallam yace "Ganduje ya hada kan malamai masu banbancin ra'ayi da fahimta, ta hanyar hadasu a wajen aiki daya, a saka dan izala shugaba, mataimaki dan darika..." toh dama rikicin malamai ba akan tauhudi da aqida bane? Dama akan rashin basu mukamai ne?
AMSA: ya salam! Ko kadan bah aka abin yake ba, kuma shi kanshi Barista yasan ba hakan bane, amma ga amsar tambayar ka kamar haka:
1. Da farko dai hadin kai tsakanin mabanbanta akidu don zaman lafiya ba bakon abu bane a duniyar musulunci , kuma babban abin koyi akan haka shine shugaban mu Annabi MUHAMMAD (SAW), kamar yadda takardar yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin musulmai da yahudawa da aka rubuta ta kunsa, kuma manzo saw ya amince da ita.
2. Kungiyar izala karkashin jagorancin Dr. PAKISTAN itace ta fara mika hannu ga jagororin tijjaniyya da na qadiriyya da nufin rage zafin gaba da qiyayya tsakanin mabiya, ba tare da kowa ya bar aqidar saba, saboda koyi da abinda manzon Allah ya yi a madinah, kuma ba shakkah wannan ya bada gagarumar gudunmawa wajan raguwar fitintinu tsakanin kungiya da mabiya wadancan dariku, alhamdulillahi.
3. Idan muka dubi wadannan bayanai da suka gabata, zamu yarda cewa duk wani yunkuri na karfafa zaman lafiya da dakile fitintinu ya cancanci a goya masa baya, a yabawa maiyi kuma ayi masa fatan alkhairi, wannan shine abinda kungiya ta yiwa gwamna Ganduje, saboda kowa yana bada gudunmawar sane da irin damar da yake da ita, don haka yayi amfani da kasancewarsa gwamna ya jawo wadannan malaman ya hada su guri guda don cimma wanacan buri.
Dan haka maganar cewa dama rashin nadasu mukamai ne yake jawo taqaddama a baya, inaga kodai rashin sanin abinda manzon Allah yayi a Madina, ko kuma rufe ido daga abinda malam Pakistan yai ta faman yi tun lokacin da gwamna bai zama gwamna ba, in kuwa ba haka ba, wanne mukami malam Pakistan yake nema a wancan lokacin kuma a wajan wa?
Dole ne dukkanmu mu fahimci cewa yin nesa da juna yana daga abinda yake kara iza wutar fitina tsakanin al’umma. Amma matsowa kusa yakan bayar da gudunmawa wajen kulla alaka, zumunci, jin kunyar juna, da kuma tattaunawa cikin laluma ta hanyar ilimi da hujjoji. Kenan zama ko aiki waje daya yana bada gudunmawa wajen hadin kai.
Ina fata barista da duk wanda ke bukatar fahimtar wannan ma'salar ya fahimta.
Allah yasa mu dace.
Zamu karasa tambayoyin nan ba da jimawa ba insha Allah.
Awaisu Al'arabee Fagge
Chairman Jibwis
Social Media
Kano State.
29-11-2018
0 Comments