HotBreaking News
Fetching data...

TA YAYA ZAN IYA GANE MUKTARIN SALLAH DA LALURINTA?

*_TA YAYA ZAN IYA GANE MUKTARIN SALLAH DA LALURINTA?_*

*Tambaya*

Assalamcualaika mal da Allah amin bayanin yadda ake gàne yanayin muhktari da lalurin sallan Asuba da maghrib

*Amsa:*

Wa'alaikum assalam, Muktari da laluri, lokuta ne da Allah ya rataya hukunce-hukuncen sallah akan şu, a na gane muktarin sallar asuba idan alfijir na biyu ya keto, ana gane lalurin sallar asuba idan gari ya yi fayau, an gane muktarin sallar azahar idan rana ta karkata daga tsakiyar sama, ana gane lalurin sallar azahar idan inuwar mutum ta yi daidai da tsawonsa, ana gane lokacin la'asar zababbe ya shiga idan inuwar mutum ta yi daidai da tsawonsa, ana gane lalurinta ya shiga idan inuwar mutum ta ninka tsawonsa, ana gane muktarin sallar magriba, idan rana ta fadi, Muktarin sallar Isha yana shiga idan ragowar Jan rana ya buya (shafaki) Bayan dare ya raba lokaci ne na lalurin magriba da Isha.

Allah ne mafi Sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *