HotBreaking News
Fetching data...

SHIN ABIN DA MUKE GANI DAGA 'YAN KUNGIYAR SALAFIYYUN HASADA DA ZALUNCI NE KENAN?

SHIN ABIN DA MUKE GANI DAGA 'YAN KUNGIYAR SALAFIYYUN HASADA DA ZALUNCI NE KENAN?
Sau da yawa masu bin Manhajin Guluwwi a bidi'antarwa sukan gafala, sai ka samu ba su sanin abin da suke fada. Sai mutum ya zo yana jifan Malamai da kalmomi da sunaye amma bai san cewa; bidi'antar da su yake yi ba, ko ma kafirtawa.
Misali sau da yawa za ka ji suna jifan Malaman da suke bidi'antarwa suna jarraha su da sunan "Shaidanu cikin Mutane" ( ﺷﻴﺎﻃﻴﻦ ﺍﻹﻧﺲ ) alhali suna ne na kafirai da munafukai makiya Annabi (saw).
Haka kuma suna jifan Malamai Ahlus Sunna da sunan "Ikhwaniy", "Qutbiy", "Sururiy", "Hizbiy" (Dan Kungiya), da irin wadannan sunaye, alhali ma'anarsu a wajen Malamansu shi ne Dan Bidi'a. Suna jifan mutane da su, a lokaci guda kuma suna raya cewa; su ba sa Bidi'antar da Malaman da suke jifa da wadannan sunaye. Wannan tufka da warwara ne!
Haka kuma sun siffanta da hasada da zalunci, suna hasada ga Malaman da suka sa a gaba ba tare da hakki ba, alhali malamai ne da suka sadaukar da rayuwarsu ga amfanar da al'umma a Addininsu, su kuma sun zo suna cin dunduniyarsu saboda tsananin hasada da zalunci. A kan irin haka Shaikh Ibnu Uthaimeen (r) ya ce:
ﺍﻵﻥ ﺗﺠﺪ ﺑﻌﺾ ﺍﻹﺧﻮﺍﻥ - ﻣﻊ ﺍﻷﺳﻒ - ﻳﺮﺩ ﻋﻠﻰ ﺇﺧﻮﺍﻧﻪ ﺃﻛﺜﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺮﺩ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻠﺤﺪﻳﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮﻫﻢ ﺻﺮﻳﺢ، ﻳﻌﺎﺩﻳﻬﻢ ﺃﻛﺜﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﻌﺎﺩﻱ ﻫﺆﻻﺀ ﻭﻳﺸﻬﺮ ﺑﻬﻢ ﻓﻲ ﻛﻼﻡ ﻻ ﺃﺻﻞ ﻟﻪ، ﻭﻻ ﺣﻘﻴﻘﺔ ﻟﻪ، ﻟﻜﻦ ﺣﺴﺪ ﻭﺑﻐﻲ، ﻭﻻﺷﻚ ﺃﻥ ﺍﻟﺤﺴﺪ ﻣﻦ ﺃﺧﻼﻕ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﺃﺧﺒﺚ ﻋﺒﺎﺩ ﺍﻟﻠﻪ . ﺛﻢ ﺇﻥ ﺍﻟﺤﺴﺪ ﻻ ﻳﺴﺘﻔﻴﺪ ﻣﻨﻪ ﺍﻟﺤﺎﺳﺪ ﺇﻃﻼﻗﺎ، ﺑﻞ ﻻ ﻳﺰﻳﺪﻩ ﺇﻻ ﻏﻤﺎ ﻭﺣﺴﺮﺓ
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﻭﺭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﻌﺜﻴﻤﻴﻦ ‏( /26 262 - 263 )
"Yanzu za ka samu wani daga cikin 'Yan uwa - abin takaici - yana raddi ga 'yan uwansa fiye da yadda yake raddi a kan Mulhidai, wadanda kafircinsu yake a fili, yana gaba da su fiye da yadda yake gaba da wadannan, yana yi musu batanci a bainar jama'a da maganar da ba ta da asali ba ta da hakika, kawai saboda hasada da zalunci. Babu shakka hasada tana cikin halayen Yahudawa mafi munin bayin Allah. Sa'annan kuma mai hasada ba zai amfana da komai a hasadar tasa ba, kai, sai dai bakin ciki da tsananin bacin rai".
Su Malaman da suke yi musu irin wannar hasada, kowa ya ga kokarinsu, na karantar da al'umma Addini da Sunna da raddi ga Bidi'o'i, sabanin masu wannan Manhaji, ba a sansu da wani abin kirki a wadannan fagage ba.
To wai shi wannan Manhaji na Guluwwi a Bidi'antarwa da sunan Manhajin Salafiyya, wanda ake ta kururuwa a kansa, don me ya sa ba za a nuna mana shi cikin Nassin Alkur'ani ko Sunna ko Ijma'i ba ne?!
Hasali ma Manhaji ne da yake kirkirarre na raba kan Ahlus Sunna, mun tabbatar da haka a lokuta daban - daban.
Load disqus comments

0 Comments

 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *