HotBreaking News
Fetching data...

YADDA ZAKA GANE BOKA

GA YADDA BOKA KE TAMBAYARSA WAJEN SANIN CUTA:-

       1- Zai tambayi ka/ki sunan ki/ka da na mahaifiya(basa tambayar sunan mahaifi domin sihiri da sunan mahaifiya akeyinsa)


      2-Neman wani bangare na jikin mutum: kamar Gashin kai,Farce, Da sauransu


      3)- Neman wani Abu wanda ya taba jikin matumin da za ayi wa sihirin(Wato dole ne sai kayan da Gumi ko zufa(sweat) na mutumin ya taba kafin a wanke saboda haka yana da kyau mu lura da kayan da muke zubarwa ko kuma wasu suce mu basu kaya,) ,ko daukar sawun kafa na mutum wato kasar mutum ya taka ba takalmi,


     4-Nema akai masa wani bayyanannan abu kamar Farin goro,Jan zakara ko kaza,bakar akuya ko dan taure,ko kuma bangare na jikin wasu halittu,


    5-Sukan Nemi Da mutum yayi wani aiki wanda Allah Ya haramta (domin nemo fushin Allah) kamar sallah ba alwala, zina da wadanda aka haramtawa mutum kamar akanwa ko mahaifiya ko Yayar mutum ko kuma Yar'sa,


  6)- Rubutawa mutum Wani Hatimi ko bashi wasu tarin layu yasa a jikinsa da yi masa sharadin cewar "MATUQAR YA RABU DA ITA TO BAZAI SAMU KARIYA BA KO KUMA WANI ABU ZAI SAMESA"


  7- Wani lokaci zaka ji yana karatu maras ma'ana,ko kuma ya kawo kalamai marasa ma'ana a tsakiyar karatun Al-qur'ani kamar..."JIB YADAKA YANUS,JIB YA SAQARADDIN," Wato yana kiran sunayen wasu aljanu.


  8- Sukan Bayr da umarni ga mutum,ko kuma maras lapiyan da yaje gurinsu domin neman lapiya akan ya lazimci fadin wasu kalamai ko kuma ya yawaita  zuwa suna Sanennan guri yaana yin wani aiki da zasu Gindaya masa.


 

Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *