Da yawa daga cikin wadanda suka zaba wa kansu
sabanin shiriyar Manzon Allah cikin gudanar da
addininsu suna ganin cewa: In har Idin Maulidi
bidi’ah ne, to kuwa lalle Musabaka a kan haddar
Alqur’ani Mai girma, ko haddar Hadithan Annabi
masu daraja ko haddar wani ilmi na Musulunci su
ma yin su bidi’ah ce!!!
*************************
A nan muna ganin cewa yawan nisantar wadannan
mutane ga littattafan Shari’ah na maluman
Musulunci ne ya sa ba su ma san cewa: Dukkan
abin da halaccinsa ya tabbata ta yanyar Ijma’in
Musulmi cikin wani zamani daga cikin zamuna, to
dole ne ya zamanto daya daga cikin abubuwa uku:-
1- ko dai ya zamanto Mubaahi, watau abin da yin
sa da rashin yin sa duk daya a idanun Shari’ah.
2- ko kuwa ya zamanto Mustahabbi, watau abin da
in har ba a yi shi ba to ba a yi wani laifi ba, in
kuma aka yi shi to ana da wani lada na
musamman.
3- ko kuwa ya zamanto Waajibi, watau abin da in
har ba a yi shi ba za a sami zunubi, in kuma an yi
shi to an yi abin da Shari’ah ta tilasta yin shi.
******************************
shi kuwa Musabaka domin haddar Alqur’ani Mai
girma abu ne da Maluman Sunnah, da su kansu
masu bidi’ah na Duniya suka hadu a kan halaccinsa
a bisa hujjar kiyasin shi a kan Musaabakokin da
Nassi ya zo da halaccinsu. In kuwa haka lamarin
yake, to ta kaka ne za a hada hukuncin Musaabaka
domin haddar Alqur’ani da hukuncin Idin Maulidin
da babu mai yin shi ko halatta shi in banda wasu
daga cikin masu yin bidi’ah??
*********************
HUKUNCIN MUSABAKA:
1. Imam Ibnu Qudaamah mai rasuwa a shekara ta
620 watau da mutuwarsa yau shekaru 815 ke nan,
ya ce cikin littafinsa mai suna Almugnii
13/404-405 :-
{ ﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﺟﺎﺋﺰﺓ ﺑﺎﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻻﺟﻤﺎﻉ، ﺍﻣﺎ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺮﻭﻯ ﺍﺑﻦ ﻋﻤﺮ ﺍﻥ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺳﺎﺑﻖ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﺨﻴﻞ ﺍﻟﻤﻀﻤﺮﺓ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻔﻴﺎﺀ
ﺍﻟﻰ ﺛﻨﻴﺔ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ، ﻭﺑﻴﻦ ﺍﻟﺘﻲ ﻟﻢ ﺗﻀﻤﺮ ﻣﻦ ﺛﻨﻴﺔ ﺍﻟﻮﺩﺍﻉ ﺍﻟﻰ ﻣﺴﺠﺪ
ﺑﻨﻲ ﺯﺭﻳﻖ . ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ … ﻭﺍﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﺟﻮﺍﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻓﻲ
ﺍﻟﺠﻤﻠﺔ . ﻭﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺿﺮﺑﻴﻦ : ﻣﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ، ﻭﻣﺴﺎﺑﻘﺔ
ﺑﻌﻮﺽ . ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻮﺽ ﻓﺘﺠﻮﺯ ﻣﻄﻠﻘﺎ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﺗﻘﻴﻴﺪ ﺑﺸﻲﺀ
ﻣﻌﻴﻦ، ﻛﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻻﻗﺪﺍﻡ، ﻭﺍﻟﺴﻔﻦ، ﻭﺍﻟﻄﻴﻮﺭ، ﻭﺍﻟﺒﻐﺎﻝ، ﻭﺍﻟﺤﻤﺮ،
ﻭﺍﻟﻤﺰﺍﺭﻳﻖ، ﻭﺍﻟﻤﺼﺎﺭﻋﺔ، ﻭﺭﻓﻊ ﺍﻟﺤﺠﺮ ﻟﻴﻌﺮﻑ ﺍﻻﺷﺪ، ﻭﻏﻴﺮ ﺫﻟﻚ؛ ﻻﻥ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺳﻔﺮ ﻣﻊ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻓﺴﺎﺑﻘﺘﻪ ﻋﻠﻰ
ﺭﺟﻠﻬﺎ، ﻓﺴﺒﻘﺘﻪ، ﻗﺎﻟﺖ : ﻓﻠﻤﺎ ﺣﻤﻠﺖ ﺍﻟﻠﺤﻢ ﺳﺎﺑﻘﺘﻪ ﻓﺴﺒﻘﻨﻲ، ﻓﻘﺎﻝ :
ﻫﺬﻩ ﺑﺘﻠﻚ . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻮﺩﺍﻭﺩ . ﻭﺳﺎﺑﻖ ﺳﻠﻤﺔ ﺑﻦ ﺍﻻﻛﻮﻉ ﺭﺟﻼ ﻣﻦ ﺍﻻﻧﺼﺎﺭ
ﺑﻴﻦ ﻳﺪﻱ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺫﻱ ﻗﺮﺩ . ﻭﺻﺎﺭﻉ
ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺭﻛﺎﻧﺔ ﻓﺼﺮﻋﻪ . ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ . ﻭﻣﺮ
ﺑﻘﻮﻡ ﻳﺮﺑﻌﻮﻥ ﺣﺠﺮﺍ ﻳﻌﻨﻲ ﻳﺮﻓﻌﻮﻧﻪ ﻟﻴﻌﺮﻓﻮﺍ ﺍﻻﺷﺪ ﻣﻨﻬﻢ ﻓﻠﻢ ﻳﻨﻜﺮ
ﻋﻠﻴﻬﻢ . ﻭﺳﺎﺋﺮ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺎﺕ ﻳﻘﺎﺱ ﻋﻠﻰ ﻫﺬﺍ .{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Musabaka halal ce cikin sunnar Manzon
Allah, da Ijma’in Maluma. A cikin Sunnah dai Ibnu
Umar ya ruwaito cewa Annabi mai tsira da amincin
Allah ya shirya Musabaka tsakanin dawakin da aka
yi musu “Tadhmiir” (watau wadanda aka yi musu
horon tinkarar yaki ta hanyar karanta abinci gare su
da sanya musu tufafinsu da sauransu) a filin da ya
taso daga Haifaa har zuwa Thaniyyatul Wadaa, haka
nan ya shirya wata Musabakar tsakanin dawakin da
ba a yi musu Tadhmiiri ba, a filin da ya taso daga
Thaniyyatul Wadaa har zuwa Masjidu Bani Zuraiq.
Buhari da Muslim ne suka ruwaito hadithin…Sannan
Musulmi sun yi Ijma’i a kan halaccin Musabaka a
dunkule. Sannan ita Musabaka ta kasu ne zuwa
kashi biyu: Musabaka da ake yi tare da sanya wasu
kudi cikinta (ga duk wanda ya yi nasara). Akwai
kuma Musabaka da ake yi ba tare da an sanya kudi
cikinta (ga duk wanda ya yi nasara ba). To ita
Musabaka da ake yi ba tare da an sanya wasu kudi
cikinta ba wannan ta halatta ba tare da sanya mata
wani tarnaki a cikinta ba, kamar dai Musabakar da
ake yi na tseren gudu da kafa, ko Musabakar tseren
jiragen ruwa, ko Musabakar tsere tsakanin tsutsaye,
ko Musabakar tsere tsakanin alfadaru, ko
Musabakar tsere tsakanin jakuna, ko Musabakar
tsere tsakanin giwaye, ko Musabakar yin harbi da
kananan masu, ko Musabakar yin kokowa, ko
Musabakar daga dutse mai nauyi sanoda gwada
karfi, da dai nau’o’in Musabaka dabam daban.
Saboda Annbi mai tsira da amincin Allah wata rana
a hanyar tafiye-tafiyensa ya yi Musabakar tseren
gudu da kafa tsakaninsa da matarsa Nana A’isha
Allah Ya kara mata yarda, kuma ta yi nasara a
kansa. Sai A’isha ta ce: da na yi kiba sai wata rana
muka sake yin Musabakar tseren gudu da kafa sai
ya yi nasara a kaina. Sai ya ce da ni: ni ma na rama
wancan ci da kika yi mini. Wannan hadithi Abu
Dawuda ne ya ruwaito shi. Kuma Salamah Dan
Ak’wa ya yi Musabakar tsere da kafa tsakaninsa da
wani mutum a gaban Annabi mai tsira da amincin
Allah a ranar Ruwan Zuu Qarad. Sannan Annabi mai
tsira da amincin Allah ya yi Musabakar kokowa
tsakaninsa da wani gwanin kokowa mai suna
Rukaanah, kuma ya yi nasara a kansa ya kada shi.
Tirmizii ne ya ruwaito hafithin. Sannan wata rana
Annabi mai tsira da amincin Allah ya wuce wasu
mutane suna Musabakar daga dutse mai nauyi
saboda sanin wane ne ya fi karfi, amma bai hana su
yin hakan ba. Sauran Musabakpkin sai a kiyasta su
a kan wadannan)) [da nassi ya tabbatar]. Intaha.
2. Imamu Ibnu Qayyimil Jauziyyah wanda ya mutu a
shekarar Hijira ta 751 watau yau shekaru 684 ke
nan da suka wuce ya ce cikin littafinsa mai suna
Alfuruusiyyah 1/318:-
{ ﺍﻟﻤﺴﺎﻟﺔ ﺍﻟﺤﺎﺩﻳﺔ ﻋﺸﺮﺓ : ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺣﻔﻆ ﺍﻟﻘﺮﺍﻥ، ﻭﺍﻟﺤﺪﻳﺚ،
ﻭﺍﻟﻔﻘﻪ، ﻭﻏﻴﺮﻩ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﻠﻮﻡ ﺍﻟﻨﺎﻓﻌﺔ، ﻭﺍﻻﺻﺎﺑﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺎﺋﻞ، ﻫﻞ ﺗﺠﻮﺯ
ﺑﻌﻮﺽ؟ ﻣﻨﻌﻪ ﺍﺻﺤﺎﺏ ﻣﺎﻟﻚ، ﻭﺍﺣﻤﺪ، ﻭﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ . ﻭﺟﻮﺯﻩ ﺍﺻﺤﺎﺏ
ﺍﺑﻲ ﺣﻨﻴﻔﺔ، ﻭﺷﻴﺨﻨﺎ، ﻭﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﺒﺮ ﻋﻦ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲ . ﻭﻫﻮ ﺍﻭﻟﻰ
ﻣﻦ ﺍﻟﺸﺒﺎﻙ، ﻭﺍﻟﺼﺮﺍﻉ، ﻭﺍﻟﺴﺒﺎﺣﺔ، ﻓﻤﻦ ﺟﻮﺯ ﺍﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺑﻌﻮﺽ،
ﻓﺎﻟﻤﺴﺎﺑﻘﺔ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ، ﻭﻫﻲ ﺻﻮﺭﺓ ﻣﺮﺍﻫﻨﺔ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ
ﻟﻜﻔﺎﺭ ﻗﺮﻳﺶ ﻋﻠﻰ ﺻﺤﺔ ﻣﺎ ﺍﺧﺒﺮﻫﻢ ﺑﻪ، ﻭﺛﺒﻮﺗﻪ . ﻭﻗﺪ ﺗﻘﺪﻡ ﺍﻧﻪ ﻟﻢ
ﻳﻘﻢ ﺩﻟﻴﻞ ﺷﺮﻋﻲ ﻋﻠﻰ ﻧﺴﺨﻪ . ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺼﺪﻳﻖ ﺍﺧﺬ ﺭﻫﻨﻬﻢ ﺑﻌﺪ ﺗﺤﺮﻳﻢ
ﺍﻟﻘﻤﺎﺭ . ﻭﺍﻥ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻗﻴﺎﻣﻪ ﺑﺎﻟﺤﺠﺔ، ﻭﺍﻟﺠﻬﺎﺩ، ﻓﺎﺫﺍ ﺟﺎﺯﺕ ﺍﻟﻤﺮﺍﻫﻨﺔ
ﻋﻠﻰ ﺍﻻﺕ ﺍﻟﺠﻬﺎﺩ، ﻓﻬﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺍﻭﻟﻰ ﺑﺎﻟﺠﻮﺍﺯ . ﻭﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻮﻝ ﻫﻮ
ﺍﻟﺮﺍﺟﺢ .{ ﺍﻧﺘﻬﻰ .
Ma’ana: ((Mas’alah ta goma sha daya: Yin
Musabakar haddace Alkur’ani, da Hadithi, da Fiqhu,
da wasu Ilmummuka masu amfani, ko gane abin da
yake daidai cikin wasu mas’alolin, shirya irin
wannan Musabaka a bisa wani kudi, shin hakan zai
halatta ko kuwa ba zai halatta ba? Mutanen Malik,
da Ahmad, da Sha’fi’ii sun hana yin sa. Amma
mutanen Abu Hanifah da Malaminmu (Ibnu
Taimiyah) da ma hikayar Ibnu Abdil Barr daga
Sha’fi’ii sun halatta yinsa. Shi wannan nau’i na
Musabaka ya fi yin Musabaka a kan harkar iya sa
tarko, ko kokowa, ko ninkaya, sanoda haka
wadanda suka halatta shirya Musabaka a bisa kudi
cikin wadannan, lalle shirya Musabaka cikin harkokin
habaka ilmi shi zai fi cancantar halatta, kuma
wannan ita ce surar Muraahanar da Sbubakar Siddiq
ya yi da kafuran Quraishawa a kan gaskiyar labarin
da ya ba su (na cewa Ruumaawa za su yi nasara a
kan Faatisaawa bayan shekaru kadan). Dalili ya
gabata na cewa babu abin da ya shafe ingancin
wannan Muraahanar. Kuma shi Abubakar ya yi
Muraahanar da su ne bayan haramta yin caca.
Sannan ita tsayuwar Addini da ma tana samuwa ne
ta hanyar kafa hujja, da yin jihadi, saboda wannan
idan har Muraahanah za ta halatta a kan abubuwan
karfafa jihadi, ke nan ta halatta a kan abubuwan
karfafa ilmi da za su karfafa kafa hujja shi ne zai fi
cancanta, kuma wannan magana ita ce abin
rinjayarwa)). Intaha.
******************************
Lalle da wadannan bayanai ne mahankalta za su
fahimci cewa ita Musabakar haddar Alkur’ani mai
girma, ko musabakar haddar Hadithan Manzon Allah
Masu daraja, ko musabakar haddar wani ilmi mai
amfani -tare da sanya wani kudi ga wanda ya yi
nasara ko kuwa ba tare da sanya wani kudi ga
wanda ya yi nasara ba- abu ne da yake halal ta
hanyar hujjoji biyu:-
1. Ijma’i.
2. Qiyaasi.
Wannan kuwa duka sabanin maida ranar haihuwar
Annabi mai tsira da amincin Allah wani Idi ne,
wanda babu Ijma’i a kansa, babu kuma wani
Qiyaasi sahihi a kansa. Muna rokon Allah Ya
taimake mu Ya tabbatar da dugaduganmu a kan
Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah. Ameen.
