BABU ABIN DA YAKE KAWO SABANI NA RABUWAR KAI KAMAR JAHILCI DA ZALUNCI DA MUMMUNAN NUFI
Lallai sabuba da dalilai da suke kaiwa ga mummunan sabani wanda Allah da Manzonsa (saw) suka yi zargi a kansa, kuma Allah ya tanadi azaba a kansa, wanda yake raba kan al'umma suna da yawa, amma mafi girmansu shi ne JAHILCI da BACIN NIYYA DA MUNGUN NUFI, wanda ya kunshi kulla zalunci da hasada a cikin zuciya da son neman daukaka a bayan kasa. Wannan shi ne sababin da ya sa Yahudawa suka yi sabani da rarrabuwa a tsakaninsu, kuma Allah ya zargesu a dalilin haka.
Allah ya ce:
ﻭﻟﻘﺪ ﺁﺗﻴﻨﺎ ﺑﻨﻲ ﺇﺳﺮﺍﺋﻴﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺤﻜﻢ ﻭﺍﻟﻨﺒﻮﺓ ﻭﺭﺯﻗﻨﺎﻫﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻄﻴﺒﺎﺕ ﻭﻓﻀﻠﻨﺎﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ( 16 ) ﻭﺁﺗﻴﻨﺎﻫﻢ ﺑﻴﻨﺎﺕ ﻣﻦ ﺍﻷﻣﺮ ﻓﻤﺎ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﺇﻻ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﺟﺎﺀﻫﻢ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺑﻐﻴﺎ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﺇﻥ ﺭﺑﻚ ﻳﻘﻀﻲ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻓﻴﻤﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻓﻴﻪ ﻳﺨﺘﻠﻔﻮﻥ ( 17 )
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah (r) ya ce:
ﺍﻻﺧﺘﻼﻑ ﺍﻟﻤﺬﻣﻮﻡ ﻣﻦ ﺍﻟﻄﺮﻓﻴﻦ ﻳﻜﻮﻥ ﺳﺒﺒﻪ ﺗﺎﺭﺓ : ﻓﺴﺎﺩ ﺍﻟﻨﻴﺔ؛ ﻟﻤﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﻔﻮﺱ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﻐﻲ ﻭﺍﻟﺤﺴﺪ ﻭﺇﺭﺍﺩﺓ ﺍﻟﻌﻠﻮ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ، ﻓﻴﺤﺐ ﻟﺬﻟﻚ ﺫﻡ ﻗﻮﻝ ﻏﻴﺮﻫﺎ، ﺃﻭ ﻓﻌﻠﻪ، ﺃﻭ ﻏﻠﺒﺘﻪ ﻟﻴﺘﻤﻴﺰ ﻋﻠﻴﻪ، ﺃﻭ ﻳﺤﺐ ﻗﻮﻝ ﻣﻦ ﻳﻮﺍﻓﻘﻪ ﻓﻲ ﻧﺴﺐ ﺃﻭ ﻣﺬﻫﺐ ﺃﻭ ﺑﻠﺪ ﺃﻭ ﺻﺪﺍﻗﺔ، ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ، ﻟﻤﺎ ﻓﻲ ﻗﻴﺎﻡ ﻗﻮﻟﻪ ﻣﻦ ﺣﺼﻮﻝ ﺍﻟﺸﺮﻑ ﻭﺍﻟﺮﺋﺎﺳﺔ ﻭﻣﺎ ﺃﻛﺜﺮ ﻫﺬﺍ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﺁﺩﻡ، ﻭﻫﺬﺍ ﻇﻠﻢ .
ﻭﻳﻜﻮﻥ ﺳﺒﺒﻪ - ﺗﺎﺭﺓ - ﺟﻬﻞ ﺍﻟﻤﺨﺘﻠﻔﻴﻦ ﺑﺤﻘﻴﻘﺔ ﺍﻷﻣﺮ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺘﻨﺎﺯﻋﺎﻥ ﻓﻴﻪ، ﺃﻭ ﺍﻟﺠﻬﻞ ﺑﺎﻟﺪﻟﻴﻞ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺮﺷﺪ ﺑﻪ ﺃﺣﺪﻫﻤﺎ ﺍﻵﺧﺮ، ﺃﻭ ﺟﻬﻞ ﺃﺣﺪﻫﻤﺎ ﺑﻤﺎ ﻣﻊ ﺍﻵﺧﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻖ : ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻜﻢ، ﺃﻭ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻟﻴﻞ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻋﺎﻟﻤﺎ ﺑﻤﺎ ﻣﻊ ﻧﻔﺴﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻖ ﺣﻜﻤﺎ ﻭﺩﻟﻴﻼ .
ﻭﺍﻟﺠﻬﻞ ﻭﺍﻟﻈﻠﻢ : ﻫﻤﺎ ﺃﺻﻞ ﻛﻞ ﺷﺮ، ﻛﻤﺎ ﻗﺎﻝ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ : } ﻭﺣﻤﻠﻬﺎ ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻇﻠﻮﻣﺎ ﺟﻬﻮﻻ }.
Ya ce:
"Mummunan sabani (na rabuwar kai) wanda yake abin zargi a tsakanin dukkan bangarorin guda 2, a wani lokacin sababinsa yana kasancewa ne a dalilin bacin niyya (mummunan nufi), saboda abin da ke cikin zukata na zalunci (wuce iyaka da ketare haddin Shari'a ta hanyar kin aikata wani abin da aka wajabta a lokacin sabanin ko aikata wani abin da aka haramta in sabanin ya auku), da hasada da son samun daukaka a bayan kasa da makamancin haka. Saboda wannan sai bangare ya so ya zargi ra'ayin daya bangaren, ko aikinsa, ya ki yarda da shi, ko neman ya yi galba a kansa don ya nuna ya fi shi, ko ya so ra'ayin wanda ya dace da shi a dangantaka ko mazhaba ko gari ko abokantaka da makamancin haka, saboda in ra'ayinsa ya tabbata ya tsayu to zai samu matsayi da shugabanci. Abin mamaki, akwai irin wannan kuwa masu yawa a cikin 'yan adam. Wannan kuwa zalunci ne (wuce iyakan Allah).
A wani lokacin kuwa sababin sabanin bangarorin yana kasancewa ne a dalilin jahilcin masu sabanin ne a kan hakikanin lamarin da suke sabani a kansa, ko jahilci game da dalilin da daya bangaren yake kafa hujja da shi ma daya bangaren, ko jahilcin daya bangaren da dalilin da yake tare da daya bangaren na gaskiya, a hukuncin ko a dalilin (imma yana da gaskiya a hukunci, amma ba shi da gaskiya a dalili, ko kuma yana da gaskiya a dalili amma kuma ba shi da gaskiya a hukunci), ko da kuwa shi yana da ilmi game da abin da ya rike nasa na gaskiya a hukuncin da dalilin.
JAHILCI DA ZALUNCI SU NE ASALIN KOWANE SHARRI, kamar yadda Allah ya ce:
{ ﻭﺣﻤﻠﻬﺎ ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻇﻠﻮﻣﺎ ﺟﻬﻮﻻ }
"... Mutum ya kasance mai matukar zalunci da jahilci".
Duba Iqtidha'us Siradil Mustaqeem 1/ 131 - 132.
Abin lura:
1. Babban abin da yake haifar da rabuwar kai a cikin al'umma shi ne ZALUNCI DA JAHILCI.
2. Zalunci shi ne ketare iyakan Allah da dokokin Shari'arsa, ta hanyar kin aikata abin da ya wajaba a lokacin da sabani ya faru, ko aikata abin da ya haramta. Kamar kin yarda da SULHU, ko kin yarda da ZAMA TARE DON A TATTAUNA MAS'ALOLIN DA AKA YI SABANI A KANSU, ko KAURACE MA JUNA, ko KIN YIN SALLAMA DA YANKE ALAKA A TSAKANI, ko KIN KARBAN GASKIYA BAYAN TA BAYYANA da makamancin irin abubuwan da suke wajibi ne a aikatasu a lokacin da sabani ya auku a tsakanin bangarori guda biyu na Ahlus Sunna ko suka haramta a aikatasu.
3. Jahilci imma ya zama ta bangaren malamai, ko ta bangaren mabiya.
(a) Ta bangaren malamai shi ne wanda yake kasancewa a sakamakon gazawa wajen bincike a kan mas'alolin da aka yi sabani a kansu, ta yadda zai jahilci hakikanin mas'alolin a dalili ko a hukunci, ko ya jahilci na abokin sabanin nasa.
(b) Ta bangaren mabiya kuwa, a mafi yawan hali za ka samu mabiyan su mukallidai ne, ba su da ta cewa a mas'alolin ilmi, amma kuma su ne a kan gaba wajen zalunci da rura wutar fitina da haddasa gaba da kiyayya a tsakani, har su taimaka wa malamin nasu ko jagoran nasu wajen kin yarda da gaskiya bayan ta bayyana masa. Irin wadannan mabiya sun zama shedanu, masu haddasa fitina da raba kan al'umma, masu toshe hanyar Allah.
4. Mummunan nufi shi yake haifar da ta'assubanci (bin ra'ayi don biyan bukata ta kashin kai ko son zuciya) da kin karban gaskiya da aiki da ita.
5. Duka wadannan ababen tambaya ne a ranar kiyama, Allah ya yi gargadi a kan sabani na rabuwar kai da sabubansu, kuma ya tanadi azaba mai girma a kansu.
Ya Allah ka yi mana afuwa ka kubutar da mu.
0 Comments