HotBreaking News
Fetching data...

SANIN GASKIYAR MUTUM SAI ALLAH

*SANIN GASKIYAR MUTUM SAI ALLAH*

A wata Makaranta ne aka sace Alkalamin wata

daliba. Sai ta kai kara a wurin Malaminsu.

Malam ya hana kowa fita daga cikin aji har sai

an caje jakar kowa an gano wadda ta dauki

wannan Alkalami.

Da aka zo kan wata yarinya sai ta ki bari a buda

Jakarta. Aka yi juyin duniya ta ce ita ba za ta

bari a yi cajin Jakarta ba. Da aka matsa mata sai

kawai ta fara kuka. ‘Yan ajin duka sun dauka ita

ta yi satar nan. Saboda haka aka ce aje ofishin

shugaban Makaranta.

Da suka zo Hedimasta ya tambaye ta, me ya sa

kika yi sata? Sai ta ce, idan kowa ya fita zan

gaya maka. Hedimasta ya yi umurni kowa ya

fita aka bar su su biyu a cikin ofis. Ko da suka

fita sai ta bude ma sa Jakarta. Babu abin da ke

ciki sai gutsattsarin biredi da guntayen biskit da

‘yan Makaranta suka ci suka zubar. Hedimasta

ya ce, me nake gani a nan? Ta ce, wallahi

wannan abin da nake tsinta kenan a kullum

idan na je gida mu ci ni da mahaifiyata da

kannena. Domin Mahaifinmu ya rasu ba mu da

kowa sai Allah! Shi ne na ji kunyar a buda

wannan jakar a cikin aji abokaina su yi mani

dariya.

*Darasi:* Ba kowa ne yake iya bayyana

uzurinsa ba. Ka kyautata ma mutane zato.

Sanin gaskiyar mutum sai Allah.

Rubutawa:

*Dr. Mansur Ibrahim Sokoto*

Continue reading...

MANYA-MANYAN ALAMOMIN BAKIN ALJANI GA MACE

MANYA-MANYAN ALAMOMIN BAKIN ALJANI GA MACE.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


 Kamar yadda duk wani mai karanta littattafan addini da littafin Allah Alqur'ani, yasan fadin Allah subhanahu wata'ala akan cewar Akwai Aljanu a duniya, kuma suna gudana a jikin Dan Adam kamar yadda jini yake gudana a jikin mutum.

  Allah madaukakin sarki acikin suratul Baqara yana cewa, "LIYUFARRIQUUNA BIHI BAINAL MAR'I WA ZAUJIY" ليفرقون به بين المرع وزوجه. Wato (sai sun Raba tsakanin mace da mijinta). Ko sai sun raba tsakanin saurayi da budurwar da zai Aura, Burinsu hana aure ko raba aure ta hanyoyi da dama :::---

👉 Kamar daukewa mace Ni'ima lokacin saduwa. 

  Da wannan ne zaisa miji yaji matarsa ta fita a ransa, abu kadan sai a Rabu. Anan ne kuma Burin wannan aljanin ya cika kenan.

👉 Rashin jin Dadin Jima'i.

  Anan ita kanta matar idan mijinta ya sadu da ita, babu abinda zataji sai dai zafi a gabanta, sabida haka anan ne fa wani Lokacin da zarar taga mijinta yana Neman kusantarta zataji hankalinta gaba daya ya tashi, zataji bata da wata nutsuwa, bazaiji Dadi ko Nishadi awajen saduwa da ita ba. Wanda Wannan ma hanya ce da wadannan shaidanu sukebi wajen kashe aure, musamman ma idan sukaga mijin mai tsananin sha'awa ne. 

👉 Rashin haihuwa.

 Anan ma wannan bakaken Aljanun suna bada Matsala, musamman ma ga mace idan ta sami ciki sai sun zubar da wannan cikin, zata zama ba ita ba haihuwa har abada, har sai ta rabi da wannan mugun aljani da yake tare da ita. Sai kuma Su sanyawa mijin tsananin son haihuwa. Dan Su bakantawa ma'aurata,  har azo ana yiwa juna gorin haihuwa. Amma basu gano menene matsalar ba. 

👉 Sanya damuwa da bacin rai ga mace

   haka kawai mace zataji ranta yana baci, wani Lokacin ma sai tayi kuka kawai zataji saukin wannan damuwar. 

  Sau da yawa kuma suna sanya wanan damuwar ne idan suka fahimci mai gida ya kusan zuwa ko kuma lokacin mu'amala irin ta aure. Ko mace ta tsani mijin ba tare da yayi Mata komi ba. 

👉 kwaranyar jini daga farjin mace. 

  Musamman ma lokacin da mai gida yake matukar son zuwa wajen iyalinsa, sannan Wannan jinin ba wai lokacin hailar mace bane, haka kawai Dan ya hana mu'amala ta aure tsakanin mace da mijinta. 

👉 Rashin son maganar aure, wata matar kwata-kwata bata son ayi maganar aure a gabanta, Alhalin tana son tayi auren, ko kuma duk wanda zaizo wajenta wanda ba aure zaiyi ba shine nata, shi kadai take so, idaance ba aurwnta zaiyi ba, sai ayi fada da ita akansa, amma duk wanda yazo da maganar aure bazata kulashi ba, bazata soshi ba. A haka sai kaga anayiwa kawayenta aure ita tana nan a kasa ba aure, ko kuma ma kaga mace mai hankali, mai kyau amma ba wanda yake zuwa wajen ta, Sabida basa son tayi aure. 

👉 yawan faduwar gaba da mummunan mafarki a gidan miji ko kuma a gidan iyaye, wani Lokacin kuma sai mace taji ana taba jikinta ko taji ana tafiya a bayanta, harma tana Jin karar tafiyar, amma bazataga kowa ba. A haka suke cire mata son zaman gidan miji. 

👉 yawan saka mummunan abu, kamar kana saka cewar kawai ka aikata wani Sabo, ko ki Aikata wani sabo, wani lokacin ma sabon da zai iya fidda ki daga musulunci, ko idan kana tafiya a mota kakeji cewar wannan motar yanzu zata wuntsula ko zata fadi ko bazaka sauka lafiya ba, harma wannan zaisa wani ya dena bulaguro kwata-kwata, da dai sauransu.

👉 mummunan mafarkin shanu ko Namun daji ko ruwa ko ana bin mutum da gudu ya kasa gudu ko kana tashi sama ko kin haihu ko kina shayarwa da dai sauransu. 


 Akwai matsaloli na daban wanda bamu kawo bayaninsu anan ba. 


Wannan cibiya ta ZAUREN SUNNAH ISLAMIC MEDICINE CENTER ta tanadar da magunguna a iya bincikenta wanda suke babbake irin wadannan  migayen aljanu ya Kone Su gabaki daya. 

     mai bukatar magani zai iya Tintibarmu ta wannan number 08108605876 

Continue reading...

ADDU'AR FITA DAGA MASALLACI - HISNUL MUSLIM

Addu'ar Fita Daga Masallaci.


بِسمِ الله وَالصّلاةُ وَالسّلامُ عَلى رَسولِ الله، اللّهُـمَّ إِنّـي أَسْأَلُكَ مِـنْ فَضْـلِك، اللّهُـمَّ اعصِمْنـي مِنَ الشَّيْـطانِ الرَّجـيم.


Bismil-lah wassalatu wassalamu ala rasoolil-lah, allahumma innee as-aluka min fadlik, allahumma iAAsimnee minash-shayta

nir-rajeem.


Da sunan Allah tsira da Aminci su tabbata ga Manzon Allah. Ya Allah! Ina rokonka daga falalarka. Ya Allah! Ka kare ni daga shaidan tsinanne.


Continue reading...

ADDU'AR SHIGA MASALLACI - HISNUL MUSLIM

Addu'ar Shiga Masallaci


أَعوذُ باللهِ العَظيـم وَبِوَجْهِـهِ الكَرِيـم وَسُلْطـانِه القَديـم مِنَ الشّيْـطانِ الرَّجـيم،[ بِسْـمِ الله، وَالصَّلاةُ] [وَالسَّلامُ عَلى رَسولِ الله]، اللّهُـمَّ افْتَـحْ لي أَبْوابَ رَحْمَتـِك . 

A'uzu billahil-azeem wabiwajhihil-kareem wasultanihil-kadeem minash-shaytanir-rajeem, 

[bismil-lah, wassalatu] [wassalamu AAala rasoolil-lah] , allahumma iftah lee abwaba rahmatik.


Ina neman tsarin Allah mai girma, da na fuskarsa mai alfarma, da na mulkinsa dadadde, daga shaidan tsinanne. Da sunan Allah, tisara da Aminci su tabbata ga Manzon Allah. Ya Allah! Ka bude mini kofofin rahamarKa.


Continue reading...

ADDU'AR TAFIYA MASALLACI - HISNUL MUSLIM

Addu'ar tafiya Zuwa Masallaci


اللّهُـمَّ اجْعَـلْ فِي قَلْبِـي نُورًا، وَفِي لِسَـانِي نُورًا، فِي سَمْعِي نُورًا، فِي بَصَرِي نُورًا، مِنْ خَلْفِي نُورًا،  وَمِنْ أَمَامِـي نُورًا، وَ مِنْ خَلْفِي نُوراً، فِي نَفْسِي نُوراً، وَأَعْظِمْ لِي نُوراً، وَعَظِّمْ نُوراً، وَاجْعَلْ لِي نُوراً ، وَاجْعَلْنِي نُوراً، اَللُّهُمَّ أَعْطِنِي نُوراً، وَاجْعَلْ فِي عَصَبِي نُوراً، وَفِي لَحْمِي نُوراً، وَفِي دَمِي نُوراً ، وَفِي شَعْرِي نُوراً، وَفِي بَشَرِي نُوراً ". "اَللَّهُمَّ اجْعَلْ لِي نُوراً فِي قَبْرِي .. وَنُوراً فِي عِظَامِي، وَزِدْنِي نُوراً، وَزِدْنِي نُوراً، وَزِدْنِي نُوراً، وَهَبْ لِي نُوراً عَلَى نُوراً.

Allahumma j'al fi kalbi nuran, wa fi lisani nuran, wa fi sam'i nuran, wa fi basari nuran, wa min fawki nuran, wa min tahti nuran, wa 'an yamini nuran, wa 'an shimali nuran, wa min amami nuran, wa min khalfi nuran waj'al fi nafsi nuran, wa a'zim li nuran, wa 'azzim li nuran. Wa j'al li nuran, wa j'alni nuran. Allahumma a'tini nuran, wa j'al fi 'asabi nuran, wa fi lahmi nuran, wa fi dami nuran, wa fi sha'ri nuran, wa fi bashari nuran. (Allahumma j'al lin nuran fi kabri, wa nuran fi izami)

(wa zidni nuran, wa zidni nuran, wa zidni nuran) (wa hab li nuran 'ala nur).


Ya Allah ka sanya haske a cikin zuciyata, da haske a kan harshena, da haske a gabana, da haske a damana, da haske a haguna, da haske a gabana, da haske a bayana; Ka sanya haske a cikin raina, Ka girmama haske gare ni, ka girmama min haske, ka sanya haske gare ni, Ka sanya ni (na zama) haske, Ka sanya haske a cikin jijiyoyina, da haske a cikin namana, da haske a cikin gashina, da haske a cikin fatata, Ya Allah Ka sanya mini haske a cikin kabarina, da haske a cikin kasusuwana, ka kara mini haske, Ka kara mini haske, Ka kara mini haske, Ka ba ni haske a kan haske.


Continue reading...

ZIKIRI YAYIN SHIGA GIDA - HISNUL MUSLIM

Zikiri Yayin Shiga Gida.


بِسْـمِ اللهِ وَلَجْنَـا، وَبِسْـمِ اللهِ خَـرَجْنَـا، وَعَلَـى رَبِّنَـا تَوَكَّلْـنَا .

Bismil-lahi walajna, wabismil-lahi kharajna, wa'ala rabbina tawakkalna.


Da sunan Allah muka shiga, kuma da sunansa muka fita kuma ga Allah kadai, Ubangijinmu, muka dogara.


Continue reading...

ZIKIRI YAYIN FITA DAGA GIDA - HISNUL MUSLIM

Zikiri Yayin Fita Daga Gida


بِسْمِ اللهِ ، تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللهِ وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللهِ.

Bismil-lah, tawakkaltu alal-lah, wala hawla wala kuwwata illa billah.

Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu karfi sai da Allah.


اللّهُـمَّ إِنِّـي أَعـوذُ بِكَ أَنْ أَضِـلَّ أَوْ أُضَـلَّ ، أَوْ أَزِلَّ أَوْ أُزَلَّ ،  أَوْ أَظْلِـمَ أَوْ أَُظْلَـمَ ، أَوْ أَجْهَلَ أَوْ يُـجْهَلَ عَلَـيّ .

Allahumma innee a'uzu bika an adilla aw udalla, aw azilla aw ozall, aw azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya.


Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na bata ko a batar da ni, ko na zame ko a zamar dani, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta.


Continue reading...

ZIKIRI BAYAN GAMA ALWALA - HISNUL MUSLIM

Zikiri Bayan Gama Alwala



أَشْهَدُ أَنْ لاَ إِلَـهَ إِلاّ اللهُ وَحْدَهُ لا شَريـكَ لَـهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمّـداً عَبْـدُهُ وَرَسـولُـهُ.

 Ashhadu an la ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, wa-ashhadu anna Muhammadan abduhu warasooluh.


Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai, babu abokin tarayya a tare da shi; kuma ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne.

 kuma 



 اَللَّهُـمَّ اجْعَلْنِـي مِنَ التَّـوّابِينَ وَاجْعَـلْنِي مِنَ الْمُتَطَهِّـرِينَ.

Allahummaj-alnee minat-tawwabeena waj'alnee minal-mutatahhireen.


Ya Allah! Ka sanya ni a cikin masu yawan tuba, kuma ka sanya ni a cikin masu tsarkaka.


15.

سُبْحَـانَكَ اللّهُـمَّ وَبِحَمْدِكَ أَشْهَـدُ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَـيْكَ . 

Subhanakal-lahumma wabihamdika ashhadu an la ilaha illa anta astaghfiruka wa-atoobu ilayka.


Tsarki ya tabbata gare Ka ya Allah tare da yabo gare Ka. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, ina neman gafarka kuma ina tuba gareKa.


Continue reading...

ADDU'AR DA AKE WA WANDA YA SANYA SABUWAR TUFA -HISNUL MUSLIM

Addu'ar da ake Wa wanda ya sanya sabuwar tufa

"تُبْلِي وَيُخْلِفُ اللهُ تَعَالَى"

Tublee wayukhliful-lahu ta'ala


Allah ya sa ka mayar da ita tsumma, kuma Allah madaukaki ya mayar maka da wata (tufar).



"إِلْبِسْ جَدِيداً وَعِشْ حَمِيداً ومُتْ شَهِيداً"

Ilbas jadeedan waAAish hameedan wamut shaheedan.


(Allah ya sa) ka sanya sabo, kuma ka rayu kana abin yabo, kuma ka mutu kana shahidi (wanda aka kashe a tafarkin Allah).


Continue reading...

ADDU'AR SANYA SABABBIN TUFAFI - HISNUL MUSLIM

Addu'ar Sanya Sababbin Tufafi.

"اَللَّهُمَّ لَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ كَسَوتَنِيهِ، أَسْأَلُكَ مِنْ 

خَيْرِهِ وَخَيْرَ ماَ صُنِعَ لَهُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهِ وَشَرَّ مَا صُنِعَ لَهُ.

Allahumma lakal-hamdu anta kasawtaneeh, as-aluka min khayrihi wakhayri ma suni'a lah, wa-a'u'zu bika min sharrihi washarri ma suni'a lahu.


Ya Allah! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, Kai ne Ka tufatar da ni shi (wannan tufar). Ina rokonKa alherinsa da alherin abin da aka yi shi dominsa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrinsa da sharrin abin da aka yi shi dominsa.


Continue reading...

ADDU'AR SANYA TUFAFI - HISNUL MUSLIM

Addu'ar Sanya Tufafi:

الحَمْدُ ِللهِ الَّذِي كَسَانِي هَذَا الثَّوْب ورَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلاَ قُوَّةٍ"

Alhamdu lillahil-lazee kasanee hatha aththawb warazakaneehi min ghayri hawlin minnee wala kuwwah.


Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya tufatar da ni wannan (tufa), kuma ya azurta ni da ita, ba tare da wata dabara daga gare ni ba ko wani karfi.


Continue reading...

ADDU'O'IN TASHI DAGA BARCI - HISNUL MUSLIM

Addu'o'in Tashi daga Barci.

"الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور"

Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba'ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.


Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya dauki rayukanmu, kuma zuwa gare shi tashi yake.


(2)Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya farka da daddare ya ce;

لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللّهُ وَحْـدَهُ لاَ شَـرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْـكُ وَلَهُ الْحَمْـدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، سُـبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْـدُ ِللهِ ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَاللهُ أكْبَرْ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوّّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ الْعَلِيِّ الْعَظِيمِ. رَبِّ اغْفِرْ لِي. 

La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah, lahul-mulku walahul-hamd, wahuwa ala kulli shay-in kadeer, subhanal-lah, walhamdu lillah, wala  ilaha illal-lah wallahu akbar, wala hawla wala kuwwata illa billahil-aliyyil azeem. Rabbi ghfir li.


"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai, babu abokin tarayya a gare shi; mulki da yabo nasa ne, kuma Shi Mai iko ne bisa komai. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah shi ne mafi girma, kuma babu dabara babu karfi sai da Allah, madaukaki mai girma, Ya Ubangijina! Ka gafarta mini".

Wanda ya fadi wannan za a gafarta masa, idan kuma ya yi addu'a za a amsa, idan kuma ya tashi ya yi alwala, ya yi sallah za a karbi sallarsa.


"الحَمْدُ لله الذِي عَافَانِي في جَسَدِي ورَدَّ عَلَيَّ رُوحِي، وأَذِنَ لي بِذِكْرهِ"

Alhamdu lillahil-lathee AAafanee fee jasadee waradda AAalayya roohee wa-athina lee bithikrih.


Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya bani lafiya a jikina, kuma ya ya dawo mini da raina, kuma ya bani izinin ambatonsa.



إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَاخْتِلاَفِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ لآيَاتٍ لِّأُوْلِي الألْبَابِ *الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللّهَ قِيَاماً وَقُعُوداً وَعَلَىَ جُنُوبِهِمْ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ رَبَّنَا مَا خَلَقْتَ هَذا بَاطِلاً سُبْحَانَكَ فَقِنَا عَذَابَ النَّارِ*رَبَّنَا إِنَّكَ مَن تُدْخِلِ النَّارَ فَقَدْ أَخْزَيْتَهُ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ *رَّبَّنَا إِنَّنَا سَمِعْنَا مُنَادِياً يُنَادِي لِلإِيمَانِ أَنْ آمِنُواْ بِرَبِّكُمْ فَآمَنَّا رَبَّنَا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرْ عَنَّا سَيِّئَاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ الأبْرَارِ * رَبَّنَا وَآتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَى رُسُلِكَ وَلاَ تُخْزِنَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِنَّكَ لاَ تُخْلِفُ الْمِيعَادَ *فَاسْتَجَابَ لَهُمْ رَبُّهُمْ أَنِّي لاَ أُضِيعُ عَمَلَ عَامِلٍ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَى بَعْضُكُم مِّن بَعْضٍ فَالَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخْرِجُواْ مِن دِيَارِهِمْ وَأُوذُواْ فِي سَبِيلِي وَقَاتَلُواْ وَقُتِلُواْ لأُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلأُدْخِلَنَّهُمْ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ ثَوَاباً مِّن عِندِ اللّهِ وَاللّهُ عِندَهُ حُسْنُ الثَّوَابِ *لاَ يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ الَّذِينَ كَفَرُواْ فِي الْبِلاَدِ *مَتَاعٌ قَلِيلٌ ثُمَّ مَأْوَاهُمْ جَهَنَّمُ وَبِئْسَ الْمِهَادُ *لَكِنِ الَّذِينَ اتَّقَوْاْ رَبَّهُمْ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا نُزُلاً مِّنْ عِندِ اللّهِ وَمَا عِندَ اللّهِ خَيْرٌ لِّلأَبْرَارِ * وَإِنَّ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ لَمَن يُؤْمِنُ بِاللّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْهِمْ خَاشِعِينَ لِلّهِ لاَ يَشْتَرُونَ بِآيَاتِ اللّهِ ثَمَناً قَلِيلاً أُوْلَـئِكَ لَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ إِنَّ اللّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ *يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اصْبِرُواْ وَصَابِرُواْ وَرَابِطُواْ وَاتَّقُواْ اللّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ 


Inna fi khalki s-samawati wa-l-ardi wa khtilafi l-layli wa n-nahari la-ayatin lu-uli-l-albab, al-ladhina yadhkuruna l-laha kuyaman wa ku'udan wa ala junubihim, wa yata fakkaruna fi khalki s-samawati wa-l-ardi, rabbana! Ma khalakta hadha batilan subhanaka fa-kina adhaba n-nar.

Rabbana! Innaka man tudkhili n-nara fa-kad akhzaytahu wa ma li-zalimina min ansar, Rabbana! Innana sami'na munadiyan yunadi li-l-imani an aminu bi-rabbikum fa-amanna. Rabbana! Fa-ghfir lana dhunubana wa kaffir 'anna sayyi'atina wa tawaffana ma-'a-l-labrar. Rabbana! Wa a'tina ma a'dtana 'ala rusulika wa la tukhzina yawma-l-kiyamati, innaka la tukhlifu-l-mi'ad.

Fa-stajaba lahum rabbuhum anni la udi'u amala amilin minkum m-min dhakarin aw untha, ba'dukum min ba'din, fa-l-ladhina hajaru wa ukhriju min diyarihim wa udhu fi sabili wa katalu wa kutilu, la-ukaffiranna 'anhum sayyi'atihim wa la-udkhilannahum jannatin tajri min tahtiha-l-anharu, thawaban min 'indi l-lahi, wa l-lahu 'indahu husunu-ththawab.

La yaghurrannaka takallubu l-ladhina kafaru fi-l-bilad, mata'un kalilun, thumma ma'wahum jahannamu wa bi'sa-l-mihad.

Ladini l-ladhina t-takaw rabbahum lahum jannatun tajri min tahtiha-l-anharu khalidina fiha, nzulan m-min 'indi l-lahi wa ma inda l-lahi khayrun li-l-abrar.

Wa inna min ahli-l-kitabi la-man yu'minu bi-l-lahi wa ma unzila ilaykum wa ma unzila ilayhim, khash'ina li-l-lahi, la yashtaruna bi-ayati l-lahi thamanan kalilan. Uwla'ika lahum ajruhum 'inda rabbihim, inna l-laha sari'u-l-hisab.

Ya ayyuha l-lahdhina amanu-sbiru wa sabiru wa rabitu wa t-taku l-laha la'allakum tuflihun. [Suratu Ali'imran 190-200)


Hakika a cikin halittar sammai da kassai, da sabawar dare da rana, lallai akwai ayoyi ga ma'abota hankula. (Su ne) wadanda suke ambatyon Allah a tsaye da kuma zaune da kuma kishingide, suke kuma tunani a kan halittar sammai da kassai (suna cewa): "Ya Ubangijinmu! Ba ka halicci wannan abu a banza ba. tsarki ya tabbata gareKa, Ka kiyashe mu azabar wuta. Ya Ubangijinmu! Hakika Kai, duk wanda Ka shigar das hi wuta, babu shakka Ka kunyata shi. Azzalumai kuwa ba su da wasu   mataimaka. Ya Ubangiji! Hakika mu, mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani, cewa: "Ku yi imani da Ubangijinku". Sai muka yi imani. To, ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, Ka kuma kankare mana miyagun aiyukanmu, Ka kuma karbi rayukanmu tare da mutane na gari. Ya Ubangijinmu! Ka bam u abin da Ka yi mana alkawari da shi a kan harshen Manzanninka, kada kuma ka kunyata mu ranar alkiyama hakika Kai ba Ka saba alkawari". Sai Ubangijinsu ya amsa musu (cewa): "Hakika Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinku, namiji ko mace; sashinku daga sashi yake. To, wadanda suka yi hijira, aka kuma fitar da su daga gidajensu, aka cuce su saboda Ni, suka kuma yi yaki, kuma aka kasha su, lallai zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar da su aljannatai wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu; (wannan) sakamako ne daga Allah. Allah kuwa a wurinsa kyakkyawan sakamako yake. Kada kai-komon wadanda suka kafirta a cikin garuruwa ta rude ka. Jin dadi ne dan kankani; sannan sakamakonsu wutar Jahannama ce, tir da wannan makwanta. Amma wadanda suka ji tsoron Ubangijinsu, suna da aljannatai wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu, masu dawwama a cikinsu; wannan liyafa ce daga wajen Allah; abin da kuwa ya zo daga wajen Allah shi ya fi ga managarta. Kuma hakika akwai daga ma'abota littafi wanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ku, da abin da aka saukar zuwa gare su, suna masu kankan da kai ga Allah ba sa musanya ayoyin Allah da dan tamani kankani. Wadancan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu. Hakika Allah mai hanzarta hisabi ne. yak u wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri, kuma ku rinjayi kafirai a cikin hakuri, kuma ku yi zaman dako, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta". [Ali-Imran, 190 zuwa karshen surar].


Continue reading...

FALALAR ZIKIRI - HISNUL MUSLIM

FALALAR ZIKI

 Allah Madaukakin Sarki ya ce:

فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُواْ لِي وَلاَ تَكْفُرُونِ 

Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni.

Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152].


يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْراً كَثِيراً

Ya'ayyuhallazina Amanuzkurullaha Zikran Kathiran.


Ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". (Ahzab aya ta 41).

وَالذَّاكِرِينَ اللَّهَ كَثِيراً وَالذَّاكِرَاتِ أَعَدَّ اللَّهُ لَهُم مَّغْفِرَةً وَأَجْراً عَظِيماً

Wazzakirinallaha Kathiyran Wazzakirati A'addanlahu Lahum magfiratan Wa'ajran Aziyman.

Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma". [Ahzab, aya ta 35]

وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعاً وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالآصَالِ وَلاَ تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ

Wazkurrabbaka Fiy Nafsika Tadarru'an Wakhiyfatan waduwanaljahri Minal kawli Bil'guduwi Wal'asali Walatakun Minalgafiliyna.

Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kankan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (saka-tsaki) tsakanin asirtawa, da bayyanawa, da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu". [A'araf, aya ta 205].

Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne". (Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208). Muslim ya rawaito shi da lafazin; 'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayye ne da matacce". (1/539).)

Kuma ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Madaukaki". (Tirmizi (5/459), da Ibn Majah (2/1245). Duba Sahih Ibn Majah (2/316). Da Sahihul Tirmizi (3/139).)

Kuma ya ce: "Allah madaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawana da ni, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni a cikin ransa zan ambace shi a cikin raina, idan ya ambace ni a cikin jama'a zan ambace shi a cikin jama'ar da ta fi su alheri, in ya kusance ni taki daya zan kuance shi tsawon gaba guda, in ya zo min ya na tafiya zan zo masa ina gaggawa".( Bukhari (8/171), da Muslim (4/2061). Lafazin ruwayar na Bukharine.)

Daga Abdullahi Ibn Busr, Allah ya yarda da shi, ya ce; Ya Ma'aikin Allah! Shari'o'in Musulunci sun yi yawa a gare ni, saboda haka ka nuna wani abu da zan yi riko da shi. Ya ce: "Ku harshenka ya gushe face yana danye daga ambaton Allah". (Tirmizi (5/458). Da Ibn Majah (2/1246). Duba Sahihul Tirmizi (/139), da Sahih Ibn Majah (2/317).)

Kuma mai tsira da amincin Allah yace; "Wanda ya karanta harafi daya daga littafin Allah yana da (ladan) kyakkyawan aiki daya saboda shi, kuma dukkan kyakkyawan aiki daya yana da (ladan) misalinsa goma. Ba ina cew Alif Lam Mim harafi ba ne. A'a, Alif harafi ne, Lam harafi ne, Mim harafi ne".( Tirmizi (5/175) Duba Sahihul Tirmizi (3/9), da Sahihul Jami'us Sgir (5/340).)

Kuma daga Ukbata ibn Amir, Allah ya yarda da shi, ya ce; "Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gareshi, ya fito alhali muna cikin rumfa, sai yace; "Wane ne daga cikinku zai so ya fi kullum da safe zuwa koramar Budhan ko Akik, ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna, ba tare da yin wani laifi ba ko yanke zumunta?" Muka ce: muna son haka. Ya ce; "Dayanku ya je masallaci ya nemi sani, ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin littafin Allah Mabuwayi Mai Daukaka, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku, ayoyi hudu sun fi masa taguwa hudu, da kwantankwacin adadinsu na rakuma". (Muslim (1/553))

Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; "Wanda ya zauna a wani waje bai ambaci Allah a wajen ba, wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah. Wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajen ba, shi ma zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah. (Abu Dawud (4/264), da waninsa. Duba Sahihul Jami (5/342).)

Kuma Mai tsira da amincin Allah ya ce: "Babu wasu mutanen da suka zauna a wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba, kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya, in Allah ya so ya yi musu azaba, in ya so ya gafarta musu".( Tirmizi, duba Sahihul Tirmizi (3/140).)

Kuma Mai tsira da amincin Allah yace; "Babu wasu mutane da zu su tashi daga wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan mushen jaki ne, kuma zai zamanto musu abin da-na- sani".( Abu Dawud (4/264). Da Ahmad (2/389). Duba Sahihul Jami' (5/176).)


Continue reading...

TAMBAYA DA AMSA

*Assalamu Alaikum*

.

.

*Tambaya 

=

Mutunne yayi zina da wata sabida anhanasu aure sai wani da akema lakabi da malam wai saiyace ma yaron da yayi zina sai yayi kwana 40 yana sallah ba akarba hakane? Hkuncinsa yayi

=

=

Amsa

=

_Toh wannan hukuncin nasa beyiba domin kuwa hadisin da ya dogara dashi na karyane, dan haka wannan maganar batada wani inganci ko yanzu ya tuba Allah yana iya yefe masa sannan kuma lefin zinarshi daban matsayin sallarshi kuma daban, amma duk mutuminda ba kafiri ba kuma ba gidan boka yajeba to babu dalilinda zesa ace sallolinshi na kwanaki basuyiba****_

=

=

Allah Yasa mudace.

=

=

Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar

http://m.facebook.com/ibnhujjahislamic

ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka wa atubu ilaikai

Continue reading...

KADDARA TA RIGA FATA 003 Dr. Mansur Ibrahim Sokoto (Hafizahullah)

*KADDARA TA RIGA FATA 003*

 iii. IDAN AJALI YA YI KIRA..
Kafin Usamatu ya bar birnin Madina sai da ya zo
ya yi bankwana da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama. Gurin Usamatu ne ya ga ya ji wasu
kalmomi daga wurin Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama tun da yake ga halin da ake
ciki.
Amma ina! a wannan lokaci ciwo ya sake zagayo
shi har ma ba zai iya furta kalma guda daya ba
da bakinsa. Don haka sai Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya rinka motsa yatsansa yana
nuna wa Usamatu cewa, yana yi masa addu’a da
zuci.
Daga karshe dai sai aka ji Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama yana fadin “Na za6i
abokin sama.. Na za6i abokin sama.. Na za6i
aljanna…” Sannan rayuwarsa mai tsarki ta fita.
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un.
Kafin wannan, Abubakar ya samu kwanaki da
dama bai ziyarci iyalinsa11 ba wadda ta ke a
Sunhu wani kauye mai nisan mil daya daga
Madina a dalilin kulawarsa da Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma tsayar da
sha’anin ba da Sallah da aka dora masa.
Amma ganin sauki ya samu sai ya tafi can domin
ya ziyarci matarsa.
Isowarsa ke da wuya sai ya tarar duk wuri ya
rude, mutane suna ta kuka.
Umar kam har ya zare takobinsa yana barazanar
sare kan duk wanda ya kuskura ya ce Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya mutu.
Abinka da sadauki sai Abubakar duk ya fita
batunsu, ya shiga dakin ‘yarsa A’ishah wurin da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake
kwance, ya kware mayafi daga fuskarsa, ya
hakikance lallai Manzon Allah kam ya gama da
duniya. Nan take sai ya sunkuya ya sumbace shi,
ya ce, “na fanshe ka da uwata da ubana ya
Manzon Allah! Kai tsarkakakke ne a raye ko
bayan cikawa”.
Fitowarsa ke da wuya sai Abubakar ya hau
mimbari, daman dai Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya nada shi liman, kuma aikinsa bai
kare ba sai in Musulmi sun za6i wani sun ce shi
ya saurara.
Abin da ko Musulmi a wannan lokaci ba za su
ta6a yi ba ke nan.
*Abin Lura*
* Gaba za mu ga yadda Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya rinka yin ishara game da Abubakar,
har ma sai ya yi kamar ya fito fili sai ya fasa.
* Sunanta Habibatu Diyar Kharijah. Ita ce
amaryarsa da ya bari da cikin Ummu Kulsum.
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
*Rubutawa:*
*_Dr. Mansur Ibrahim Sokoto_

Continue reading...

KADDARA TA RIGA FATA 002 DR. MANSUR IBRAHIM SOKOTO

*KADDARA TA RIGA FATA 002*

 ii. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya
Samu Sauki.
Ana haka ne sai kwatsam Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallama ya samu sauki har ya umurci iyalinsa
su kai masa ruwa ya yi wanka. Samun wannan
kuzari da Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yi sai ya fita Masallaci har ma ya
samu sukunin yin huduba wadda a cikinta ya yi
addu’a ga wadanda su kayi shahada a yakin
Uhudu, ya tsawaita addu’a gare su.
Sannan ya ce ma mutane,“ku sani Allah ya bai
wa wani bawansa za6i a tsakanin rayuwar duniya
da koma ma Allah, amma wannan bawan ya zabi
abin da ke wurin Allah”. Mafi yawan Sahabbai ba
su gane in da maganar ta nufa ba sai da suka ga
Abubakar yana kuka, yana cewa, a’a Manzon
Allah! Mun fanshe ka da iyayenmu da
ubanninmu!!
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi
umurni a cikin hudubarsa da a tabbatar da ganin
rundunar da ya tura don ta yaki Rumawa a
karkashin jagorancin Usamatu Dan Zaidu ta tafi.
Ya bayyana ma jama’a cewa, ya ji maganganun
da ake yi game da kuruciyar Usamatu. Ya ce, to,
ai babansa ma haka ku ka ce masa.
Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
ya yi ma Muhajirai wasicci akan Ansaru, ya ce,
“Ya ku Muhajirai ku sani Ansaru su ne mafakar
Musulunci. Don haka ku kyautata ma wanda ya
kyautata a cikinsu, wanda ya munana a cikinsu
kuwa ku yafe masa”. Kamar dai yana nuni ga
cewa, Muhajirai za su rike al’amarin mulki a
bayansa, to kar su watsar da ‘yan uwansu, masu
masaukinsu, mutanen Madina.
Bayan haka sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya fadi falalar Abubakar yana cewa,
“Ku sani ba ni da wani aboki kamar Abubakar,
kuma ba wanda Allah ya amfane ni da dukiyarsa
kamar Abubakar. Kuma da ya halalta in riki wani
badadayi a cikin mutane da shi zan za6a. To,
amma bai halalta ba domin Allah ya riga ya rike
ni badadayinsa kamar yadda ya riki Ibrahimu. Don
haka dai shi abokina ne a imani har Allah ya
hada mu da shi a aljanna”.
Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama
ya ba da umurnin a rufe duk kofofin da mutane
suka bude wa kansu na zuwa Masallaci, ya ce,
amma a bar ta Abubakar.
*Abin Lura*
* Baban Usamatu, Zaidu Dan Harithah yana cikin
jagorori uku wadanda suka yi shahada a yaqin
Mu’utah.
* Watakila wannan shi ne nuni na karshe da
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ma
sahabbai game da jagorancin da yake son a
damka ma Abubakar na wannan al’umma, amma
ba ya son ya tilasta, ya fi son al’umma ta za6a
da kanta don ya zamo abin koyi har abada. A
nan
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_
*Rubutawa:*
*_Dr. Mansur Ibrahim Sokoto_*

Continue reading...

KADDARA TA RIGA FATA 001 Dr. Mansur Ibrahim Sokoto

KADDARA

 TA RIGA FATA 001

 _Shimfida_
i. Farkon Jinyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Bayan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kammala aikin hajjinsa da ya yi a shekara ta Goma bayan hijira wanda a cikinsa ya ce ma Musulmi “Ku yi koyi da aikin hajjina domin ban sani ba watakila ba zan sake haduwa da ku bayan wannan shekarar ba” sai masu zurfin ilmi daga cikin Sahabbai suka fara ji a jikinsu cewa fa lokacin ciratar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga wannan duniyar ya kusanto.
Ga shi kuma ana cikin aikin hajjin sai ayar Alqur’ani ta sauka tana ba da labarin cewa, addini kam ya cika, kuma duk wata ni’imar da Madaukakin Sarki yake son yi wa bayinsa ta fuskar dora su a kan shiriya to an kammala ta. Sai suka fahimci cewa, aikin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo yi na isar da manzanci ya kare kenan, don haka ajalinsa ya kusa.
Komawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Madina ke da wuya kuwa sai ya kwanta
ciyon ajali wanda ya dauke shi tsawon watanni uku, amma dai bai tsananta ba sai a cikin watan Rabi’ul Awwal, wata na uku ke nan bayan aikin hajji.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gamu da zafin ciwo fiye da yadda za a kamanta don ko har sai da aka tambaye shi ya ce, mu Annabawa muna da lada biyu ne, don haka a ciwo ma Allah cikin adalcinsa yake ribinya mana nauyinsa.
Mai jinyarsa Uwar Muminai A’ishah ta ba da labarin yadda jikinsa ya gashe, har a kan dauko ruwa mai sanyi a ajiye a gabansa yana sanya hannunsa a ciki don ya dan ji sanyi, amma kuma nan take sai ruwan ya sauya yanayi saboda zafin masassara daga hannayensa masu tsarki.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rinka fadin cewa, tabbas mutuwa kina da zafi. Ya Allah ka taimake ni a kan zafin mutuwa!
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya suma a cikin wannan lokaci har sau uku, a ko wanne ya kan tambaya idan ya farka, “Shin ko mutane sun yi Sallah?” akan ce masa, suna nan dai suna jiranka ya Manzon Allah! Sannan ya yi wanka da nufin ya fita zuwa Masallaci. Sai bayan da haka ta faru har sau uku ne, ya hakikance gajiyawarsa a kan fitowa, sannan ya yi umurni a gaya ma Abubakar ya ba mutane Sallah.
_Madogara_
* Duba Sahihul Bukhari a littafin yaqe – yaqe, Babin Mutuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
_Mu hadu a rubutu na gaba…………_

Continue reading...

MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BINTA AZUMI !

MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI !

 Tambaya :
Aslm mlm dan Allah ina da tambaya : tun kafin a kama azumi uwata ba ta da lafiya har akayi sallah, rana ta 16 ga watan karamar sallah Allah yayi mata rasuwa, shin za mu ranka mata azumi ko ba sai mun ranka ba ? Allah ya saka da hairi.
Amsa :
To malam mutukar rashin lafiyar ta zarce mata, har zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba sakaci ta yi ba, saboda fadin Allah madaukaki : “Kuma duk wanda yake mara lafiya ko matafiyi to sai ya rama a kwanaki na daban” Bakara aya ta : 185, wato bayan Ramadahana, idan mara lafiya ya samu sauki, ko matafiyi ya dawo , Ka ga wanda bai samu sauki ba har ya mutu, zai zama bai kai lokacin da zai rama ba, don haka sai ya saraya akan shi . .
Amma idan ta samu damar ramawa, ta yi sakaci ba ta rama ba har ta mutu, to sai makusancinta ya rama mata, saboda fadin Annabi s.a.w. : “Duk wanda ya mutu akwai azumi akansa, to sai makusancinsa ya rama masa” . kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1851. Duba Fataawa nuru aladdarb lamba ta : 247.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.

Continue reading...

BABANA YA RASU ANA BINSA AZUMI, SABODA RASHIN LAFILA

*_BABANA YA RASU ANA BINSA AZUMI, SABODA RASHIN LAFIYA:_*

 *Tambaya:*
Dr. Allah ya yiwa mahaifina rasuwa be samu yin azimin watan Ramadan ba sakamakon rashin lpy da yake fama da ita awannan lokacin.
Tambaya ta anan shi ne za'a ciyar ne ko za'a rama masa aximin ko kuma babu komai akansa duba da ayoyin da sukayi bayani akan hakan Allah ta'ala ya karawa mln lpy yasa agama lpy da kyakkywan karshe?
*Amsa:*
Wa'alaikum assalam, in har rashin lafiyar ya zarce masa tün daga watan ramadanan har ya mutu, to ba za'a rama masa ba, saboda Allah ba ya dorawa rai abin da ba ta iya ba, amma idan ya samu saukin da zai iya ramawa, amma ya yi sakaci bai rama ba, wani daga cikin makusantansa zai rama maşa kamar yadda malamai suka fahimci haka a hadisin da Bukhari da Müslim suka rawaito, wanda Annabi S.A.W yake cewa: "Duk wanda ya mutu ana binsa azumi,to waliyinsa zai biya maşa"
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

ZAN IYA ZUBAR DA CIKIN DA NA TABBATAR SIKILA NE

*ZAN IYA ZUBAR DA CIKIN DA NA TABBATAR SIKILA NE ?*



*_Tambaya_*


Assalamu Alaikum. mallam ni AS ce, mijinama ma desame genotype muke da shi, yarana biyu babban AA karamar AS, duk sanda na sami chiki muna zuwa a duba mana genotype din babyn dake chikin, likitochi suka tabbatar da SS ne sai musa a chire, amma bai kaiwa 4months muke chirewa, mallam meye hukunchin yin hakan ?



*Amsa*


Wa alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu,

To 'yar'uwa Malamai sun yi ijma'i akan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.


Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai watanni hudu, wasu sun haramta, wasu kuma sun halatta wasu sun karhanta


Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin Scler ba dole ya zama lalura ba, tun da ana iya haihuwarsa ya rayu, ya bautawa Allah ya amfani al'uma, don haka barin cikin shi ne ya fi, saidai idan kuka zubar kafin ya cika wata hudu saboda matsalar da kuke tunanin yaron zai iya fuskanta a rayuwarsa, ba za'a ce kun yi laifi ba, tun da bai zama mutum ba, kuma ba za'a tashe shi ranar alkiyama ba.      

Don neman karin bayani duba Ahkamu al-janin fil-fiqhil islamy na Umar Ganam


 Allah ne mafi sani.

                                                 

*Dr. Jamilu Zarewa*

Continue reading...

TAMBAYA DA AMSA

TAMBAYA

=========

👇

Salama alaikumu 


mal abokina sunce in tambayi ka ka basu amsa 1 a cikin azumi na Ramadan ɗin nan da ya wuce yayi wasa da gaban sa da safe sau 2 har maniyyi ya fito masa amma ya kame baice komai ba, har saida aka sha ruwa. yanzu kuma yayi nadamar hakan ya zai yi idan yayi niyar ramuwar su 




Diriba ne shi yana ɗaukar mutane zuwa wani gari ya kai su, kasuwa ko kuma garuruwan su da aka haifi su = wata rana ya tsanci kansa a halin babu. a cikin wan nan tafitafiyin da suke. daga cikin fasinjan da ya ɗauka a kan hanya sai suka buƙace su huta suka sauqo daga muta suka zauna = sai wani ya zuɓda kuɗin sa a cikin su . Shi kuma diriban yaga kuɗin ya ɗauka ya ɓuye kuma yaji mai kuɗin yana cigiya yanzu shima yayi nadamar hakan kuma abun ya faru ne a Nigeria yanzu kuma muna tare da shi a nan ƙasar Saudia yanzu yana so ya sauqi wan nan haƙƙin ya zai yi.




AMSA

======

👇

1. Abinda yake kansa anan shine, Zaiyi Ramuwar wannan Azumin guda daya, sannan yaci gaba da istigfari, domin Manzon Allah saw yace koda yayi Azumin shekara bazai biya masa wannan gibin Azumin da ya karya ba, tinda ba ta hanyar saduwa bane.

 Idan Allah ya gadama ya yafe masa, idan kuma ya gadama ya kama shi da lefin abinda ya aikata, domin akwai malaman da suke ganin ma ba wani Azumi da zakayi, suna ganin Wanda kaffara take kansa shine, wanda ya sadu da matarsa Da rana kuma da gangan Alhali yana Azumi. Domin shine aka sami Nassi sarihi daga Manzon Allah saw. 

 Wanda yake son Karin bayani ya duba littafin صحيه فقه السنة، zai sami karin bayani.

  

2. Yana faruwa Wani lokacin mutum ya aikata wani Abunda zaizo daga baya idan imani ya dawo masa yayi Nadama,  domin Barawo bashi da imani inji manzon Allah saw. Manzon Allah saw yace لايسرق السارف حين يسرق وهو مئمن، Wato Barawo bazaiyi sata ba A lokacin da yayi sata Alhalin yana da Imani, domin sai an cire masa rigar Imani zai aikata wannan Aika-Aikar. Idan Allah ya taimakeshi daga baya a dawmasa da rigar imaninsa, idan kuma ba haka ba, to a haka Zai mutu a matsayin maras imani.

   A yanzu Abinda yake kansa, dole ne kamar yadda imamunnawawiy yace, Zaiyi ردالمظالم، wato zai maida Zalinci ga wanda ya zalunta. 

  Zai maida wannan hakkin ne ga mai shi ta fuskar da ta dace.

  Ko dai ya nemi mai hakki ya maida masa hakkinsa (Zallar kudinsa), ko kuma yayi masa sadaka da Adadin kudin da ya dauka, Da niyyar Allah ya maidawa mai hakki hakkinsa. Nan gaba kuma kar ya sake.


Allah Shine Masani 


Continue reading...

GWARZON NAMIJI 1&2

GWARZON NAMIJI….1&2

Da sunan Allah me rahma me jinkai tsira da aminci su kara tabbata ga manzon tsira manzon rahma (SAW) ina farin cikin gabatarda wannan littafin tareda fatan zai amfanar da al’umma allah yasa albarka acikinsa


Akowanne zamani Allah yana kawo jarumai gwaraza wadanda suke sadaukar da farin cikinsu domin farin cikin iyalansu, daga cikinsu ne ake samun gwarzon namiji wanda duk yanda al'umma takai ga lalacewa tofa wadannan basa kasa a guiwa wajen nuna kyakyawar mu'amala ga iyalansu,


Akwai abu uku da gwarzon namiji yakeda wanda shine ma babba makasudin da yasa kowacce mace ke fatan samunsa, haka zalika sune abu mafi girma da mace keso wajen namiji,


1 KAUNA --gwarzon namiji shine kadai ke nunawa mace kauna bawai soyayya ba don akwai gagarumin banbanci tsakanin kauna da soyayya,

Misali wanda yake kaunar ka shine kadai zai zauna dakai a kowanne yanayi kake, shine wanda kana shiga wata matsala yana kara kaunarka, kauna itace me saka tausayi wanda duk wani yanayi da mutum ya shiga me kaunar sa bazai taba juya masa baya ba, haka zalika shine zaiso 'yan uwar matarsa yaso 'ya'yanta.


2 BIYAN BUKATUN MACE --wajen biyan bukatun iyalinsa kuwa baya bada uziri yakanyi duk yanda zaiyi don farin cikin iyalinsa, shine wanda baya dogaro da dukiyar matarsa, domin namiji baya zama gwarzo matukar matarsa tana daukar nauyin kanta kona yaransu komai kankanta.



3 ME GAMSARDA MACE-- gamsar da mace lokacin saduwa yana karawa namiji kwarjini awajen mace akasin haka kuma yana kawo raini wanda wannan ba dabi'ar gwarzon namiji bane domin shi ya kanyi kokarin magance duk wata matsala da zata hanashi gamsar da iyalansa, matsalar daga wurinsa ne ko daga wajen matarsa.

 

Nasara ko faduwa bata samun namiji saida sahalewar mace, mace itace alkiblar namiji komai jarumtar sa itace rauninsa, kuma domin samun daraja a wajenta dole sai namiji ya zama gwarzo wanda yake rikeda akalar zuciyarsa bawai wanda zuciyarsa ke rike akalar saba.


 

Wannan shine gwarzon wanda akidarsa itace shimfida rayuwar farin ciki da abokiyar rayuwarsa wato matarsa, Jarumin yasha alwashin cimma burinsa ta hanyar yiwa rayuwarsa tsari me kyau

Har saida takai kafin aurensa ya samu komai na jin dadin rayuwa a tunaninsa mace ta gari itace kadai bukatarsa awajen allah sai kuma gashi allah ya amshi addu'arsa, to saidai kash abunda akaso ya faru ba shine ya faruba bayan anyi aure nanfa wannan jarumin ya sake fahimtar hankali bazai taba kwanciyaba har sai anyi farin ciki da iyali shikuwa farin ciki da iyali bazai taba samuwa ba har sai an magance matsaloli a bangaren kwanciya.


Na kirashi da gwarzon namiji ne saboda shine mutum na farko da yayi tattaki har saida takai ga ya ketare iyakar kasar sa ya shiga wata kasar domin magance matsalolin iyalinsa wanda acewar mata wannan ba dabi'ar maza bane suna ganin matsalolin aure na mata ne

Harma suna ganin idan namiji yaga mace ta kasa gyara matsalarta tofa zabi biyu zai bata kodai ya kara aure ko kuma tasan yanda dare yayi mata amma a yau wannan jarumin ya karyata wannan hasashen yayi kaca kaca da kundin shi kadai ya samarwa gidansa da matarsa farin ciki.

 

DAREN FARKO

Abu na farko da wadannan ma'auratan suka fuskanta shine lokacin saduwar farko yanda biyan bukatar su ta gagara saida suka dauki sama da mako biyu wannan mijin bai samu damar shiga ba domin a daidai lokacinda yake yunkurin sakawa zafi takeji kofar wajen ta toshe wannan yasa dole saida ya bincika littattafai na baya dana wallafa inda ya samu bayanai akan yanda ake magance matsalar wato amfanida man zaitun bayan an hadashi da zuma kadan an dafa sai mace ta shafa awajen kafin lokacin saduwa wajen zaiyi laushi sannan dole wajen samun santsi ma'aurata su rage amfanida miyau na baki don idan yayi yawa yakan iya haifarda kaikayi da rashin ni.ima kuma wadanda suka fuskanci wannan matsalar yanada kyau mace ta dage dashan kayan karin ni,ima sosai hakan zai kawo saukin al'amarin


Sannan akwai abunda sabon aure ke tsammani a zaman aure shine jin dadi dari bisa dari wanda kuma azahiri ba hakan bane, dole arinka fuskantar kalubale a rayuwar zaman aure kamar ta fuskar zashigtakewa

Continue reading...

AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM

AMFANIN KUBEWA A JIKIN DAN ADAM
-----+-+++++++++++-----------------------

1. Ana amfani da kubewa wajen maganin ciwon sugar wato Diabetes. Saboda abinda ake kira (fiber ) a cikinta, na amfani wajen daidaita yawan suga a cikin jiki, wandakuma ke rage karfi ciwon sugar ko ma
maganinsa.

2. Masu ciki kan iya amfani da kubewa domin ingancin lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki domin kubewa na kunshe da dimbin Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki (cells) da kuma ( folates) don haka kubewa na hana haihuwar jariri mai dauke da wasu nakasu a jikinsa kuma na sa jaririn ya girma a ciki kuma da koshin lafiya yadda ake so.

Haka kuma jaririn da ke ciki zai iya amfana da dimbin Vitamin C dake cikin kubewa domin kare lafiyarsa.

3. Kubewa na maganin ciwon koda. Wani bincike daga jami’ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da wannan. Binciken. Ya nuna cewar wadanda suke ci ko shan kubewa a kullun sun nuna nasarar rashin lalacewar koda musamman wadanda ke da ciwon sugar domin kusan kasha 50 na masu matsalar koda sun samu matsalar ne saboda suna da ciwon sugar.

4. Kubewa na kara lafiyar dubura (colon) wato karshen babban hanji.yana wanke hanji da tumbi sosai don haka yana maganin kumburin ciki.

Kuma Vitamin A da ke cikin kubewa na taimakawa lafiyar wani abu kamar majina (Mucous membranes) na cikin babban hanji.

5. Kubewa na maganin Asthma da wasu cututtukan numfashi. Yana dauke da Vitamin C da ke taimakawa hanyoyin numfashi.

6. Kubewa na kara ingancin fatan jikin mutum yay i laushi da santsi kamar yaukin kubewa. Ka ga mutum kullun kamar yaro ko yarinya a fatarsa.

Yana kuma taimakawa wajen mayar da fatar da ta lalace (Meosis).

7. Yana matukar maganin Anaemia wato karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfaani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har yayi maka lahani ba (blood coagulation).

8. Yawan sha ko cin kubewa na matukar rage nauyin jiki ga wadanda suke jin kiba ya musu yawa.

Naku: Jamilu Gora
Continue reading...

YA SAKE MU SAKI DAYA, SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADONSA?

*YA SAKE MU SAKI DAYA, SAI YA MUTU KAFIN MU GAMA IDDA, KO MUNA DA GADONSA?* 

*Tambaya:*


Malam mutum ne yana cikin halin rashin lafiya, ya saki matansa har guda biyu saki daya, kuma bai dawo da su  ba har ya mutu, kuma ba su gama iddah ba, yaya za'a yi ? za su yi masa takaba, kuma suna da gadonsa, ko ko a'a ?


*Amsa:*


To dan'uwa mutukar yadda ka sifanta, haka abin yake, to za su bar iddar saki, su koma iddar mutuwa, kuma za su ci gadonsa, saboda suna nan a matansa, tun da saki daya ne, Ibnu-khudamah  ya hakaito ijma'in malamai akan  haka.


Don neman Karin bayani duba : Al-mugni 8\94.


Allah ne mafi sani .


9\5\2015

Amsawa: Dr Jamilu zarewa.

Continue reading...

AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM

AMFANIN ZAITUN DA MAN ZAITUN GA DAN ADAM.


Shidai zaitun itaci- yace mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan Adam , kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninta acikin ALKUR'ANI MAI GIRMA_

.

_haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan *Manzon Allah (ﷺ)an karbo daga sayyadina umar yana cewa Manzon Allah (ﷺ)* yace kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafashi ajikinku, domin hakika shi yana daga acikin bishiya mai albarka._

 _*tirmizi ne ya ruwaito*_

.

_*DAGA CIKIN AIKIN  ZAITUN*_

.

_*́KARFIN MAZAKUTA--* Duk mutumin da ya samu kanshi a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa acikin ruwan danyan kwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum , insha Allah zai samu karfin mazakuta sosai_

.

_Kada ka gaji duk wani magani da kagani ka gwada zaka dace insha Allah_

.

_*CIWON CIKI--* Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma._

.

_Yasamu kamar sati daya yana sha ko kina sha insha Allah_

.

_*CIWON KAI--* Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare insha Allah zai samu lafiya._

.

_*CIWON HAKORI--* duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganya zaitun da ya'yan habbatussauda ya sakasu acikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah._

.

_*CIWON HANTA--* duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan manzaitun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare._

.

_*CIWON DADASHI--* Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi._

.

_*CIWON SUKARI--* duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci insha Allah_

.

_*CIWON ASMA--* duk mutumin da wannan ciwon ya kamashi ,to sai ya samu ganyen zaitun ko ya'yan sa ya dinga turara wa._

.

_*CIWON KODA--* duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana insha Allah._

.

_*CIWON BAYA--* duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaba ya dinga shafawa abayan insha Allah._

.

_*CIWON RAMA--* duk mutumin da yaga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku insha Allah zaiyi kiba._

.

_*ZAZZABI MAI ZAFI--* duk mutumin daya kamu da zazzabi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya sannan yana karanta ayatul kursiyyu sau  yana tofawa acikin yana shafe jikinsa dashi insha Allah._

.

_*KYAWUN FUSKA--* Duk mutumin da yake so fuskar sa tayi kyau, tayi fari Wanda bazai cutaddashi ba, to yadinga shafa man zaitun Dana habbatussauda in zai kwanta bacci bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo zai mamakin yadda fuskarsa data koma._

.

_*ZUBEWAR GASHI--* duk mutumin da gashinta baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zube , to saita samu ruwan zafi ta wanne kanta dashi sannan bayan ya dan bushe saita zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kannata dashi gaba daya kullum._

.

_*KARANCIN JINI* duk mutumin da yake da karanci jini a jikinsa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a Rana._

.

_*BAYAN GIDA MAI KAURI BASUR* duk mutumin da yake shan wahala in yazo zaiyi bayan gida, wani ma sai Yayi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatus sauda ya kwaba sai ya turashi acikin duburarsa._

.

_*CIWON MARA GA MATA* duk matar da take haila tana fama da ciwon Mara saboda fitar jini in tana so ta samu saukin wannan ciwon ,saita samu man zaitun tana hadawa da ruwan tsamiya tana sha, insha Allah duk lokacin da zatayi haila bazai Mata ciwo ba._

.

_*SANYIN KASHI* duk mutuda kashinsa yayi sanyi baya iya motsashi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha yana kuma shafawa a wajan insha Allah ._

.

_*KYAWUN FATA DA LAUSHINTA,* Duk mutumin da yake so fatarsa tayi laushi da kyau, to sai ya sami man ya dinga shafe jikinsa dashi bayan Yayi wanka da ruwan dumi, zai yi mamaki yadda fatarsa zata koma insha Allah_

.

_*KURAJEN KARZUWA* duk mutumin da yake da karzuwa ko wasu kuraje ko sabon miki, to sai ya samu ganyan zaitun ya kirbashi ya hada da garin habbatussauda yana shafawa awajan har ya warke._

.

_*CIWON KUNNE* duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya Bari in zai kwanta bacci sai a dinga hada man zaitun Dana habbatussauda yana digawa a kunnensa insha Allah._

.

_*CUTAR KYASFI* duk mutumin da yake da KYASFI ajikinsa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe ,ya dakashi yayi laushi sai ya hada shi da man zaitun ya cakuda, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta bacci.sai ya wanke_

.

_*SHAFAR ALJANU* duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun saboda aljanu basa sonshi, shida habbatussauda_

.

_Da haka yana da kyau mutum ya lazimci amfani da su akowane hali, in da hali ma ya mai dasu mansa na shafawa amma yana da kyau kafin a Fara shafawa a karanta ayoyin rukya sai a nemi addu'a._

.

_*CIWON KARKARE* Duk mutumin da ciwon karkare yasa meshi, to sai ya samu man zaitun, sannan asamu lalle a kwaba, sai azuba man zaitun din acikin lalle a gauraya, sannan a karanta (AYATUL KURSIYYU) sau  a tofa a ciki sannan sai a tofa ajikin wannan karkare insha Allah_

.

_*CIWAN NONO* Duk matar da take fama da ciwan nono saboda rashin zubar, to Ana hada man zaitun da garinsa, abarbada akan nonon saboda samun damar zuba, dan kofofin su bude._

.

_*MOTSA SHA'AWA* Man zaitun yana motsa sha'awa in an shafashi lokacin da ake yin wasa._

.

_*CIWAN SAIFA* duk mutumin da yake ciwan saifa, sai ya hada man zaitun da garin habbatussauda da kuma zuma farar saka ya sha, insha Allah._

.

_*TSUTSAR CIKI* duk mutumin da yake da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaba su yasha, wannan tsutsar zata mutu._

.

_*CIWAN HANJI (ULCER)* Duk mutumin da yake da gyanbon ciki, to sai ya samu garin habbatus sauda kamar cokali daya sannan ya samu garin (kumasari)da ganyan zaitun mai laushi yaji kasu ya dinga sha har sai ya warke._

.

_*FITSARIN KWANCE* Duk yaro da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun Dana habbatussauda a zuba a nono a dinga bashi yana sha zai dai na. Insha Allah_

.

_*MUTUWAR JIKI* Duk mutumin da jikinsa yake yawan mutuwa to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda zaiji karfin jikinsa._

.

_*YAWAN ZABBABI* duk mutumin da yake yawan yin zazzabi , to saiya samu garin habbatussauda kamar cikin ludayi ya kwaba da ruwan zafi, da kuma zuma maras hadi ya dinga sha insha Allah_

.

_*CUWON GABOBI* Duk mutumin da gabobinsa suke ciwo to saiya samu garin habbatussauda da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a GABOBI._

.

_*KWARKWATA* duk matar da take fama da kwarkwata kuma har take son rabuwa da ita, to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaba sannan sai ta Bari sai Rana ta take sai ta zubar wannan man a kannata ta barshi yayi kamar minti (20) sannan sai ta wanke insha Allah zata ban kwana da kwarkwata._

.

_*CIWAN TARI* duk mutumin da ya kamu da kowanne irin Tari to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da yar'citta da tsamiya da zuma, sai ya hadasu guri daya ya cakuda ya dinga ci insha Allah._

.

_*MAJINAR KIRJI* duk mutumin da yake yawan majinar kirji to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya hada ya dinga ci kullum sau biyu (2) safe da yamma._

.

_*TARIN FUKA* Duk Wanda yake tarin huka to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya kullum._

:

_*Allah ta'ala yasa mudace*_


_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

*-----------------------------------*

        ​

Continue reading...

ZAN IYA SADUWA DA MAI HAILA IDAN NA SANYA CONDOM?D

*ZAN IYA  SADUWA DA MAI HAILA, IDAN NA SANYA CONDOM ?*


*Tambaya:*


Salam. Malam Allah ya karama daukaka da imani. Ga tambayata: Shin mutum zai iya saduwa da matarsa idan tana Haila matukar yasa Condom?


*Amsa:*


To dan’uwa bai halatta ka sadu da mai haila ba ko da kuwa ka sanya Condum, saboda Allah ya haramta saduwa da mai haila, kuma ya kira jinin haila a aya ta 222 a suratul. Bakara da cuta, sannan ya rataya halaccin saduwa da mace mai haila da abubuwa biyu wato: yankewar jini da kuma yın wanka.

Ba namiji ne kadai haila take iya cutarwa ba, idan ana saduwa da mace mai haila mahaifarta za ta takure sai jini ya barke mata, wannan sai yake nuna cewa: ba za’a sadu da mace mai haila ba ko da an sa Condum .


Allah ne mafi sani.


*Dr. Jamilu Zarewa*

28/11/2015


Ku kasance Damu a shafin mu na Facebook ta wannan link dake kasa👇🏿👇🏿👇🏿

http://Facebook.com/ibnhujjahislamic  .                                         

Continue reading...

MIJINA ZAI IYA SIYAN KWANAN KISHIYATA, DON YA KWANTA DA NI?

*_MIJINA ZAI IYA SIYAN KWANAN KISHIYATA, DON YA KWANTA DA NI?_*

 *Tambaya*
Slm
ya halasta miji yasai kwanan kishiyanki ya biyata don ya kwana dake?
*Amsa:*
Wa'alaikum as salam, ban San dalilin da ya nuna ana sayen kwana ba, amma za'a iya nema mace ta sarayar da hakkinta na kwanan, in har ta bayar ya bayu, tun da hakkinta ne, kamar yadda Nana Sauda ta bawa Nana A'isha kwananta, saboda tsananin son da ta ga Annabi S.A.W yana Mata.
Wannan yasa Annabi S.A.W yake kwana biyu a dakin Nana Aisha kamar yadda ya tabbata a Bukhari, ragowar matansa bakwai kuma yana musu kwana dai-dai, Nana Saudat kuwa ba ya kwana a dakinta, bayan ta bawa Nana Aisha kwananta.
Allah ne mafi sani
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Continue reading...

YAUSHE ZA KA IYA ZAMA MUFTY?

*_YAUSHE ZA KA IYA ZAMA MUFTY?_*
Imamu Ahmad yana cewa bai kamata mutum ya zama mai fatawa ba, har sai an samu siffofi guda biyar tare da shi:
1. Ya zama mai tsarkakakkiyar niyya, domin in ba shi da tsarkakakkiyar niyya to ba za'a samu haske a tare da shi ba, kamar yadda ba za'a ga haske a zancensa ba.
2. Ya zama yana da ilimi da juriya da nutsuwa.
3. Ya zama ya san abin da zai yi fatawa akai yadda ya kamata.
4. Ya zama yana da rufin asiri, in ba haka ba mutane za su taune shi.
5. Ya zama ya san mutane yadda ya kamata.
Ibnul kayyim yana cewa: wannan yana nuni zuwa girman Imamu Ahmad, da kuma matsayinsa wajan ilimi, saboda wadannan abubuwan guda biyar su ne turakun fatawa, duk abin da ya samu nakasu a cikinsu to hakan zai haifar da nakasu a fatawa.
16/10/2012
Amsawa: Dr Jamilu zarewa.

Continue reading...

BANA SHA AWAR NAMIJI SAM-SAM , ZAN IYA CIGABA DA ZAMA DA MIJINA A WANNAN HALIN?

*_BANA SHA’AWAR NAMIJI SAM-SAM, ZAN IYA CIGABA DA ZAMA DA MIJINA A WANNAN HALIN?_*
*Tambaya:*
Mata ce da mijinta suke zaune amma kuma matar bata da sha awar namiji ko kadan, ya zamana zaman nasu ya zama mara dadi, tana ganin kamar tana cutar mijinta tunda shi yana da sha awa, shin zamansu ya halatta kuwa a addini?
*Amsa:*
In har shi ya kan neme ta in sha’awarsa ta tashi, kuma ta biya masa, babu laifi şu ci gaba da zama tare, tun da za ta kare shi daga fadawa cikin haramun, sannan akwai mata da yawa da Allah ya halicce su a wannan yanayin.
Zamanku zai iya zama cuta ne in har ya kasance ba kya biya masa bukata ta yadda zai kalli matar da bata hallata a gare shi ba.
An shar’anta aure ne saboda samun zuriyya da kuma katange ma’aurata daga zina, kamar yadda ya tabbata a dalilan sharia, duk auren da ya gaza cika wadannan manufofi akwai matsala a cikin shi.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Continue reading...

SHIN ZAMU IYAYIN WANKA DA RUWAN ZAMZAM?

*_SHIN ZAMU IYA YIN WANKA DA RUWAN ZAMZAM?_*
*Tambaya*
Shin Malam zamu iya yin wanka da Ruwan Zam-Zam?
*Amsa*
To dan’uwa ruwan Zam-Zam ruwa ne mai albarka, kamar yadda ya zo a hadisi cewa: Waraka ne ga cututtuka, Suyudi ya kyautata shi a Jami’ussagir, duba Faidhu Alkadeer 3/489.
Saidai duk da haka ya halatta ayi wanka da tsarki da shi a zance mafi inganci, saboda ba’a samu dalilin da ya hana hakan ba, ga shi kuma daga cikin ka’idojin malamai duk abin da ba’a samu nassin hani akansa ba a cikin mu’amalolin mutane, to ya halatta.
Sannan sahabbai sun yi tsarki da ruwan da ya bubbugo daga hannun Annabi S.A.W, ruwan Zam-Zam kuma ba zai fi wannan ruwan daraja ba.
Don neman Karin bayani duba: Hashiyatu Ibnu-abiidin 1\180 da kuma Insaf 1\27.
Allah ne mafi Sani
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Continue reading...

ZA MU IYA FATAUCIN FATUN JAKUNA!!

ZA MU IYA FATAUCIN FATUN JAKUNA!!

 Tambaya:
Assalamu Alaikum. Sheikh don Allah menene hukuncin siyar da FATUN JAKI a musulunci???
Ina da 'yan uwa da suke sayen fatun jaki ne a Taraba,suna kaiwa China. Shine nake son nasan hukuncin cinikin don nice mai bada jarin.
'Yar uwarku a Musulunci UMMU FATIMAH DARMA.
Amsa:
Wa'alaikum as salam, akwai zantuttukan malaman fiqhu da yawa game fatar dabbar da ba'a cin namanta idan ta mutu, saidai abin da yafi zama daidai shi ne: Duk fatar da aka jemeta to tabbas ta tsarkaka, kamar yadda hadisin da Muslim ya rawaito ya ambata hakan, don haka fatar jaki ana iya amfana da ita, kuma a sayar da ita mutukar an jeme ta jemewar da sharia ta yarda da ita.
Allah ne mafi Sani.
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Continue reading...

INA SO NA SAN YADDA AKE ISTIBRA'I?

*INA SO NA SAN YADDA AKE ISTIBRA'I?*
*Tambaya*
Assalamu ahlaikum Don girman Allah ina da tambaya ina so na san yadda ake istibra'i da kuma dokokin su. nagode
*Amsa*
Wa'alaikum assalam, ana yin istibra'i ne da jini daya a zance mafi inganci,yana kasancewa ne ga matar da ta ta yi zina take so ta tabbatar ciki bai shiga ba, kafin ta yi aure, kamar yadda yake wajaba ga baiwar da mai gidanta ya sayar da ita bayan ya take ta ta yi, kafin ubangidan ta na biyu ya fara saduwa da ita, saboda kada a samu cakuduwar nasaba.
Allah ne mafi Sani
06/02/2016
*Dr. Jamilu Zarewa.*
Continue reading...

WANDA YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU !!!

*WANDA YA SAKI MATARSA A RUBUCE TA SAKU !!!*
*Tambaya*
Assalamu alaikum malam don Allah yaya wannan yake? Miji ne yayi Sakin da ba a furta ba kawai ya rubuta ne shin tasa ku?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, ta saku mana, saboda rubutu yana daidai da furuci a musulunci, Annabi s. a. W. yana cewa "Allah ya yiwa Al'uma rangwame akan abin da ta riya a zuciyarta, mutukar ba ta furta ba ko ta aikata.
Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: idan ya Saki matarsa a rubutu ta saku, saboda duk masu hankali sun cimma daidaiton cewa rubutu aiki NE, shi kuma ya yi aiki.
Yana daga cikin Ka'idojin Shariar da malamai suka fada a littattafan fiqhu:Rubutu kamar magana NE.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
Continue reading...

NEMAN TSARI DAGA ABUBUWA GUDA HUDU.NEMAN TSARI DAGA ABUBUWA GUDA HUDU.

NEMAN TSARI DAGA ABUBUWA GUDA HUDU.

 1-Azabar Qabari
2-Azabar wutar Jahannama
3-Fitinar Rayuwa da Mutuwa
4-Fitinar Masihil Dujal...
Annabi SAW ya kasance yana neman tsari Allah daga abubuwa guda hudu,acikin tahiyarsa ta karshe,acikin kowace Sallah,kuma yayi umarnin hakan ga Sahabbansa RA.
Daga Abu Hurairata RA yana cewa,Annabi SAW yana cewa:
*(Idan Dayanku zaiyi tahiya to ya nemi tsarin Allah daga Abubuwa guda hudu*
Yace:
" ((ﺍﻟﻠﻬﻢﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫﺑﻚﻣﻦﻋﺬﺍﺏﺍﻟﻘﺒﺮﻭﻣﻦﻋﺬﺍﺏﺟﻬﻨﻢﻭﻣﻦﻓﺘﻨﺔﺍﻟﻤﺤﻴﺎ ﻭﺍﻟﻤﻤﺎﺕﻭﻣﻦﺷﺮﻓﺘﻨﺔﺍﻟﻤﺴﻴﺢﺍﻟﺪﺟﺎﻝ))
@Bukhari da Muslim.
Ibn Uthaimeen Allah yayi masa Rahama yana fada:
*"Wadannan Zikiran Neman tsarin gudu hudu,mutum zai fadesune Karin Sallama kuma suke zikirai na karshe cikin tahiya wanda da ka furtasu sai yin Sallama.
Hakika Malamai sun sami sabani wajan hukuncin wadannan zikirai shin wajibine?ko kuma Sunnace?,kuma mafi yawan Malamai sun tafi akan yinsu sunnane,ba wajibi bane,wadansu kuma bangaran daga Malamai Suna ganin yinsu wajibine,wanda ya barsu baiyiba Sallarsa ta baci sai ya sake wata.
Imam Dhawus Allah ya jikansa yana cikin Manyan Tabi'ai ya umarci dansa da ya sake Sallah saboda ya ki karanta wadannan azkar acikin tahiyarsa ta karshe acikin Sallarsa.
Dan Haka yana da kyau mutum yayi kokari kiyaye karanta wandannan zikirai domin dacewa da falalar da alkhairi mai yawa na wannnan azkar.
Yin hakan zai sanya ya kubuta daga rashin ingancin Sallah ga wanda bai karantaba,kamar yadda wadansu Malaman suke fada.
@Sharhin Riyadus Saliheena Na Ibn Uthaimeen Vol 5.
Allah ka bamu ikon Dacewa .
Continue reading...

NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO AKWAI DAMAR KOME ?

NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO AKWAI DAMAR KOME ?
Tambaya :
Assalamu alaikum don Allah malam ka warware mana wannan matsala, yanzu haka muke cikinta, mutum ne ya sake matarsa shika Daya 1, ya koma da ita bayan wasu shekaru ya sake mata shika daya, har idarta ya kare ya sake biyan sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake rabuwa shika daya 1, kuma suna son junansu akwai aure a tsakaninsu ko sai ta sake auren wani ? shikan bayan da ya mata har idarta ya kare aka sake daura aure a matsayin shika nawa ne yake kanta nagode Allah ya kara imani da basira sai naji daga gareka
Amsa :
To dan'uwa idan abin haka yake kamar yadda ka siffanta, to babu damar kome, sai in ta auri wani mijin na daban, saboda igiyoyin da suke tsakaninku sun yanke gaba dayansu .
Auren da kuka sake, ba zai goge sakin da ka yi a baya ba, da ace ta auri wani bayan saki biyun da ka mata, kafin ka sake auranta, da ba'a kirga da saki biyun baya ba, a daya daga cikin maganganun malamai, amma tun da ba ta auri wani ba, ya wajaba ku hakurewa juna .
Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 7\388 .
Allah ne mafi sani .
Jamilu Yusuf Zarewa
Continue reading...

ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION.

ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION.
1)Rashin sanya pant.
2)Barin pant yayi dauda(Dirty) sosai ba a canja ba. Ana so in da hali kullum a canja pant sau biyu ko a wanke.
3)Saka pant a jiqe da ruwa.
4)Yawan tsarki da ruwan sanyi.
5)Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yayi yawa kwarai.
6)Rashin aski.
7)Wasa da gaba.
8)Yawan cin `Danyar Albasa.
9)Yin amfani da Magungunan mata marasa inganci.
10)Dadewa akan Masai ko toilet.
11)Rashin shan iska.
12)Musanyar tufafi.
13)Saduwa damai cutar.
12)Cutar Aljanu, wato Jinnul Ashiq. Su ma suna sanyawa mace infection mai wuyar magani.
.
.
ILLOLIN DA SANYI KO INFECTION YAKE YI WA MATA
.
1)Yana sa Rashin Sha'awa.
2)Yana sa ciwon mara mai tsanani.
3)Yana haifar da kurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki daya.
4)Yana sa mace ta dinga jinin al'ada bakikkirin maiwari.
5) Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fito mata.
6)Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta.
7)Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa.
8)Yana rikitawa mace kwanakin al'adarta, su dinga karuwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa.
9)Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta dinga fita ta gabanta.
10)Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwata-kwata.
11)In yayi karfi yana hana mace haihuwa.
12) Wani infection din alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namijin dare ko jarirai.
.
.
★Abin lura:-
★Idan mace tayi magungunan Asibiti da kuma irin wadannan da mu ka ambata amma infection din bai warke ba, to ta nemi maganin jinnul Ashiq, wato magungunan Aljanu don zai iya yiwuwa matsalarsu ce.
Continue reading...

MIYAGUN AQIDUN DARIQAR TIJJANIYA


MIYAGUN AQIDUN DARIQAR TIJJANIYA
WADANDA RIDDA NE GA DUK WANDA YA
YARDA DASU.!!!
.
1. Suna cewa " sallah cikin zawiyar shehu
tafi sallah makka da
madina, domin yazama dole Allah ya karba".
(FATHU RABBANY.
Shafi na 60).
.
2. Suna cewa wai"matsayin tijjani yafi na
annabawa 40, a aljanna".
.
Wal'iyazu biLLAH. Waye shi da har xaku
kamanta shi da annabi.???
( YAKUTATIL FAREEDAH. shafi na 5,).
.
3. Sunce wai " waliyi yana fitowa daga
kabarin shi domin amsa kiran mai bukata".
Mu Kuwa (ahlussunah) munsan Allah ne
kawai ke karba kiran mai bukata, Waliyi bai
isa ba yayi karya.(ALFAUZU WANNAJAT shafi
na 891).
.
4. Suna cewa " salatil fatihi tana dai dai da
Alkur'an sau 6000"
Wanda munsani salatil fati karya ce 100%.
(duba shafi na 631, ALATTAFIN JAWAHIRU)
.
5. Suna cewa" badan tijjani ba, da halittu
basu rayu ba, kuma shine
halifan annabi" ( duba shafi na 751, AKWAL
ADILLATY WAL BARAHIN).
.
6. Ibrahim (Assingaly INYASS), yace: shine
ruhin duk kan halittu,
(ba mai rayuwa sai da shi) wannan yana
tabbatar mana da abunda
mai wakar LAM YALID WALAM YULAD yake
fada gaskiya ne.
.
(AFDALUL WASA'IL, shafi na 181, Wanda ilyas
tukur ya wallafa aka
Buga a masar ).
.
7. Suna cewa wai duk daraja da matsayi da
hadisil kudsiy yake
dashi salatil fatihi ma yana da shi, domin
matsayin su daya.ka
duba (ALKHULASAT ALWAFIYYA. na Muhd
Sa'ad, sahafi na 16,
Wanda aka buga a Sudan).
.
8. Sunce wai duk, tasarrufin da halittun
Sama da Kasa sukeyi. Wai wannan duk aikin
tijjani ne. Wannan maganar tana cikin littafin
su
( YAKHTATIL FAREEDAH shafi na 11)
.
9. Suna sawa wa waliyan su sunayen Allah
kai tsaye, kamar yanda sukace, Albasidu
sunan tijjani ne.( ﺗﻌﺎﻟﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻤﺎ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ )
.
KITADU MAULUDI TIDJANY na Muhd
shankidiy, shafi na 43)
.
10. Wai Dan tijjaniyya ko da ya kashe rayuka
70 ba Zai shiga wuta ba, Wanda wannan ya
sabawa akidar musulunci.(MUNI'ATUL
MURID shafi na 46).
.
Wannan fa kadan kenan kuma masu saukin
kenan amma sannu
ahankali zamu kawo wadanda sukafi
wadannan.
.
Allah ya tsaremu da wannan mugunyar
Aqidah.
Continue reading...

Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe


Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe
.....An kuma Umurci Iimamai su ware lokaci domin wayar da kan Al'umma akan katin zabe (PVC)
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban kungiyar Wa'azin musulunci, mai Da'awar tuge bidi'ah, ta tsaida Sunnar Annabi Muhammadu (S), Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga shugabannin addini, Limamai da sauran masu fada aji a dukkan matakai, da su dinga wayar da kan Al'ummar musulmi a masallatai, makarantu da sauran wuraren tarukan addini akan muhimmancin yankan katin zabe c(PVC) a wannan lokaci da muke ciki.
Sheikh Bala Lau yayi wannan kiran ne a wata tattaunawa ta musamman da yayi da wakilin mu 'Ibrahim Baba Suleiman' ta wayar tangaraho a safiyar laraba.
Shehin Malamin yace, duk wanda yasan bai mallaki katin zabe ba, yayi kokari ya mallaka, domin yankar katin zabe a wannan lokaci ya zama sabon salo, idan kuwa har kuka saki jiki bakuyi ba, to yana da kyau ku ankara domin samun shugabanni na gari wadanda muke sonsu, suma suke sonmu.
Kazalika akwai wadanda suka mallaki katin zabe (PVC) amma basa zuwa rumfar zabe domin kada kuri'a, wanda hakan zai maida mu baya, musamman akan shirin da abokan zaman mu sukeyi domin su mallaki katin zabe, dan haka a daure a kada kuri'u ranar zabe ba tare da gajiyawa ba.
A karshe Sheikh Bala Lau ya umurci Shugabannin jihohi da su umurci shugabannin kananan hukumomi su wayar da kan Al'umma a yankunan su a dukkan matakai na shugabanci da sauran mabiya. Kazalika Sheikh Lau ya sake umurtan Limaman Juma'a da su ware lokaci a cikin hudubobin su na juma'ar dake gaban mu, domin fadakar da Al'umma akan muhimmancin yankan katin zabe.
Allah ya zaba mana shugabanni na gari, ya gyara mana kasar mu, ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a kasa. Amin
Continue reading...

Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe



Anyi kira ga Shugabannin addini su wayar da kan mutane akan mallakar katin zabe
.....An kuma Umurci Iimamai su ware lokaci domin wayar da kan Al'umma akan katin zabe (PVC)
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Shugaban kungiyar Wa'azin musulunci, mai Da'awar tuge bidi'ah, ta tsaida Sunnar Annabi Muhammadu (S), Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga shugabannin addini, Limamai da sauran masu fada aji a dukkan matakai, da su dinga wayar da kan Al'ummar musulmi a masallatai, makarantu da sauran wuraren tarukan addini akan muhimmancin yankan katin zabe c(PVC) a wannan lokaci da muke ciki.
Sheikh Bala Lau yayi wannan kiran ne a wata tattaunawa ta musamman da yayi da wakilin mu 'Ibrahim Baba Suleiman' ta wayar tangaraho a safiyar laraba.
Shehin Malamin yace, duk wanda yasan bai mallaki katin zabe ba, yayi kokari ya mallaka, domin yankar katin zabe a wannan lokaci ya zama sabon salo, idan kuwa har kuka saki jiki bakuyi ba, to yana da kyau ku ankara domin samun shugabanni na gari wadanda muke sonsu, suma suke sonmu.
Kazalika akwai wadanda suka mallaki katin zabe (PVC) amma basa zuwa rumfar zabe domin kada kuri'a, wanda hakan zai maida mu baya, musamman akan shirin da abokan zaman mu sukeyi domin su mallaki katin zabe, dan haka a daure a kada kuri'u ranar zabe ba tare da gajiyawa ba.
A karshe Sheikh Bala Lau ya umurci Shugabannin jihohi da su umurci shugabannin kananan hukumomi su wayar da kan Al'umma a yankunan su a dukkan matakai na shugabanci da sauran mabiya. Kazalika Sheikh Lau ya sake umurtan Limaman Juma'a da su ware lokaci a cikin hudubobin su na juma'ar dake gaban mu, domin fadakar da Al'umma akan muhimmancin yankan katin zabe.
Allah ya zaba mana shugabanni na gari, ya gyara mana kasar mu, ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a kasa. Amin
Continue reading...

ZAN IYA YIN MAGANA A PRE- HUDBA

*_ZAN IYA YIN MAGANA LOKACIN PRE-KHUDBA?_*


*Tambaya*

Asalamu Alaikum.
Allah ya karawa malam Fikira da Fasaha. Idan mutum yazo masallacin jumaa ya samu ana pre-khudba shi kuma yana so ya karanta S Kahfi, to zai iya karantawa ya jiyar da kansa sautin karatun koda na kusa dashi suna ji?


*Amsa*
Wa'alaikum assalam, zahirin hadisin da ya zo akan hana yin magana lokacin da ake hudubar juma'a bai game har da pre khudba ba, don haka za ka iya yin magana, ko ka karanta alqur'ani a lokacin da ake yinta.

Pre-khudba ta banbanta da huduba, saboda akan yi ta kafin Muktarin Juma'a ya shiga, sannan a lokuta da yawa za ka ga ba liman ne yake yi ba, Hani da umarni a shari'a abu ne da yake hanun Allah da manzonsa, wannan ya sa za'a takaita a inda ya zo a nan.
Hadisin ingantacce ya tabbatar da cewa : sai liman ya hau minbari zai fara huduba sannan mala'iku suke nannade takardun su, su zauna su saurari wa'azi da ambaton Allah, wannan sai ya nuna Pre-khudba ba ta daukar hukuncin hudubar juma'a wajan wajabta yin shiru da sauraro.

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

*DAGA ZAUREN*
����نساء اهل الجنة����
����رجال اهل الجنة����
*DOMIN SHIGA WANNAN GROUP* 08029399000 ko 08143979048
Continue reading...
 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *