HotBreaking News
Fetching data...

DAGA CIKIN BANBANCIN ANNABI DA WALIYYI

DAGA CIKIN BANBANCIN ANNABI DA WALIYYI

Shehul Islami Ibnu Taimiyya ya ce:
ﻗﺪ ﺍﺗﻔﻖ ﺳﻠﻒ ﺍﻷﻣﺔ ﻭﺃﺋﻤﺘﻬﺎ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﻛﻞ ﺃﺣﺪ ﻳﺆﺧﺬ ﻣﻦ ﻗﻮﻟﻪ ﻭﻳﺘﺮﻙ ﺇﻻ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ . ﻭﻫﺬﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﻔﺮﻭﻕ ﺑﻴﻦ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ ﻭﻏﻴﺮﻫﻢ ﻓﺈﻥ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ ﺻﻠﻮﺍﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﺳﻼﻣﻪ ﻳﺠﺐ ﻟﻬﻢ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﺑﺠﻤﻴﻊ ﻣﺎ ﻳﺨﺒﺮﻭﻥ ﺑﻪ ﻋﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰ ﻭﺟﻞ ﻭﺗﺠﺐ ﻃﺎﻋﺘﻬﻢ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﻪ؛ ﺑﺨﻼﻑ ﺍﻷﻭﻟﻴﺎﺀ ﻓﺈﻧﻬﻢ ﻻ ﺗﺠﺐ ﻃﺎﻋﺘﻬﻢ ﻓﻲ ﻛﻞ ﻣﺎ ﻳﺄﻣﺮﻭﻥ ﺑﻪ ﻭﻻ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﺑﺠﻤﻴﻊ ﻣﺎ ﻳﺨﺒﺮﻭﻥ ﺑﻪ؛ ﺑﻞ ﻳﻌﺮﺽ ﺃﻣﺮﻫﻢ ﻭﺧﺒﺮﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﻤﺎ ﻭﺍﻓﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺟﺐ ﻗﺒﻮﻟﻪ ﻭﻣﺎ ﺧﺎﻟﻒ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻛﺎﻥ ﻣﺮﺩﻭﺩﺍ
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /11 208 )
"Magabatan wannar al'umma da Limamanta a ilimi sun yi Ittifaqi a kan cewa; kowa za a iya karban maganarsa, kuma za a iya bar masa kayansa sai dai Manzon Allah (saw) kawai. Wannan yana daga cikin abubuwa da suka banbanta tsakanin Annabawa da wasunsu, saboda Annabawa (saw) wajibi ne a yi imani da dukkan abin da suke ba da labari daga Allah Mai girma da buwaya, kuma wajibi ne a yi musu da'a cikin abin da suke umurni da shi, sabanin Waliyyai, su kam ba wajibi ba ne a yi musu da'a cikin dukkan abin da suke umurni da shi, ko yin imani da dukkan abin da suke ba da labarinsa. Kai, ana bijiri da umurnin nasu da labarin da suka bayar ne ga Alkur'ani da Sunna, abin da ya dace da su wajibi ne a karbe shi, abin da ya saba musu ya zama abin a yi watsi da shi, ko da kuwa mai shi yana cikin Waliyyan Allah".
Saboda haka, babu wani mahluki da ya isa a yi masa da'a a abin da ya saba wa Alkur'ani da Hadisi, ko da Shehin Malami ne Waliyin Allah Dan Aljanna.

Continue reading...

SHIN ABIN DA MUKE GANI DAGA 'YAN KUNGIYAR SALAFIYYUN HASADA DA ZALUNCI NE KENAN?

SHIN ABIN DA MUKE GANI DAGA 'YAN KUNGIYAR SALAFIYYUN HASADA DA ZALUNCI NE KENAN?
Sau da yawa masu bin Manhajin Guluwwi a bidi'antarwa sukan gafala, sai ka samu ba su sanin abin da suke fada. Sai mutum ya zo yana jifan Malamai da kalmomi da sunaye amma bai san cewa; bidi'antar da su yake yi ba, ko ma kafirtawa.
Misali sau da yawa za ka ji suna jifan Malaman da suke bidi'antarwa suna jarraha su da sunan "Shaidanu cikin Mutane" ( ﺷﻴﺎﻃﻴﻦ ﺍﻹﻧﺲ ) alhali suna ne na kafirai da munafukai makiya Annabi (saw).
Haka kuma suna jifan Malamai Ahlus Sunna da sunan "Ikhwaniy", "Qutbiy", "Sururiy", "Hizbiy" (Dan Kungiya), da irin wadannan sunaye, alhali ma'anarsu a wajen Malamansu shi ne Dan Bidi'a. Suna jifan mutane da su, a lokaci guda kuma suna raya cewa; su ba sa Bidi'antar da Malaman da suke jifa da wadannan sunaye. Wannan tufka da warwara ne!
Haka kuma sun siffanta da hasada da zalunci, suna hasada ga Malaman da suka sa a gaba ba tare da hakki ba, alhali malamai ne da suka sadaukar da rayuwarsu ga amfanar da al'umma a Addininsu, su kuma sun zo suna cin dunduniyarsu saboda tsananin hasada da zalunci. A kan irin haka Shaikh Ibnu Uthaimeen (r) ya ce:
ﺍﻵﻥ ﺗﺠﺪ ﺑﻌﺾ ﺍﻹﺧﻮﺍﻥ - ﻣﻊ ﺍﻷﺳﻒ - ﻳﺮﺩ ﻋﻠﻰ ﺇﺧﻮﺍﻧﻪ ﺃﻛﺜﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﺮﺩ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﻠﺤﺪﻳﻦ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮﻫﻢ ﺻﺮﻳﺢ، ﻳﻌﺎﺩﻳﻬﻢ ﺃﻛﺜﺮ ﻣﻤﺎ ﻳﻌﺎﺩﻱ ﻫﺆﻻﺀ ﻭﻳﺸﻬﺮ ﺑﻬﻢ ﻓﻲ ﻛﻼﻡ ﻻ ﺃﺻﻞ ﻟﻪ، ﻭﻻ ﺣﻘﻴﻘﺔ ﻟﻪ، ﻟﻜﻦ ﺣﺴﺪ ﻭﺑﻐﻲ، ﻭﻻﺷﻚ ﺃﻥ ﺍﻟﺤﺴﺪ ﻣﻦ ﺃﺧﻼﻕ ﺍﻟﻴﻬﻮﺩ ﺃﺧﺒﺚ ﻋﺒﺎﺩ ﺍﻟﻠﻪ . ﺛﻢ ﺇﻥ ﺍﻟﺤﺴﺪ ﻻ ﻳﺴﺘﻔﻴﺪ ﻣﻨﻪ ﺍﻟﺤﺎﺳﺪ ﺇﻃﻼﻗﺎ، ﺑﻞ ﻻ ﻳﺰﻳﺪﻩ ﺇﻻ ﻏﻤﺎ ﻭﺣﺴﺮﺓ
ﻣﺠﻤﻮﻉ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﻭﺭﺳﺎﺋﻞ ﺍﻟﻌﺜﻴﻤﻴﻦ ‏( /26 262 - 263 )
"Yanzu za ka samu wani daga cikin 'Yan uwa - abin takaici - yana raddi ga 'yan uwansa fiye da yadda yake raddi a kan Mulhidai, wadanda kafircinsu yake a fili, yana gaba da su fiye da yadda yake gaba da wadannan, yana yi musu batanci a bainar jama'a da maganar da ba ta da asali ba ta da hakika, kawai saboda hasada da zalunci. Babu shakka hasada tana cikin halayen Yahudawa mafi munin bayin Allah. Sa'annan kuma mai hasada ba zai amfana da komai a hasadar tasa ba, kai, sai dai bakin ciki da tsananin bacin rai".
Su Malaman da suke yi musu irin wannar hasada, kowa ya ga kokarinsu, na karantar da al'umma Addini da Sunna da raddi ga Bidi'o'i, sabanin masu wannan Manhaji, ba a sansu da wani abin kirki a wadannan fagage ba.
To wai shi wannan Manhaji na Guluwwi a Bidi'antarwa da sunan Manhajin Salafiyya, wanda ake ta kururuwa a kansa, don me ya sa ba za a nuna mana shi cikin Nassin Alkur'ani ko Sunna ko Ijma'i ba ne?!
Hasali ma Manhaji ne da yake kirkirarre na raba kan Ahlus Sunna, mun tabbatar da haka a lokuta daban - daban.
Continue reading...

*SHARADAN {لا اله الا الله}* ASHARADI NA FARKO:-SHINE ILIMIN MA`ANAR {لا اله الا الله) wanda shi yake kore ja hilci.

                روط لا اله إلا الله}

                شروط الاول :-العلم بمعنی[لا إله إلا إلله]

        *SHARADAN {لا اله الا الله}*

     ASHARADI NA FARKO:-SHINE ILIMIN                       MA`ANAR {لا اله الا الله)

wanda shi yake kore ja hilci.

وقال تعالی:- فَاعلَم أنَّهُ٫لَآإلَهَ إلآَ اللّه
سورة محمد ١٩    
       

allah yana cewa;-{Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa bisa can canta da gaskiya fãce Allah,}


 وقال سبحانه۔:- وَلآَیَملِكُ الذِینَ يِدعُنَ مِن دُونِهِ  الشَّفَٰعَتَ إلآَّ مَن شَھِدَ بِالحَق

allah yana cewa; {Kuma wa anda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya,}

                       أی شهدَ ب[لا إله إلا الله

allah yana cewa;-(waanda ya yi saida da gaskiya )shine wanda ya shaida da(laa ilaa ha illallah)

                      وَهُم يعلَمُون َ

kuma sũ, sunã sane (da haka)

                      یعلمون بقلوبهم معنی ها

ma`ana;-(kuma sun san ma`anarta a zuciyarsu)  

سورة۔  [الزخرف: ٨٦



وقال تعالی﴿شَهِدَ اللَّه أنَّهُ٫ لاَإلَهَ إلّا هُوَ وَلمَلَٖٓئکةِ وأُولُوا العِلمِ قَائمَابِلقِسط لا إلهَ إلا هُوَالعَزَیزُالحَکِیم
       
سورة: ال عمران:١٨



allah yana cewa;-{allah ya shaida cewa :Lalle ne babu abin bautawa bisa can canta da gaskiya face shi,kuma mala`iku da ma`abota ilimi sun shaida,Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa da daskiya bisa can canta face shi, mabuwayi mai hikima}.

وقال تعالی:﴿قُل هَل یَستَوِی الَّذِنَ یَعلَمُونَ والَّذِّنَ لآَ یَعلَمُون ؓإِنَّمَایَتَذَکَّرُ ٱلُألبَابِ﴾                سورة:الزمر:٩]

allah yana cewa;-{kace "Ashe wadanda suka sani,suna daidai da wadanda basu sani ba?" Masu hankali kawai ke yin tunani}.

وقال تعالی﴿إنَّمَایَخشَی اللَّهُ مِن عِبَادِهِ ٱلعُلَمَٶٰ﴾            
 سورة: فاطر :٢٨

allah yana cewa;-{malamai kawai ke tsoron allah daga cikin bayinsa.}



mungama da ayoyi yanzu zamu fara kawo hadisai in sha allahu.



وعن عثمان بن عفان رصی الله عنه قال :قال رسول الله صلی الله علیه وسلم(من مَن مَاتَ وَهُوَ یَعلَمُ أنَّهُ لآ إلهَ إلاَّ اللَّه دَخَل الجَنَّة)  اخرجه مسلم: ٢٦]



Ankarbo daga usman dan affan, allah ya karamasa yarda, yace;-manzon allah (s.a.w), yace {duk wanda ya mutu,al-halin shi  yasan ma`anar kalmar(لا إله إلا الله), to zai shiga aljannah,(muslim ne ya rawato).



فقَیَّدَهَا بالعِلمِ بِمَعنَاها،وَهو نَفیُ العِبَادَةِ عن کُلِ مَا سوَیٰ اللهِ عزٰ وجلٰ،وإثبَاتُها اللهِ وحدَهُ لا شرِیكَ لَهُ.

a wanna hadisin sai aka kayyade shiga aljannah  da ilimin ma`anarta,

ilimin ma`anarta shine ;-kore duk wata bauta ga wanda ba allah ba,sannan,da tabbatar da ita(bautar)ga allah shi kadai,bashi da abokin taraiyya,

idan mutum yana fadarta abaki amma baisan ma´anarta ba, to.. wanna baza ta kare shi da komaiba,

misali;-kamar mai surutu acikin bacci kunga ai wannan baisan mai yake fada ba kuma maganr da yakeyi bazata amfanar da shiba

أم کیف یَعمَلُ بمقتَصَی ماَ لا یعلمه!َ!

kokuma ta ya ya zai san abin da ta kunsa (لا اله الا لله) al halin ba shi da ilimi?!

ba wai ana nufin fadarta abaki ba tare da  jahiltar ma`anarta,

domin muna fikaima suna fadarta, al halin kuwa su suna tare da kafirai acikin wuta, kaga fadar ta abaki bai karesu daga shiga wutaba

amma abin da ake nufi shine, fadart tare da sanin ma`anarta acikin zuciyar, da tabbatar da abin da ta tabbatar, da kore abin da ta kore da kuma san kalmar da son ma`abota kalmar dakin wanda ya juya mata baya.





muna rokon allah daya datar damu da sanin ma`anarta dakuma aiki da ita ameeeeeeeeeeeeeeeen👏👏.









(IDON KANA SO KARINGA SAMUN LADAN DA BAYA YAN KEWA HAR BAYAN MUTUWARKA TO KA YA DA ILIMI MAI AMFANI TSAKANIN MUTANE)َ
Continue reading...

YA YA KAMATA NAYI DA RIBAR BANKIN DA NA AMSA?

*_YA YA KAMATA NAYI DA RIBAR BANKIN DA NA AMSA?_* 



                         *Tambaya*

Assalamu alaikum malam Menene ra'ayin malaman Sunna akan kudin da banki suke karawa mutane a cikin Saving account? Ya yakamata ayi amfani dasu? Allah ya karemu daga aikata kuskure.



                            *Amsa*

Wa'alaikum assalam Farko dai ya haramta ga musulmi ya bude account din da za'a dinga saka masa kudin ruwa a ciki, saboda Allah ya haramta cin riba ya kuma yi shirin yaki da Wanda bai daina ci ba à cikin aya ta 275 a Suratul Bakara da ayoyin da suka zo bayanta. 


Annabi S.A.W ya la'anci mai cin riba da wanda ya rubutata da wanda aka wakilta da wanda ya yi shaida akanta. Kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi ingantacce. 


Idan mutum ya amshi Interest din Banki to ya wajaba ya tuba ga Allah da niyyar ba zai sake amsa ba, tun da Allah ya Hana. 


A zance mafi inganci zai iya amfani da kudin wajan yin aikin da zai amfani jama'a kamar gina Asibitoci ko kwatar da ruwa zai wuce ko kuma hanyoyin da mutane za su bi su wala, saidai ba shi da ladan wannan aikin da ya yi, saboda ba dukiyarsa ba ce.


Wannan ita ce maganar manyan malaman musulunci na wannan zamanin kamar Sheik Ibnu Bazz da sauransu. 


Allah ne mafi sani.


27/07/2017


Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

KA JE MAHAIFIYARKA TA YI MAKA ADDU'A

*KA JE MAHAIFIYARKA TA YI MAKA ADDU'A*


Al-Imam Sulaim dan Ayyub Ar-Razi, daya daga cikin manyan malaman Mazhabar Shafi’iyya (Ya rasu a shekara ta 447 BH). Yana cewa:

“Lokacin da nake yaro karami dan shekar goma a garinmu (Ar-Rayy) (Cikin kasar Iran a yanzu), sai wani bakon malami ya ziyarci garin yana koya wa yara karatun Alkur’ani. Sai ya ce min: “Matso kai ma ka karanta”. Sai matsa, na yi ta kokarin in karanta Fatiha amma na kasa, domin harshena ya yi nauyi sosai. Sai ya ce min: “Shin kana da mahaifiya a raye?” Sai na ce masa, e, ina da ita. Sai ya ce: “Ka je wurinta ta yi maka addu’a Allah ya arzutaka da karatun Alkura’ni da na ilimi”. Sai na ce, to. Sai na koma gida na roke ta ta yi mini addu’a, sai ta yi min. 


Sai ga shi na girma har na tafi garin Bagdaza na yi karatun harshen Larbaci da na Fikihu, sannan na dawo garinmu Ar-Rayy. 


Wata rana ina zaune a masallacin Juma’a, muna karanta littafin ‘Muhktasar’ na Muzani, sai ga malamin nan mai koyar da karatun Alkur’ani ya shigo masallacin, ya nufo inda muke ya yi mana sallama, muka amsa masa, amma bai gane ni ko wane ne ba, don ya manta abin da ya faru a can baya da jimawa.  Ya ga muna karatun Mukhtasar na Muzani, shi kuma ga shi ba zai iya karantawa ba, sai ya tambaye ni cewa yaushe ne mutum zai iya koyon irin wannan ilimin? Sai na ji kamar in ce masa idan mahaifiyarsa tana nan raye ya je ta yi masa addu’a, to amma sai na ji kunya na kasa fada masa.” 


Kyakkyawar addu’a ta iyaye tana da albarka matuka.


Wannan mashahurin malami Al-Imam Sulaimu ya fara neman ilimi ne bayan ya  haura shekara arbai’in a duniya. Amma ya zama daya daga cikin hamshakan malamai a zamaninsa.


*Rubutawa*: *Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo kano*


[Dubi, Az-Zahabi, Siyar Al-A’lam, Juzi’i na 3, Shafi na 18-19].

Continue reading...

ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI, AMMA INA TSORON CIN HARAM ?

*ZAN AURI MA'AIKACIN BANKI, AMMA INA TSORON CIN HARAM ?*

*Tambaya:*


Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani ma'aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu'amalarsa za mu ce Alhamdulillah, to shi ne take neman menene halarcin auransa a shari'a? Saboda tana tsoron kar ya rika ciyar da ita da dukiyar haramun.   


*Amsa*


Wa alaikum assalam To dan'uwa Annabi  s.a.w.  yana cewa : "Allah ya la'anci mai cin riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka" Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598. 

Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke mu'amala da riba, saboda ma'aikacin banki zai rubuta ko kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan aike . .

Duba fatawaa Allajanah adda'imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401.


Idan ya zama abin da ma'aikacin banki yake amsa haramun ne, kuma ba shi da wata sana'a sai wannan, akwai hadari a auransa, saboda zai ciyar da matarsa da haramun

 Malamai suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin halal da haram, idan ya maka kyauta za ka iya amsa,  saboda Annabi s.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa, kuma a dukiyarsu akwai halal da haram, amma in ba shi da wata sana'a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin dukiyarsa  ba.  

Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.  


*Allah ne mafi sani.*


*Amsawa*✍🏻


*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

10\4\2015

Continue reading...

SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO ?

*SHIN YA HALATTA ARNIYA TA YIWA MUSULMA KITSO ?*

*Tambaya*

Assalamu alaikum, shin ya halatta Arniyya ta yiwa musulma Kitso ?

*Amsa*

Wa'alaikumus salam

Ya halatta macen da ba musulma ba ta yiwa musulma kitso, saboda a zancen mafi inganci, al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace, shi ne daga guiwa zuwa cibiya, babu bambanci tsakanin kafira da musulma a cikin haka, domin a zamanin Annabi s.a.w. Yahudawa mata suna shiga gidan Annabi s.a.w., kuma ba'a samu suna yin shiga ta musamman ba idan suka ga za su shigo, saidai in kafirar tana da wani sharri da ake jin tsoro, to wannan mace za ta iya suturta daga ita, sannan kuma mutukar akwai musulma to ita ta fi dacewa ayi hulda da ita .

ALLAH NE MA FI SANI

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

Continue reading...

ASKEWA YARO GASHI RANAR BAKWAI GA HAIHUWA??

ASKEWA YARO GASHI RANAR BAKWAI GA HAIHUWA??

*Tamabaya*

Assalamu alaikum, inawa dr, fatan alheri tambaya ta itace: ina matsayin askin suna a Musulunci?

*Amsa*

Wa'alaikum assalam, Aski ranar bakwai ga wata sunna ne saboda fadin Annabi ﷺ (Dukkan abin haihuwa za'a hana shi ceton iyayensa har sai an masa Akika an sanya masa suna, an kuma yi masa aski ranar bakwai ga wata) kamar yadda Tirmizi ya rawaito daga hadisin Hasan daga Samurah sahabin Annabi ﷺ

Allah ne mafi sani.

13/02/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.


Continue reading...

MATA AYI HAKURI MAI HAKURI BAYA TABEWA

MATA AYI HAKURI MAI HAKURI BAYA TABEWA


*Idan aurenki yayi jinkiri ko kika rasa miji da*

*wuri:* tuna sayyida khadija (r.a),da tayi hakuri SAI Allah ya azurta ta da mafi alkairin mazaje a

gidan duniya kuma Annabin Allah (s.w.t.)..



*Idan Allah bai nufeki da yin aure ba gabaki*

*daya:* tuna da nana maryam (a.s) da yadda Allah ya mata albarka a gidan duniya da lahira, KUMA ya yabeta da kamewa a cikin littafinsa mai

tsarki,dukda cewa batayi aure ba...



*Idan Allah (s.w.t) bai azurtaki da haihuwa ba:* kiyi hakuri kada ki daga hankalinki ko ki damu da zancen mata: ki tuna matar Annabi Zakariyya (a.s) da tayi hakuri sai Allah ya dubi zuciyarta ya azurta ta da haihuwa dukda da cewa ta tsufa shekarunta sun tafi...



*Idan Allah ya jarrabeki da azzalumin* *miji mai sabawa Allah da bijerewa hanyarsa:* sai ki tuna Asiya matar fir'auna,da Allah ya dubi zuciyar ta sai ya sanyata ta zamto daka cikin shuwagabannin matan Aljannah..



*Idan Allah ya kaddara miki rabuwa da mijinki ko ya sake ki:* sai ki tuna fadin Allah (s.w.t).

"Idan suka rabu to Allah zai azurta kowa da

rabonsa.."



*Idan Allah yayiwa* *mai gidanki rasuwa kada kiyita sanya damuwa a zuciyarki har ki rinka furucin cewa bazaki taba samun wani wanda ya*



*fishi alkairi ba:* ki tuna ummu salma matar Abu-salma, (r.a),da mijinta yayi wafati sai Allah ya canja mata da wanda ya fishi shine Annabi Muhammad (s.a.w.),sabida kasancewarta daka cikin masu cewa:

*_Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un,a lokacin musiba..._*. 


Ki sanya a zuciyarki cewa arzikin Allah yana

zuwa..


Kada ki kwallafa ranki ko kisa ido ga arzikin da

Allah yayiwa wata ta kusa dake ko yar'uwarki..


Ki sani cewa Allah yana sane da halin da kike

ciki, domin shi ya halicceki,kuma ya fiki sanin kanki da damuwarki...



Kada ki damu da abunda mutane ke furtawa akanki,domin basuda abinda suka isa su miki idan ba wannan zancen ba,kuma shi baya cutarwa...


Allah ya shiryar da bisa tafarkin Shari'a....



*Pls u can share the message to circulate*

Continue reading...

ku iliman tar da "ya "yayenku ilimin tauhidi tun suna kana na


ﺱ :1 ﺃﻳﻦ ﺍﻟﻠﻪ؟.
1-tambaya:a ina allah yake?
ﺝ : ﻓﻲ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ‏( ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﺮﺵ ‏) .
*amsa;-yana sama(ya dai daita akan al´arshi).
ﺱ :2 ﻣﺎ ﺍﻟﺪﻟﻴﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮآﻥ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﺮﺵ؟
2-tambaya;-wane dalili ne a qur`ani cewa allah ya dai daita akan al`arshi?
ﺝ : " ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﺮﺵ ﺍﺳﺘﻮﻯ ".
amsa;-"allah mai rahama ya dai daita akan al`arshi".
ﺱ :4 ﻣﻦ ﺃﻳﻦ ﻧﺄﺧﺬ ﻋﻘﻴﺪﺗﻨﺎ؟.
4-tambaya;-a`ina zan karbi akidata ?
ﺝ : ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮآﻥ ﻭ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭ ﺍﻷﺛﺮ .
*amsa;-daga alqur`ani da sunnar manzo(s.a.w) da magan ganun sa habbai.
ﺱ :5 ﻟﻤﺎﺫﺍ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺠﻦ ﻭ ﺍﻹﻧﺲ؟
5-tambaya;-sabo dame allah ya hallicci
mutum da aljan?
ﺝ : ﻟﻌﺒﺎﺩﺗﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ .
*amsa;-sabo da su bauta masa shi kadai kada suyi shirka dashi.
ﺱ :6 ﻣﺎ ﺍﻟﺪﻟﻴﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮآﻥ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﺠﻦ ﻭ ﺍﻹﻧﺲ ﻟﻌﺒﺎﺩﺗﻪ؟.
6-tambaya;-mecece hujjah a qur`ani cewa allah ya hallici mutum da aljan don su bauta mishi? .
ﺝ : " ﻭ ﻣﺎ ﺧﻠﻘﺖ ﺍﻟﺠﻦ ﻭ ﺍﻹﻧﺲ ﺇﻻ ﻟﻴﻌﺒﺪﻭﻥ ".[الذیات :ه٦].
*amsa;-allah yana cewa acikin alqur`ani "ban halicci mutum da aljanba sai dan su bautamin .
ﺱ :7 ﻣﺎ ﻣﻌﻨﻰ " ﻳﻌﺒﺪﻭﻥ " ؟.
7-tambaya;-mecece ma`anar "su bautamin"?.
ﺝ : ﻳﻮﺣﺪﻭﻥ ﻭ ﻳﻄﻴﻌﻮﻥ .
*amsa;-ma`anarsa shine "su kadaitani wajen bauta, kuma suyimin biyya"
ﺱ :8 ﻣﺎ ﻣﻌﻨﻰ " ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ " ؟.
8-tambaya:-mecece ma`anar (لا (اله الا الله
ﺝ : ﻻ ﻣﻌﺒﻮﺩ ﺑﺤﻖ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ .
*amsa;-ma`anarta shine "kayi imani babu abin bautawa bisa cancanta da gaskiya sai allah.
ﺱ :9 ﻣﺎ ﻫﻲ ﺃﻋﻈﻢ ﻋﺒﺎﺩﺓ؟.
9-tambaya:-macece mafi girman ibada?. ﺝ : ﺍﻟﺘﻮﺣﻴﺪ
. *amsa:-kadaita allah wajen bauta.
ﺱ :10 ﻣﺎ ﻫﻮ ﺃﻋﻈﻢ ﻇﻠﻢ؟.
10-tambaya:-menene mafi girman zalunci? .
ﺝ : ﺍﻟﺸﺮﻙ .
*amsa:-hada allah da wani wajen bauta(ashshirku billah).
ﺱ :11 ﻣﺎ ﻫﻮ ﺍﻟﺘﻮﺣﻴﺪ؟.
11-tambaya;-menene tauhidi?.
ﺝ : ﺇﻓﺮﺍﺩ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﺎﻟﻌﺒﺎﺩﺓ .
*amsa;-shine kadaita allah wajen bauta
ﺱ :12 ﻣﺎ ﻫﻮ ﺍﻟﺸﺮﻙ؟.
12-tambaya:-menene shirka?.
ﺝ : ﻋﺒﺎﺩﺓ ﻏﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻊ ﺍﻟﻠﻪ .
*amsa;-shine bautawa wani allah tare da allah.
ﺱ :13 ﻛﻢ ﺃﻗﺴﺎﻡ ﺍﻟﺘﻮﺣﻴﺪ؟.
13-tambaya;-nawa ne kashe kashen tauhidi?.
ﺝ : ﺛﻼﺛﺔ .
. amsa;- uku ne (3).
ﺱ :14 ﻣﺎ ﻫﻲ ﺃﻗﺴﺎﻡ ﺍﻟﺘﻮﺣﻴﺪ؟.
14-tambaya-menene kashe kashe tauhidi? .
ﺝ : ﺍﻟﺮﺑﻮﺑﻴﺔ، ﻭ ﺍﻷﻟﻮﻫﻴﺔ، ﻭ ﺍﻷﺳﻤﺎﺀ ﻭ ﺍﻟﺼﻔﺎﺕ .

amsa;-sune 1-tauhidu rrububiyya, 2-tauhidul uluhiyya 3-tauhidul asma`i wassifat.
ﺱ :15 ﻣﺎ ﻫﻮ ﺗﻌﺮﻳﻒ " ﺗﻮﺣﻴﺪ ﺍﻟﺮﺑﻮﺑﻴﺔ " ؟.
15-tambaya;-mene ne ma`anar "tauhidur rububiyya"?.
ﺝ : ﺇﻓﺮﺍﺩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺃﻓﻌﺎﻟﻪ، ﻣﺜﻞ ﺍﻟﺨﻠﻖ ﻭ ﺍﻟﺮﺯﻕ ﻭ ﺍﻟﺘﺪﺑﻴﺮ ..
amsa;-shine kadaita allah acikin ayyukansa, misali: *halitta, *da azurtawa, *da jujjuya al`amra,(duk mutum yayi imani ba mai yin wa`anan sai allah)
. ﺱ :16 ﻣﺎ ﻫﻮ ﺗﻌﺮﻳﻒ " ﺗﻮﺣﻴﺪ ﺍﻷﻟﻮﻫﻴﺔ " ؟.

16-tambaya;-mene ne ma`anar"tauhidul uluhiyya"? .
ﺝ : ﺇﻓﺮﺍﺩ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﺄﻓﻌﺎﻝ ﺍﻟﻌﺒﺎﺩ، ﻣﺜﻞ ﺍﻟﺪﻋﺎﺀ ﻭ ﺍﻟﺬﺑﺢ ﻭ ﺍﻟﺴﺠﻮﺩ.
. amsa;-shine kadaita allah awajen ayyukan ibada, misali:-
*addu`a, *da wajen yanka, *da sujjada.
ﺱ :17 ﻫﻞ ﻟﻠﻪ ﺃﺳﻤﺎﺀ ﻭ ﺻﻔٰاة؟.
17-tambaya;-shin allah yana da sunaye da siffofi? .
ﺝ : ﻧﻌﻢ، ﻟﻪ ﻣﺎ ﻭصف ﺑﻪ ﻧﻔﺴﻪ ﻭ ﻭﺻﻔﻪ ﺑﻪ ﺍﻟﻨﺒﻲ

ﷺ . amsa;-hakan ne allah yana da sunaye
da siffofi,wanda ya siffanta kansa da su ko wanda annabin sa ya siffanta.ٓ
ﺱ :18 ﻣﻦ ﺃﻳﻦ ﻧﺄﺧﺬ ﺃﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﻭ ﺻﻔﺎﺗﻪ؟-
18-tambaya;-daga ina zamu karbi sunayen allah da siffofinsa?.
ﺝ : ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮآﻥ ﻭ ﺍﻟﺴﻨﺔ .
amsa;-daga alqur`ani da sunnah
ﺱ :19 ﻫﻞ ﺻﻔﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﺗﻤﺎﺛﻞ ﺻﻔﺎﺕ ﺍﻟﻤﺨﻠﻮﻗﻴﻦ؟ .
19-tambaya;-shin siffofin allah ta`ala da sunayen sa suna kama da na abin halitta? .
ﺝ : ﺻﻔﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻻ ﺗﻤﺎﺛﻞ ﺻﻔﺎﺕ ﺍﻟﻤﺨﻠﻮﻗﻴﻦ.
amasa;-siffar allah ta`alah bata kama da siffar bayi.
ﺱ :20 ﻣﺎ ﺍﻟﺪﻟﻴﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮآﻥ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺻﻔﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻻ ﺗﻤﺎﺛﻞ ﺻﻔﺎﺕ ﺍﻟﻤﺨﻠﻮﻗﻴﻦ؟.
20-tambaya;-menene dalili akur`ani akan cewa siffar allah ta`ala bata kama da siffofin bayi? .
ﺝ : " ﻟﻴﺲ ﻛﻤﺜﻠﻪ ﺷﻲﺀ ﻭ ﻫﻮ ﺍﻟﺴﻤﻴﻊ ﺍﻟﺒﺼﻴﺮ ".[الشوری:١١].
amsa;-dalilin shine wanna ayar "ba abin dake kama da shi,shi(allah)mai jine kuma mai gani".
[الشوری:١١]
[ ﺱ :21 ﻣﺎ ﻫﻮ ﺍﻟﻘﺮآﻥ؟.
21-tambaya;-menene alqur`ani
ﺝ : ﺍﻟﻘﺮآﻥ ﻛﻼﻡ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ.
. amsa;-alqur`ani maganar allah ta`ala ne.
ﺱ :22 ﻫﻞ ﺍﻟﻘﺮآﻥ ﻣﻨﺰﻝ ﺃﻡ ﻣﺨﻠﻮﻕ؟.
22-tambaya;-shin qur`ani saukakkene ko halittar allah ne? .
ﺝ : ﻣﻨﺰﻝ ﻭ ﻫﻮ ﻛﻼﻡ ﺍﻟﻠﻪ ﺣﻘﻴﻘﺔ ‏( ﺑﺤﺮﻑ ﻭ ﺻﻮﺕ ‏) .
. amsa;-saukakkene sannan maganar allah ne hakika(da harafi da magana)
ﺱ :23 ﻣﺎ ﻫﻮ ﺍﻟﺒﻌﺚ؟.
23-tambaya;-menene (البعث).
ﺝ : ﺇﺣﻴﺎﺀ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻌﺪ ﻣﻮﺗﻬﻢ.
. amsa;-shine rayar da mutane bayan sun mutu.
ﺱ :24 ﻣﺎ ﺍﻟﺪﻟﻴﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮآﻥ ﻋﻠﻰ ﻛﻔﺮ ﻣﻦ ﺃﻧﻜﺮ ﺍﻟﺒﻌﺚ؟.
24-tambaya;-menene dalili a aur`ani akan kafurtar wada yayi inkarin alqiyama?.
ﺝ : " ﺯﻋﻢ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻛﻔﺮﻭﺍ ﺃﻥ ﻟﻦ ﻳﺒﻌﺜﻮﺍ ". [التغانن:٧].
amsa-"wa anda suka kafirta suna riya cewa ba za a tayar da su ba." .
ﺱ :25 ﻣﺎ ﺍﻟﺪﻟﻴﻞ ﻣﻦ ﺍﻟﻘﺮآﻥ ﻋﻠﻰ ﺃﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺳﻴﺒﻌﺜﻨﺎ؟.
25-tambaya;-menene dalili a qur`ani cewa allah zai tashemu bayan mummutu?.
ﺝ : " ﻗﻞ ﺑﻠﻰ ﻭﺭﺑﻲ ﻟﺘﺒﻌﺜﻦ .
". amsa;-shine"ka ce dasu ni ina rantse da ubangijina lalle za a tayar da su"
ﺱ :26 ﻣﺎ ﻣﻌﻨﻰ ﻛﻠﻤﺔ " ﺍﻹﺳﻼﻡ " ؟.
26-tambaya;-menene ma`anar kalmar"الإسلام.
"? ﺝ : ﺍﻻﺳﺘﺴﻼﻡ ﻟﻠﻪ ﺑﺘﻮﺣﻴﺪﻩ ﻭ ﺍﻻﻧﻘﻴﺎﺩ ﻟﻪ ﻭ ﺍﻟﺒﺮﺍﺀﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﺮﻙ ﻭ ﺃﻫﻠﻪ.
. amsa;-shine mika wuya ga allah da tauhidi, da barranta da shirka da ahlinta(shirka).
ﺱ :27 ﻣﺎ ﻣﻌﻨﻰ ﻛﻠﻤﺔ " ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ " ؟
27-tambaya;-mecece ma`anar kalmar "الیمان"?.
ﺝ : ﺃﻥ ﺗﺆﻣﻦ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻭ ﻣﻼﺋﻜﺘﻪ ﻭ ﻛﺘﺒﻪ ﻭ ﺭﺳﻠﻪ ﻭ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻵﺧﺮ ﻭ ﺃﻥ ﺗﺆﻣﻦ ﺑﺎﻟﻘﺪﺭ ﺧﻴﺮﻩ ﻭ ﺷﺮﻩ .
amsa;-*shine kayiimani *da allah *da mala`ikunsa * da littattafansa *da manzanninsa *da ranar lahira *da kaddara ta alkairi ko ta akasinta.
ﺱ :28 ﻫﻞ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﻳﺜﺒﺖ ﺑﺎﻟﻘﻠﺐ ﺃﻡ ﺑﺎﻟﻠﺴﺎﻥ ﺃﻡ ﺑﺎﻟﺒﺪﻥ؟.
28-tambaya;-shin imaٓni yana tabbata a zuciya ko da harshe ko da gangar jiki?.
ﺝ : ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﻳﺜﺒﺖ ﺑﺎﻋﺘﻘﺎﺩ ﺍﻟﻘﻠﺐ ﻭ ﻗﻮﻝ ﺍﻟﻠﺴﺎﻥ ﻭ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﺒﺪﻥ ‏( ﻣﻌﺎ ‏) ، ﻭ ﻫﻮ ﻳﺰﻳﺪ ﺑﺎﻟﻄﺎﻋﺔ، ﻭ ﻳﻨﻘﺺ ﺑﺎﻟﻤﻌﺼﻴﺔ . (احذر من قول ان الإيمان في القلب فقط!!).
amsa;-imani yana tabbata da kudurcewa azuciya, da kuma fadi da harshe, da kuma aiki da jiki. tare da cewa shi imani yana karuwa da yiwa allah dٓa`a kuma yana raguwa da saba masa(ka tse hanzari masu cewa,shi imani a zuciya kada yake!!) .
ﺱ :29 ﻟﻤﻦ ﻧﺘﻀﺮﻉ ﻭ ﻧﺴﺠﺪ ﻭ ﻧﺬﺑﺢ؟.
29-tambaya;-dawa muke dogara kuma wa muke wa sujjada kuma dan wa muke yin yanka?.
ﺝ : ﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ .
. amsa;-ga allah shi kadai bashi da abokin taraiyya.
ﺱ :30 ﻫﻞ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻟﺘﻀﺮﻉ ﺃﻭ ﺍﻟﺴﺠﻮﺩ ﺃﻭ ﺍﻟﺬﺑﺢ ﻟﻐﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ؟.
30-tambaya;-shin yana halatta mu dogara dawani ko muyiwa wani sujjada ga wani ko muyi yanka don wani wanda ba allah ba? .
ﺝ : ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺫﻟﻚ، ﻷﻥ ﻓﻌﻞ ﺫﻟﻚ ﻟﻐﻴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﺷﺮﻙ .

amsa;-baya halatta muyiwa wani wanda ba allah ba,domin aikata daya daga cikin wa`annan abubuwan ga wani wanda ba allah ba shirkace babba, allah yakaremu ameeeen.
ﻭ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭ ﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﻣﺤﻤﺪ ﻭ ﻋﻠﻰ آﻟﻪ ﻭ ﺻﺤﺒﻪ ﻭ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻴﻦ، ﻭ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ

Continue reading...

YIN KARYA DA SHARRI WA MUTANE DA BATA SU A TSAKANIN MUTANE YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN SHAQIYANCI (RASHIN RABO A LAHIRA)

YIN KARYA DA SHARRI WA MUTANE DA BATA SU A TSAKANIN MUTANE YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN SHAQIYANCI (RASHIN RABO A LAHIRA)

Al- Imamu Ahmad a cikin Musnad, da Ibnu Hibban, da Abu Abdillahil Hakim Al - Naisaburiy a cikin Mustadrak, da Bukhari a cikin Adabul Mufrad, sun ruwaito da isnadi mai kyau:

ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ، ﻗﺎﻝ : ﻗﺎﻝ ﺭﺟﻞ : ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ، ﺇﻥ ﻓﻼﻧﺔ ﻳﺬﻛﺮ ﻣﻦ ﻛﺜﺮﺓ ﺻﻼﺗﻬﺎ، ﻭﺻﻴﺎﻣﻬﺎ، ﻭﺻﺪﻗﺘﻬﺎ، ﻏﻴﺮ ﺃﻧﻬﺎ ﺗﺆﺫﻱ ﺟﻴﺮﺍﻧﻬﺎ ﺑﻠﺴﺎﻧﻬﺎ، ﻗﺎﻝ : " ﻫﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ "

"Daga Abu Hurairah (ra) ya ce: Wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah (saw), wacce ana ambaton yawan sallanta, da yawan azuminta, da yawan sadakanta, sai dai tana cutar da mokotanta da harshenta (kamar zagi, cin namansu da gulmansu, yi musu karya, yi musu batanci a cikin mutane da aibantasu d.s). Sai Annabi (saw) ya ce: "Ita 'yar wuta ce".

Al- Imamuz Zahabiy (r) yana tarjamar Imamu Ahlis Sunnati wal Jama'a, Ahmad bn Hanbal (r) ya ce:

ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﺍﻟﻮﺭﺍﻕ : ﻛﻨﺖ ﻓﻲ ﻣﺠﻠﺲ ﺃﺣﻤﺪ ﺑﻦ ﺣﻨﺒﻞ، ﻓﻘﺎﻝ : ﻣﻦ ﺃﻳﻦ ﺃﻗﺒﻠﺘﻢ؟ ﻗﻠﻨﺎ : ﻣﻦ ﻣﺠﻠﺲ ﺃﺑﻲ ﻛﺮﻳﺐ . ﻓﻘﺎﻝ : ﺍﻛﺘﺒﻮﺍ ﻋﻨﻪ، ﻓﺈﻧﻪ ﺷﻴﺦ ﺻﺎﻟﺢ .

ﻓﻘﻠﻨﺎ : ﺇﻧﻪ ﻳﻄﻌﻦ ﻋﻠﻴﻚ . ﻓﻘﺎﻝ : ﻓﺄﻱ ﺷﻲﺀ ﺣﻴﻠﺘﻲ، ﺷﻴﺦ ﺻﺎﻟﺢ ﻗﺪ ﺑﻠﻲ ﺑﻲ .

"Daga Abdullahi bn Muhammad Al- Warraq ya ce: Na kasance a majlisin Ahmad bn Hanbal sai ya ce: "Daga ina kuka tafo?", sai muka ce: Daga majalisin Abu Kuraib. Sai ya ce: "Ku rubuta hadisi daga gare shi, saboda malami ne mutumin kirki". Sai muka ce: Ai kuwa yana sukanka (aibantawa). Sai ya ce: "To meye dabarata? (yaya zan yi?), mutumin kirki ne amma kuma an jarrabe shi da ni". (ma'ana, duk da cewa; mutumin kirki ne a kan kansa, amma kuma Allah ya jarrabe shi da batanci wa mutane).

Duba Siyar 11/ 317.

Abin lura:

1. Wajibi ne ka kiyaye hakkin mutane kamar yadda yake wajibi ne ka kiyaye hakkin Allah.

2. Shiga hakkin mutane ta hanyar cutar da su da baki; zagi, aibantawa, suka, yi musu karya da sharri, da yi musu batanci a wajen mutane, wadannan suna halaka mutum su shigar da shi wuta ko da mai ibada ne.

3. Mun ji labari mutanen kirki masu kiyaye hakkokin Allah da suka halaka a dalilin cutar da mutane da bakinsu, ina kuma in da ma mutumin banza ne ko jahili da ba ya kiyaye hakkokin Allah?

4. Hausawa suka ce: BAKI SHI KE YANKA WUYA...

Allah ya tsaremu.

Continue reading...

Hali ne na 'Yan Bidi'a ka kirkiri abin da babu shi a cikin Alkur'ani, babu shi cikin Hadisan Annabi (saw)

Hali ne na 'Yan Bidi'a ka kirkiri abin da babu shi a cikin Alkur'ani, babu shi cikin Hadisan Annabi (saw) amma kuma ka zo ka kakaba shi wa mutane, wanda ya bi shi ne Ahlus Sunna Salafiy, wanda kuma ya saba ya zama Hizbiy Dan Bidi'a.

Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya ya ce:

ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﺷﻌﺎﺭ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺇﺣﺪﺍﺙ ﻗﻮﻝ ﺃﻭ ﻓﻌﻞ، ﻭﺇﻟﺰﺍﻡ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻪ ﻭﺇﻛﺮﺍﻫﻬﻢ ﻋﻠﻴﻪ ﺃﻭ ﺍﻟﻤﻮﺍﻻﺓ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺍﻟﻤﻌﺎﺩﺍﺓ ﻋﻠﻰ ﺗﺮﻛﻪ، ﻛﻤﺎ ﺍﺑﺘﺪﻋﺖ ﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺝ ﺭﺃﻳﻬﺎ ﻭﺃﻟﺰﻣﺖ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻪ، ﻭﻭﺍﻟﺖ ﻭﻋﺎﺩﺕ ﻋﻠﻴﻪ ...

ﻭﺍﺑﺘﺪﻋﺖ ﺍﻟﺠﻬﻤﻴﺔ ﺭﺃﻳﻬﺎ ﻭﺃﻟﺰﻣﺖ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻪ ﻭﻭﺍﻟﺖ ﻭﻋﺎﺩﺕ ﻋﻠﻴﻪ، ﻟﻤﺎ ﻛﺎﻧﺖ ﻟﻬﻢ ﻗﻮﺓ ﻓﻲ ﺩﻭﻟﺔ ﺍﻟﺨﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺜﻼﺛﺔ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺍﻣﺘﺤﻦ ﻓﻲ ﺯﻣﺎﻧﻬﻢ ﺍﻷﺋﻤﺔ ﻟﻴﻮﺍﻓﻘﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺭﺃﻱ ﺟﻬﻢ ﺍﻟﺬﻱ ﻣﺒﺪﺅﻩ ﺃﻥ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﻣﺨﻠﻮﻕ، ﻭﻋﺎﻗﺒﻮﺍ ﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﻮﺍﻓﻘﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ .

ﺍﻟﺘﺴﻌﻴﻨﻴﺔ ‏( /1 176 - 177 )

"Ya kasance yana daga cikin tambarin 'Yan Bidi'a akwai kirkiran magana ko aiki da lazimta wa mutane da tilasta musu binsa, da kulla soyayya a kansa, da kulla kiyayya ga wanda ya ki bi, kamar yadda Khawarijawa suka kirkiri ra'ayinsu, kuma suka lazimta shi ga mutane, suka kulla soyayya da kiyayya a kansa. Haka Rafidha...

Haka Jahamiyya ma, suka kirkiri ra'ayinsu, kuma suka lazimta shi ga mutane, suka kulla soyayya da kiyayya a kansa, musamman lokacin da suke da karfi a Daular Khalifofi guda uku, wadanda suka yi Jarabawa (Imihani) wa Manyan Malaman Sunna a zamaninsu, don su bi ra'ayin Jaham, wanda ya kirkira na cewa; Alkur'ani Halittacce ne, suka yi ta yin ukuba ga wanda bai bi su a kan haka ba".

Sabanin halin Malaman Sunna, su ba sa yin Ijtihadi su fitar da abu amma kuma su lazimta shi ga mutane.

Ya ce:

ﻛﺎﻥ ﺃﺋﻤﺔ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ ﻻ ﻳﻠﺰﻣﻮﻥ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻤﺎ ﻳﻘﻮﻟﻮﻧﻪ ﻣﻦ ﻣﻮﺍﺭﺩ ﺍﻻﺟﺘﻬﺎﺩ ﻭﻻ ﻳﻜﺮﻫﻮﻥ ﺃﺣﺪﺍ ﻋﻠﻴﻪ، ﻭﻟﻬﺬﺍ ﻟﻤﺎ ﺍﺳﺘﺸﺎﺭ ﻫﺎﺭﻭﻥ ﺍﻟﺮﺷﻴﺪ ﻣﺎﻟﻚ ﺑﻦ ﺃﻧﺲ ﻓﻲ ﺣﻤﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻋﻠﻰ ﻣﻮﻃﺌﻪ، ﻗﺎﻝ ﻟﻪ : ﻻ ﺗﻔﻌﻞ ﻳﺎ ﺃﻣﻴﺮ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ...

ﺍﻟﺘﺴﻌﻴﻨﻴﺔ ‏( /1 177 - 178 )

"Manyan Malaman Sunna da Jama'a sun kasance ba sa lazimta wa mutane ra'ayoyinsu da yake cikin mas'alolin Ijtihadi, ba sa tilasta ma wani bin ra'ayin nasu. Saboda haka ne lokacin da Khalifa Harunar Rasheed ya shawarci Imamu Malik bn Anas a kan dora mutane bisa "Mawadda" sai ya ce masa: Kar ka yi haka ya Amirul Muminina...".

Imamu Malik ya ki yarda a lazimta wa mutane aiki da Littafinsa "Mawadda", ina kuma ga mai da'awar bin Malik, mai neman lazimta wa mutanen Nigeria bin Risala da Mazhabar Malikiyya?!

Saboda haka, babu wanda ya isa ya lazimta wa mutane bin wani abun da babu shi a cikin Alkur'ani ko Hadisi ko Ijma'i. Sawa'un mas'ala ce ta Fiqhu ko wani abu ne na Manhaji, ko da an kira shi ne da sunan Manhajin Salafiyya.

Continue reading...

BAYANIN JAHILCIN MASU SUKAN MALAMAN SUNNA DA CEWA; SU KHAWARIJAWA NE QA'ADIYYA

BAYANIN JAHILCIN MASU SUKAN MALAMAN SUNNA DA CEWA; SU KHAWARIJAWA NE QA'ADIYYA

'Yan Kungiyar Salafiyyun Masu guluwwi a Bidi'antarwa suna sukan Malaman Sunna suna Bidi'anar da su bisa shubuhar -wai- su Khawarijawa ne Qa'adiyya, wato Khawarijawa na zaune.

To abin da wadannan suke fada suke rubutawa kuma suke yadawa jahilci ne da shubuhohi ba ilimi da hujjoji ba. Saboda asali su ba su san menene hakikanin Khawarijanci ba!

A baya na taba yin posting na yi tambaya don a tattauna a kan mas'alar a Facebook, amma saboda su ba sa iya tattauna mas'aloli a ilmance, saboda rashin abin tattaunawar da rashin fahimtar maganganun Malamai, da rashin sanin Usul na mas'alolin Addini, da kuma abin da suke da shi na zafin kai da ruduwa shi ya sa ba a cimma buri ba.

Abun da suke zargin Malaman Sunna da shi shi ne inkarin munanan aiyuka ga shugabanni a bainar jama'a. To lallai wannan kuskure ne, saboda an samu Hadisi da Annabi (saw) yake umurni da yin Nasiha wa shugaba a sirrance. Saboda in ana yi musu Nasiha a bainar jama'a, to jama'a za su rena su, in kuma suka rena su to jama'a za su iya yi musu tawaye su ki bin dokokinsu, to sai a samu matsala da rashin zaman lafiya. Wannan kuwa zai sa a rasa Maslahar shugabanci, na haduwar al'umma karkashin shugabancin jagora guda daya, wanda zai daidaita lamura a samu zaman lafiya, don a zauna lafiya a samu damar bautar Allah Madaukaki.

To amma shin wannan shi ne Khawarijanci?!

A'a, ba shi ne hakikanin Khawarijanci ba, saboda Khawarijanci shi ne fita daga al'umma gaba daya da halasta jininta, da kuma daukan makami a kanta da kashe mutane.

Duk wanda ba shi da wannar Aqida to shi ba Bakhawarije ba ne.

Annabi (saw) ne da kansa ya yi bayanin Khawarijanci inda ya ce:

" ﻭﻣﻦ ﺧﺮﺝ ﻋﻠﻰ ﺃﻣﺘﻲ، ﻳﻀﺮﺏ ﺑﺮﻫﺎ ﻭﻓﺎﺟﺮﻫﺎ "

"Duk wanda ya fita daga al'ummata, ya dauki makami a kanta yana kashe mutanen kirki da mutanen banza...".

Kuma ya ce:

" ﻳﻘﺘﻠﻮﻥ ﺃﻫﻞ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﻳﺪﻋﻮﻥ ﺃﻫﻞ ﺍﻷﻭﺛﺎﻥ ".

"Suna kashe Musulmai suna barin kafirai".

Shaikhul Islam ya ce:

" ﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺝ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻓﺎﺭﻗﻮﺍ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻭﺍﺳﺘﺤﻠﻮﺍ ﺩﻣﺎﺀ ﻣﻦ ﺧﺎﻟﻔﻬﻢ ."

ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /3 420 )

"Khawarijawa wadanda suke rabuwa da Jama'ar Musulmai, kuma suka halasta jinanen wadanda suka saba musu".

A wani wajen ya ce:

" ﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺝ ﺩﻳﻨﻬﻢ ﺍﻟﻤﻌﻈﻢ ﻣﻔﺎﺭﻗﺔ ﺟﻤﺎﻋﺔ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻭﺍﺳﺘﺤﻼﻝ ﺩﻣﺎﺋﻬﻢ ﻭﺃﻣﻮﺍﻟﻬﻢ ."

ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /13 209 )

"Khawarijawa tushen Addininsu mafi girma shi ne rabuwa da Jama'ar Musulmai, da halasta jinanensu da dukiyoyinsu".

Saboda haka yaushe mutum zai yi zaton irin wannar Aqida ta halasta jinanen Musulmai gaba daya ga Malaman Sunna in ban da jahili dan zafin kai ba?!

To kasancewar su Khawarijawa masu irin wannar Aqida ta FITA DAGA AL'UMMA DA DAUKAR MAKAMI A KANTA DA HALASTA JININTA DA KASHE MUTANE BA JI BA GANI, SU KASHE MUTUMIN KIRKI SU KASHE MUTUMIN BANZA BABU BANBANCEWA, suna da Aqidar cewa; su ne kawai Musulmai, don haka garuruwa ko dazukan da suke zaune a cikinsu su ne KASAR MUSLUNCI (ﺩﺍﺭ ﺍﻹﺳﻼﻡ ), don haka garuruwan sauran Musulmai kuma garuruwan kafirai ne, sai suke kiransu da suna KASAR KAFIRCI ( ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻜﻔﺮ ), wannan ya sa suke wajabta wa mabiyansu hijira zuwa gare su, kuma suke haramta zama a cikin sauran al'umma da suka kafirta suka halasta jinanensu, to wannan ya sa mabiyansu suke yin hijira su bar cikin sauran al'umma su koma cikin 'yan uwansu Khawarijawa a garuruwa ko dazukan da suke zaune su kadai, - kamar dai yadda Boko Haram suka yi -. To duk wanda bai yi hijira ya koma cikinsu daga cikin masu irin Aqidarsu ba, wato wadanda suka ki yin hijira daga cikin mabiyansu, sukan zauna cikin mutane sauran al'umma suna da'awa da yada ra'ayoyinsu na Khawarijanci da Kafirta Musulmai gaba daya, to wadannan su ake kira KHAWARIJAWA QA'ADIYYA, ma'ana; wadanda suka zauna cikin al'umma ba su yi hijira sun koma cikin 'yan uwansu Khawarijawa a can inda suke zaune ba.

To Khawarijawa masu irin waccar Aqida da muka ambata ta halasta jinanen al'umma gaba daya, da daukan makami a kanta suna kashe kowa da kowa, amma kuma su ba su yi Hijira sun koma garuruwan 'yan uwansu Khawarijawa ko inda suke zaune a dazuka ba, su ake kira KHAWARIJAWA QA'ADIYYA.

To in ban da guluwwi da zafin kai na Kungiyar Salafiyyun ba, yaushe Malaman Sunnan da suke Bidi'antarwa suka kulla Aqida irin ta su Shekau a cikin zukatansu, amma ba su tattare sun koma Sambisa ba, kawai sun zauna ne a cikin al'umma suna kiran mutane ga Aqidar Boko Haram, balle har a kira su da Khawarijawa Qa'adiyya?!

Wannan wane irin jahilci da zalunci ne haka?!

Sa'annan in ban da jahilci ba, wa ya gaya musu Tawaye wa shugaba shi ne Khawarijanci?

Tawaye wa shugaba yana cikin Aqidun Khawarijawa amma ba shi ne hakikanin Khawarijanci ba. Na yi maka bayanin hakikanin Khawarijanci a sama.

Tawaye wa shugaba ba Khawarijanci ba ne kai tsaye, shi ya sa ake samun wadanda Malamai suke kira da BUGAAT, wato 'yan tawaye da suke da Tawili a kan Tawayensu wa shugaba.

Irinsu ne wadanda suka yaki Sayyidina Aliyu (ra) cikin Sahabbai, irin su A'isha (ra), Dalhat (ra), Zubair (ra), Mu'awiya (ra) da sauran Sahabban da suke tare da su. Da Hussain (ra) wanda ya yi tawaye wa Yazidu. Duka wadannan babu wanda ya taba kiransu da Khawarijawa, babu wanda ya taba kiransu da Fasikai. Duk da sun yaki Shugaba sun yi masa Tawaye amma su Adilai ne mutanen kirki masu falala.

Kuma hatta Khawarijawa da Aliyu (ra) ya yaka, Sayyidina Aliyu (ra) bai fara yakarsu ya kira su Khawarijawa ba, - duk da ya san sun yi masa Tawaye a matsayinsa na shugaba -, har sai da suka halasta jinanen Musulmai suka kashe Abdullahi bn Khabbab (ra), suka farka cikin matarsa, suka kora dukiyoyin Musulmai.

Da farko sun yi masa Tawaye, amma bai kira su da Khawarijawa da Annabi (saw) ya ba da labarinsu ba har sai da suka halasta jinanen Musulmai gaba daya, suka fita daga cikin al'umma, suka fita daga cikin Musulmai, suka koma wani kauye mai suna Haraura'u, saboda suna ganin ba za su zauna cikin Kafirai ba.

Wadannan fa su ne Khawarijawa!

To yaushe Malaman Sunna suka taba kira ga wannan, da har za a kira su da Khawarijawa Qa'adiyyah, in ban da jahilci ba?!

Wannan ya sa Ibnu Qudama a cikin "Al-Mugniy" ya yi bayanin kasuwan masu Khuruji da tawaye ga Shugaba, ya kasa su kashi Biyar. Na farkonsu Khawarijawa, sai kuma Bugaatu 'Yan tawaye masu Tawili...

Don me ya sa ya banbanta tsakaninsu, inda dukkansu Khawarijawa ne?!

Saboda haka, duk abin da wadannan matasan suke yadawa ba komai ba ne face rudu da jahilci saboda zafin kai da kungiyanci.

Ai yanzu a Nigeria lokaci ya wuce wani ya zo ya jefi wani Malami da Khawarijanci a kasa gane shirmensa, saboda kowa ya ga Khawarijawa a zahiri, wato 'Yan Boko Haram.

Yanzu don Allah wane mai ilimi da adalci ne zai zargi wani daga cikin Malaman Sunna da Khawarijanci a gabanmu, alhali mun ga yadda ake Khawarijanci a wajen 'Yan Boko Haram, wadanda suka halasta jinin kowa in ban da su kadai kawai?!

Abin mamaki, da wannan ne jahilan 'Yan Kungiyar Salafiyyun suke Bidi'antar da Shaikh Ja'afar da Shaikh Albaniy da sauran Malaman Sunna.

Allah ya shiryar da mu gaba daya.

Continue reading...
 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *