HotBreaking News
Fetching data...

INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINA BA LAFIYA?

*_INA YAWAN FITAR DA MANIYYI, SABODA MIJINA BA LAFIYA?_*

*Tambaya:*

Slm, Dr macece mijinta ba yada lafiyan aure tsawon lokachi, sai ya zamana tana yawan releasing ba sai tayi wani dogon tunani na sha'awaba, ya matsayin ibadarta yake ?

*Amsa:*

To gaskiya abin yake daidai shi ne: ya nemi magani, in kuma bai samu ba, ana iya raba auran, tun da yana daga cikin manufofin aure, kadange ma'aurata daga fadawa haramun, kamar yadda shararren hadisinnan ya tabbatar.

Yawan fitar maniyyi zai iya zama lalurar da za ta iya haifar da saukin sharia, saidai na ki ba zai zama lalura ba, saboda iyayenki za su iya wajabtawa mijin neman magani, in kuma bai samu ba, za ku iya rabuwa, Allah ya azurta kowa dağa falalarsa.

Cigaba da zamanku a wannan halin yana iya jefa ki cikin hadari, mata nawa ne suka zama mazinata ta hanyar wannan sababin? Ya wajaba ki yi wanka duk sanda maniyyin ya fita, tun da ya fita ne ta hanyar jin dadi.

Allah ne mafi sani.

12/6/1437

22/3/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

Amfanin Goruba 10 Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

Amfanin Goruba 10 ga lafiyar jikin dan Adam

Goruba wata bishiya ce da ta dade a duniya sannan an fi samun ta ne a kasashen Afrika. Bincike da aka gudanar akan goruba ya bayyana mamora da kuma alfanu da dama da take da shi, sakamakon sunadaran flavonoids, saponins da tananis, wanda wannan sunadaran ba sabon abu ne a wurin masana kiwon lafiya da likitoci.

Baya ga fa’idar ta wajen magance cututtuka ana amfani da ganyan ta wajen yin igiya, Kwando da tabarma.

Wannan ya sa muka binciko maku maganin cututtuka da Gorub ke yi a jikin dan adam.

Amfanin Goruba 10 ga lafiyar jikin dan Adam

1. Masu fama da cutar asma za su iya shan garin kwallon goruba a cikin tafashashen ruwa.

2. Yana taimakawa masu samun matsala lokacin fitsari.

3. Shan garinta a ruwan dumi na taimakawa masu karancin jini a ji.

4. Goruba na maganin matsalar hawan jini.

5. Haka zalika goruba na magance cutar basir.

6. Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar daji.

7. Cin goruba na kara karfin namiji.

8. Yana kuma rage kiba a jiki.

9. Cin goruba na kara karfin kashi da hakora.

10. Ruwan jikakkiyar goruba na tsiro da gashin mutum idan dai aka wanke kai da shi.

Continue reading...

ZAN IYA JAN CARBI, KO KO BIDI'A NE?

*_ZAN IYA JAN CARBI, KO KO BIDI'A NE?_*

*Tambaya:*

Assalamu Alaikum. Tambaya. Allah ya gafartawa Mal. Na kasance ina amfani da charbi (Tasbaha) domin yana tunatar dani wajen ambaton Allah a kowane lokaci.

Ina matsayin haka a sharia ?

*Amsa:*

To dan'uwa jan carbi ba bidi'a ba ne, saboda duk da cewa babu shi a zamanin Annabi ﷺ hakan ba zai sa ya zama bidi'a ba, saboda wanda yake amfani da shi ba ya nufin cewa ibada ce mai zaman kanta, yana amfani da shi ne, don ya kiyaye adadin zikirinsa.

Yin amfani da 'yan yatsu shi ne yafi, saboda hadisi ya yi nuni cewa : za'a ba su dama su yi magana, ranar alkiyama, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 3486, don haka za su yi maka shaidar abin da ka yi na alkairi, sabanin carbi.

Sannan sau da yawa za ka ga mutum yana jan carbi amma hankalisa yana wani wajen, sabanin idan da hannu yake yi.

Jan carbi yakan iya sanya wasu su yi riya, saboda wasu suna ratayawa ne a wuya don a gane su zakirai ne. Annabi ﷺ yana yin tasbihi da hannunsa na dama kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu- dawud mai lamba ta: 1286, wanda Albani ya inganta, sai dai wasu malaman suna cewa in ya yi da hagu ma yayi, tare da cewa yi da dama shi ne ya fi.

Sai dai duk da dalilan da suka gabata, mutum zai iya jan carbinsa, tun da jan carbi ba ibada ce mai zaman kanta ba, balle ace ya zama bidi'a, ga shi kuma ba'a samu wani hadisi da ya hana ba, tare da cewa yi da hannu shi ne yafi.

Don neman Karin bayani duba: Majmu'ul fataawa 22\187. Da Lika'ul maftuh na Ibnu-uthaimin 3\30.

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

Zan Iya Turawa Wanda Zan Aura Hotona, Ba Riga?

TAMBAYA 

========

👇

Assalamu alaikum mallam inada Wanda xan aura harya kawo sadaki toh saiyace inje  mallam ya hallata inje gidansu in gaida maman shi da matar shi mallam balai fi nagode 


2 mallam Wanda xan aura muna waya saiyace inturomai hotona Wanda bansa riga ba mallam inace Mai aa saiyace bakomai inturomai  mallam ya hallata intumai tunda shine xai aureni kokowa katashi lfy mallam nagode🤝🤝



AMSA 

======

👇

1. Babu lefi Dan kinyi shiga mai kyau, kinje gidan mahaifiyarsa da matarsa kun gaisa. Matukar dai baza Ku kwane wani wajenba, tinda bai zama mijinki ba. 


2. Bai halatta ki turawa wani namiji hotonki babu riga a jikinki ba. Har sai idan ya zama mijinki. Idan har ta zama mijinki to babu lefi ko yaga tsiraicin ki. Domin kin zama tasa shi kadai. Babu zargi duk abinda ya shiga tsakanin ki dashi. Kamar yadda Allah madaukakin sarki ya halatta mana a cikin Alqur'ani mai girma a cikin SURATUL MU'UMINUUN. 

 Amma ina jiye miki aikata hakan ba tare da ya zama mijinki ba. 

 Wani mijin yana karbar hoton mace, idan sun sami matsala, sai ya yada wannan hoton da zummar wai sai ya zubar mata da mutunci. Sabida yana jin haushin ta. 


Allah shine masani. 


ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08108605876

Continue reading...

ASALIN BULLAR KUNGIYAR SALAFIYYUN A TAKAICE

ASALIN BULLAR KUNGIYAR SALAFIYYUN A TAKAICE

Da'awar Shaikh Muhammad bn AbdilWahhab (r) ta zo ne a matsayin sabunta Da'awar Annabawa ta kira ga Tauhidi da kadaita Allah da bauta shi kadai, da nisantar shirka gaba daya. Kamar yadda Annabi (saw) ya samu Kuraishawa a kan bautar gumaka, ya kira su zuwa ga kadaita Allah da bauta, haka Shaikh Muh'd bn AbdilWahhab ya samu al'umma a Kasar Najadu da Hijaaz a kan shirka da bautar kabarbura, ya kira su zuwa ga Tauhidi da nisantar Shirka.

Don haka Da'awa ce da ta ginu a kan kiran al'umma zuwa ga komawa ga Musluncin farko, wanda Manzon Allah (saw) ya zo da shi; kadaita Allah da bauta da nisantar Shirka. Kuma ta ginu ne a kan Aqidar Ahlus Sunnati wal Jama'a, wato Aqidar da take cikin Alkur'ani da Sunna, wato tafarkin da Annabi (saw) yake kai shi da Sahabbansa, Salaf Magabata cikin Tabi'ai da A'imma suka bi su a kai, suka yi Ijma'i a kansa.

Kuma daga cikin abin da Aqidar Ahlus Sunna ta ginu a kai akwai Da'a wa Shugabannin Musulmai, sawa'un masu adalci ne ko azzalumai, da hakuri a kan zaluncin nasu, da rashin yi musu tawaye, matukar ba su zo da kafirci bayyananne ba.

Daga baya sai aka samu wasu kungiyoyi suka fara bulla a kasashen Larabawa bisa sabuba daban - daban, kamar mamayar Turawan Mulkin Mallaka, yaduwar Ilhadi da Almaniyanci, da mamayar Yahudawa ga Kasar Palasdinu, da Juyin juya halin Ayatullahi Khomaini a Iran, yakukuwan Kasar Afganista, da kuma yakin Saddam Hussaini na Iraq bayan ya mamaye Kasar Kuwait. Sai aka fara kafa kungiyoyin bisa manufofin yakar Turawan Mulkin Mallaka, da yakar Yahudawa da suka mamaye Kasar Palasdinu da nufin kwato Birnin Kudus, da kuma yakar Gomantoci da sunan yakar zalunci, da nufin dawo da Daular Muslunci.

Kungiya mafi girma da aka kafa bisa irin wadannan manufofi ita ce Kungiyar Ikhwanul Muslimuna a Kasar Masar, a karkashin jagorancin Ustaz Hasanul Banna, wanda asalinsa Sufiy ne Dan Dariqa. Ita wannar kungiya, kungiya ce da ba ta damu da kira ga Tauhidi da yakar Shirka da Bidi'o'i ba, kawai manufarta tara jama'a don kafa gomnati da cimma wadancan manufofi. Haka wannar kungiya ta yi tasiri a sauran kasashe, wanda daga baya aka yi ta samun kungiyoyi daban - daban da suka tasirantu da ita bisa munasabobi daban - daban, har aka samu kungiyoyin Khawarijawa masu fita daga al'umma gaba daya.

Duka irin wadannan kungiyoyi sun yi tarayya a manufar yakar Gomantocin kasashen Musulmai da sunan yakar zalunci, da nuna nufin gyara al'umma ta hanyar kawar da Gomnatoci da kafa tasu bisa tsarin Kungiyoyin.

Wannan ya sa aka samu jaddada Da'awa ta Salafiyya mai kalu-balantar irin wadannan Kungiyoyi, da kira ga lazimtar Jama'ar Musulmi da take karkashin shugabanci, da kiran al'umma zuwa ga lazimtar Aqidar Ahlus Sunna da ta kunshi riko da Tauhidi da Sunna da nisantar Shirka da Bidi'o'i da kungiyoyinsu, da hana tawaye wa shugabannin Musulmai, da rashin rarraba kan al'umma ta hanyar kafa kungiyoyi masu manufar Tawaye wa shugaba. Da'awar Salafiyya bisa wannan Manhaji shi ne abin da Malamai suke kai a Saudiyya, tun da ita ce dai Da'awar Shaikh Muhammad bn AbdilWahhab ta kira ga Tauhidi da Sunna da yakar Shirka da Bidi'o'i, da kuma hada kan al'umma a karkashin shugaban Musulmai ba tare da rarrabuwa kungiya - kungiya ba.

Amma sai dai daga baya kuma wasu daga cikin masu Da'awar Salafiyyar suka fara tsanantawa a kan sauran 'yan uwansu Ahlus Sunna mabiya wannar Da'awar ta Salafiyya, suka dawo suna suka da bidi'antar da su da fitar da su daga Sunna da koransu daga Salafiyya bisa kurakuran da ba su kai ga haka ba, da takaice Salafiyya da wani sabon manhaji, da mayar da ita kungiya ta Malami guda daya. Duka da sunan aiki da ilimin "Jarhi da Ta'adili" wanda Malaman Hadisi suke amfani da shi wajen tantance Hadisan Annabi (saw). Wannan Manhaji ya jawo rarrabuwar kan Ahlus Sunna masu Da'awar Salafiyya.

Wannan ya sa Manyan Malamai suka shagala wajen Nasiha da fadakarwa ga masu irin wannan sabon Manhaji, musamman Manyan Malaman nan uku:

1- Samahatus Shaikh AbdulAzeez Ibnu Baaz.

2- Babban Malamin Fiqhu Shaikh Muhammad Ibnul Uthaimeen.

3- Babban Malamin Hadisi Shaikh Muhammad Nasiruddeen Albaniy.

Daga cikinsu har aka samu wadanda suka wallafa littatafai don kashe wutar wannar fitina da ta kunnu tsakanin masu Da'awar Salafiyya. Daga cikinsu akwai;

1- Babban Malamin Hadisi a Madina Shaikh AbdulMuhsin Al-Abbad Al- Badar, wanda ya wallafa littatafai har guda uku a kan wannar matsala:

(a) ﺭﻓﻘﺎ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺑﺄﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ

(b) ﻭﻣﺮﺓ ﺃﺧﺮﻯ ﺭﻓﻘﺎ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺑﺄﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ

(c) ﺍﻟﺤﺚ ﻋﻠﻰ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺘﺤﺬﻳﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﺑﻴﺎﻥ ﺧﻄﺮﻫﺎ

Wadannan littatafai ba su yi dadi ga masu Guluwwi a bidi'antarwa ba, wadanda suka mayar da Salafiyya a matsayin wata Kungiya ta wani Malami guda daya. Har yau suna matukar jin haushin littafi na farkon.

2- Babban Malami Muhaqqiq Shaikh Bakar Abu Zaid, wanda ya wallafa littafi mai suna:

ﺗﺼﻨﻴﻒ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻈﻦ ﻭﺍﻟﻴﻘﻴﻦ

Shi ma wannan littafi bai yi musu dadi ba.

Haka aka cigaba da samun littatafai da suke yakar wannan Manhaji na Kungiyanci da raba kan Ahlus Sunna da guluwwi a bidi'antarwa da sunan Salafiyya.

Sai aka samu:

3- Shaikh Muhammad bn Abdallah Al-Imam, wanda ya wallafa:

ﺍﻹﺑﺎﻧﺔ ﻋﻦ ﻛﻴﻔﻴﺔ ﺍﻟﺘﻌﺎﻣﻞ ﻣﻊ ﺍﻟﺨﻼﻑ ﺑﻴﻦ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ

Wannan littafi ya samu yabo daga Manyan Malamanmu, daga cikinsu akwai Shaikh Saleh Al- Suhaimiy, wanda ya ce: a wannan zamani ba a wallafa littafi kamarsa ba.

4- Shaikh Ibrahim Al-Ruhailiy, wanda ya wallafa:

ﺍﻟﻨﺼﻴﺤﺔ ﻓﻴﻤﺎ ﻳﺠﺐ ﻣﺮﺍﻋﺎﺗﻪ ﻋﻨﺪ ﺍﻻﺧﺘﻼﻑ ﻭﺿﻮﺍﺑﻂ ﻫﺠﺮ ﺍﻟﻤﺨﺎﻟﻒ ﻭﺍﻟﺮﺩ ﻋﻠﻴﻪ

Malaminmu ne a Jami'ar Madina da Masallacin Annabi (saw), amma sai da ta kai suna mu'amalantarsa mu'amala ta kafirai saboda tsananin guluwwi.

5- Daga karshe an samu Babban Malaminmu Shaikh Saleh Al-Suhaimiy ya wallafa littafi mai suna:

ﺗﻨﺒﻴﻪ ﺫﻭﻱ ﺍﻷﻓﻬﺎﻡ ﻋﻠﻰ ﺭﺃﺏ ﺍﻟﺼﺪﻉ ﻭﺍﻟﻮﺋﺎﻡ ﻋﻠﻰ ﻣﻨﻬﺞ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﻜﺮﺍﻡ

6- Kafinsa akwai littafin Shaikh Aliy Al-Halabiy Almajirin Shaikh Albaniy, wanda ya wallafa:

ﻣﻨﻬﺞ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ ﻓﻲ ﺗﺮﺟﻴﺢ ﺍﻟﻤﺼﺎﻟﺢ ﻭﺗﻄﻮﻳﺢ ﺍﻟﻤﻔﺎﺳﺪ ﻭﺍﻟﻘﺒﺎﺋﺢ ﻓﻲ ﺃﺻﻮﻝ ﺍﻟﻨﻘﺪ ﻭﺍﻟﺠﺮﺡ ﻭﺍﻟﻨﺼﺎﺋﺢ

To kasancewar wadannan littatafai da ire - irensu sun yi bayanin bacin Manhajin Kungiyar Salafiyyun shi ya sa 'Yan kungiyar suke matukar fada da kwadaitar da dalibai a kan karanta su.

Alhali duk wanda ya karanta wadannan littatafai zai fahimci bacin wannan Manhaji na Guluwwi a Bidi'antarwa da raba kan Ahlus Sunna da kungiyanci da sunan Salafiyya. Kuma duk wanda ya yi aiki da abin da yake cikinsu na bayanin gaskiya to ya rabu da Manhajin Kungiyar Salafiyyun tun daga farkonsa har karshensa.

Kuma har yau manyan Malaman Saudiyya tun daga kan "Hai'atu Kibaril Ulama'i" har kasa, suna gargadin Daliban ilimi da tsoratar da su ga wannan Manhaji na Kungiyanci da Guluwwi da raba kan Ahlus Sunna.

Continue reading...

DUK SABANIN DA YA KAI GA RABUWA DAGA JAMA'AR AHLUS SUNNA SABANI NE DA BA YA CIKIN ADDININ MUSLUNCI

DUK SABANIN DA YA KAI GA RABUWA DAGA JAMA'AR AHLUS SUNNA SABANI NE DA BA YA CIKIN ADDININ MUSLUNCI

Lallai idan muka nazarci nassoshin Shari'a za mu ga cewa; sabani a tsakanin mutane abu ne kaddararre, ba zai gushe a cikin 'yan Adam ba, Allah ya kaddara shi ne don ya jarabi bayinsa, don a tantance shaqiyyai 'yan wuta da masu rabo.

{ ﻭَﻟَﻮْ ﺷَﺎﺀَ ﺭَﺑُّﻚَ ﻟَﺠَﻌَﻞَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱَ ﺃُﻣَّﺔً ﻭَﺍﺣِﺪَﺓً ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺰَﺍﻟُﻮﻥَ ﻣُﺨْﺘَﻠِﻔِﻴﻦَ ‏( 118 ‏) ﺇِﻟَّﺎ ﻣَﻦْ ﺭَﺣِﻢَ ﺭَﺑُّﻚَ ﻭَﻟِﺬَﻟِﻚَ ﺧَﻠَﻘَﻬُﻢْ ﻭَﺗَﻤَّﺖْ ﻛَﻠِﻤَﺔُ ﺭَﺑِّﻚَ ﻟَﺄَﻣْﻠَﺄَﻥَّ ﺟَﻬَﻨَّﻢَ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺠِﻨَّﺔِ ﻭَﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﺃَﺟْﻤَﻌِﻴﻦَ { ‏[ ﻫﻮﺩ : 118 ، 119 ]

Sai Allah ya bayyana cewa; mutane ba za su gushe suna sabani ba, amma kuma sai ya kasa mutanen kashi biyu a bayan sabanin; wadanda Allah ya yi musu rahama, masu rabo kenan, da kuma wadanda zai cika Jahannama da su.

To amma Allah saboda rahamarsa bai sanya nau'in sabanin ya zama kashi daya kawai ba, saboda dabi'ar da ya halicci mutane a kanta tun asali, na ba za su gushe suna masu sabani a tsakaninsu ba, saboda haka ya sanya sabanin ya kasu kashi biyu;

1- Sabani da yake cikin Addini, wanda ba ya kaiwa ga gaba da kiyayya da kaurace ma juna da rabuwar kai, shi ne wanda ake komawa ga Qur'ani da Sunna don warware shi, kuma shi ne irin sabanin da ya faru a tsakanin Sahabbai.

Allah ya ce:

{ ﻭَﻣَﺎ ﺍﺧْﺘَﻠَﻔْﺘُﻢْ ﻓِﻴﻪِ ﻣِﻦْ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﺤُﻜْﻤُﻪُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ { ‏[ ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ : 10 ]

"Dukkan wani abu da kuka yi sabani a cikinsa to hukuncinsa yana wajen Allah".

Kuma ya ce:

{ ﻓَﺈِﻥْ ﺗَﻨَﺎﺯَﻋْﺘُﻢْ ﻓِﻲ ﺷَﻲْﺀٍ ﻓَﺮُﺩُّﻭﻩُ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺍﻟﺮَّﺳُﻮﻝِ ﺇِﻥْ ﻛُﻨْﺘُﻢْ ﺗُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻟْﺂﺧِﺮِ ﺫَﻟِﻚَ ﺧَﻴْﺮٌ ﻭَﺃَﺣْﺴَﻦُ ﺗَﺄْﻭِﻳﻠًﺎ { ‏[ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ : 59 ]

"Idan kun yi jayayya a kan wani abu to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa in kun kasance kuna imani da Allah da ranar Lahira, hakan shi ne mafi alheri kuma mafi kyaun fassara".

2- Sabani da ba ya cikin Addini, wanda yake kaiwa ga gaba da kiyayya da kaurace ma juna da rabuwar kai, shi ne wanda yake abin zargi a cikin nassoshin Shari'a, wanda ake yinsa a bisa wata manufa ta daban, ba don Allah ba, sai don bin son rai ko neman biyan wata bukata ta abin duniya, ko biyan wata sha'awa da take cikin zuciya.

Allah ya ce:

{ ﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻓَﺮَّﻗُﻮﺍ ﺩِﻳﻨَﻬُﻢْ ﻭَﻛَﺎﻧُﻮﺍ ﺷِﻴَﻌًﺎ ﻟَﺴْﺖَ ﻣِﻨْﻬُﻢْ ﻓِﻲ ﺷَﻲْﺀٍ { ‏[ ﺍﻷﻧﻌﺎﻡ : 159 ]

"Lallai wadanda suka raba Addininsu suka zama kungiya – kungiya ba ka tare da su a komai (Annabi (saw) ba ya daga cikin kowane bangare da ya rabe daga Jama'a, Annabi (saw) ba ya tare da su a komai)".

Al- Imamus Shatibiy ya naqalto wata magana daga wani malami inda ya ce:

ﻛﻞ ﻣﺴﺄﻟﺔ ﺣﺪﺛﺖ ﻓﻲ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻭﺍﺧﺘﻠﻒ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻴﻬﺎ ﻭﻟﻢ ﻳﻮﺭﺙ ﺫﻟﻚ ﺍﻻﺧﺘﻼﻑ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﻋﺪﺍﻭﺓ ﻭﻻ ﺑﻐﻀﺎﺀ ﻭﻻ ﻓﺮﻗﺔ، ﻋﻠﻤﻨﺎ ﺃﻧﻬﺎ ﻣﻦ ﻣﺴﺎﺋﻞ ﺍﻹﺳﻼﻡ، ﻭﻛﻞ ﻣﺴﺄﻟﺔ ﺣﺪﺛﺖ ﻭﻃﺮﺃﺕ ﻓﺄﻭﺟﺒﺖ ﺍﻟﻌﺪﺍﻭﺓ ﻭﺍﻟﺒﻐﻀﺎﺀ ﻭﺍﻟﺘﺪﺍﺑﺮ ﻭﺍﻟﻘﻄﻴﻌﺔ ﻋﻠﻤﻨﺎ ﺃﻧﻬﺎ ﻟﻴﺴﺖ ﻣﻦ ﺃﻣﺮ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻓﻲ ﺷﻲﺀ، ﻭﺃﻧﻬﺎ ﺍﻟﺘﻲ ﻋﻨﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺑﺘﻔﺴﻴﺮ ﺍﻵﻳﺔ .

ﻭﺫﻟﻚ ﻣﺎ ﺭﻭﻱ ﻋﻦ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﻗﺎﻟﺖ : ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ " : ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺸﺔ، ﺇﻥ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻓﺮﻗﻮﺍ ﺩﻳﻨﻬﻢ ﻭﻛﺎﻧﻮﺍ ﺷﻴﻌﺎ، ﻣﻦ ﻫﻢ؟ ﻗﻠﺖ : ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﺃﻋﻠﻢ . ﻗﺎﻝ : ﻫﻢ ﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻷﻫﻮﺍﺀ ﻭﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﺃﺻﺤﺎﺏ ﺍﻟﻀﻼﻟﺔ ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻷﻣﺔ " ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﻭﻗﺪ ﺗﻘﺪﻡ ﺫﻛﺮﻩ .

ﻗﺎﻝ : ﻓﻴﺠﺐ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺫﻱ ﻋﻘﻞ ﻭﺩﻳﻦ ﺃﻥ ﻳﺠﺘﻨﺒﻬﺎ، ﻭﺩﻟﻴﻞ ﺫﻟﻚ ﻗﻮﻟﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ : } ﻭﺍﺫﻛﺮﻭﺍ ﻧﻌﻤﺖ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺇﺫ ﻛﻨﺘﻢ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﻓﺄﻟﻒ ﺑﻴﻦ ﻗﻠﻮﺑﻜﻢ ﻓﺄﺻﺒﺤﺘﻢ ﺑﻨﻌﻤﺘﻪ ﺇﺧﻮﺍﻧﺎ { ، ﻓﺈﺫﺍ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﻭﺗﻘﺎﻃﻌﻮﺍ ﻛﺎﻥ ﺫﻟﻚ ﻟﺤﺪﺙ ﺃﺣﺪﺛﻮﻩ ﻣﻦ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﺍﻟﻬﻮﻯ ..

ﻫﺬﺍ ﻣﺎ ﻗﺎﻟﻪ، ﻭﻫﻮ ﻇﺎﻫﺮ ﻓﻲ ﺃﻥ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻳﺪﻋﻮ ﺇﻟﻰ ﺍﻷﻟﻔﺔ ﻭﺍﻟﺘﺤﺎﺏ ﻭﺍﻟﺘﺮﺍﺣﻢ ﻭﺍﻟﺘﻌﺎﻃﻒ، ﻓﻜﻞ ﺭﺃﻱ ﺃﺩﻯ ﺇﻟﻰ ﺧﻼﻑ ﺫﻟﻚ ﻓﺨﺎﺭﺝ ﻋﻦ ﺍﻟﺪﻳﻦ

ﺍﻻﻋﺘﺼﺎﻡ ﻟﻠﺸﺎﻃﺒﻲ ‏( /3 169 – 170 ‏) ، ﺍﻟﻤﻮﺍﻓﻘﺎﺕ ‏( /5 163 - 164 )

"Dukkan wata mas'alar da ta faru a cikin muslunci sai mutane suka yi sabani a cikinta, amma kuma wannan sabani bai gadar da gaba da kiyayya da rabuwar kai a tsakaninsu ba, to mun san cewa; tana cikin mas'alolin Muslunci.

Dukkan wata mas'alar da ta faru ta bijiro sai ta samar da gaba da kiyayya da juya baya ma juna (kauracewa) da yanke alaka, to mun san cewa; ba ta cikin lamarin Addini a komai, kuma ita ce wacce Annabi (saw) yake nufinta a tafsirin ayar, a hadisin da aka ruwaito daga A'isha (ra) ta ce: Manzon Allah (saw) ya ce:

"Ya ke A'isha, wadanda suka raba Addininsu suka zama kungiya – kungiya su wanene su?".

Sai ta ce: Allah da Manzonsa ne suka sani.

Sai ya ce:

"Su ne ma'abota son rai, da ma'abota bidi'a, da ma'abota bata daga wannar al'umma". Hadisin ya gabata (sai dai bai inganta ba).

Ya ce: Don haka ya wajaba a kan kowane mai hankali mai riko da Addini ya nisancesu, dalili a kan haka shi ne fadin Allah (T):

{ ﻭَﺍﺫْﻛُﺮُﻭﺍ ﻧِﻌْﻤَﺖَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﺇِﺫْ ﻛُﻨْﺘُﻢْ ﺃَﻋْﺪَﺍﺀً ﻓَﺄَﻟَّﻒَ ﺑَﻴْﻦَ ﻗُﻠُﻮﺑِﻜُﻢْ ﻓَﺄَﺻْﺒَﺤْﺘُﻢْ ﺑِﻨِﻌْﻤَﺘِﻪِ ﺇِﺧْﻮَﺍﻧًﺎ { ‏[ ﺁﻝ ﻋﻤﺮﺍﻥ : 103 ]

"Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lokacin da kuka kasance abokan gaba, sai ya hada zukatanku, sai kuka wayi gari kuna 'yan uwan juna da ni'imarsa".

Saboda haka idan suka yi sabani suka yanke alaka hakan ya kasance ne a dalilin bin son rai da suka kirkira.

Wannan shi ne abin da malamin ya fada, kuma a bayyane yake cewa; Muslunci yana kira ne zuwa ga hadin kai da soyayya da tausayi da tausasawa, saboda haka duk ra'ayin da ya kai ga sabanin haka to ya fita daga cikin Addinin Muslunci".

Duba Al- li'itisam 3/ 169 – 170, da Al- Muwafaqat 5/ 163 – 164.

Saboda haka dukkan sabani da ya kai ga fitina da rabuwar kai sabani ne abin zargi, kuma ba ya cikin Addini, saboda da yana cikin Addini da bai kai ga rabuwar kai ba, saboda sabani na cikin Addini ba ya kaiwa ga raba kai, da gaba da kiyayya, shi ya sa aka samu Salaf; Sahabbai da Tabi'ai da A'imma sun yi sabani amma bai kai ga gaba da kauracewa da rabuwar kai ba.

Saboda haka, dukkan sabanin da za ayi a kan mas'aloli na Ijtihadi ko a kan Sunnoni Mustahabbai amma har ya kai ga rabuwar kai to ba ya cikin Addini, saboda an yi sabanin ne saboda bin son rai, ko neman abin duniya, ko neman biyan wata bukata da take cikin zuciya, in da don Allah aka yi da ba za a taba samun rabuwar kai da gaba da kaurace masallaci da makamancin haka ba.

Allah ya shiryar da mu ya yi mana afuwa.

Continue reading...

BABU ABIN DA YAKE KAWO SABANI NA RABUWAR KAI KAMAR JAHILCI DA ZALUNCI DA MUMMUNAN NUFI

BABU ABIN DA YAKE KAWO SABANI NA RABUWAR KAI KAMAR JAHILCI DA ZALUNCI DA MUMMUNAN NUFI

Lallai sabuba da dalilai da suke kaiwa ga mummunan sabani wanda Allah da Manzonsa (saw) suka yi zargi a kansa, kuma Allah ya tanadi azaba a kansa, wanda yake raba kan al'umma suna da yawa, amma mafi girmansu shi ne JAHILCI da BACIN NIYYA DA MUNGUN NUFI, wanda ya kunshi kulla zalunci da hasada a cikin zuciya da son neman daukaka a bayan kasa. Wannan shi ne sababin da ya sa Yahudawa suka yi sabani da rarrabuwa a tsakaninsu, kuma Allah ya zargesu a dalilin haka.

Allah ya ce:

ﻭﻟﻘﺪ ﺁﺗﻴﻨﺎ ﺑﻨﻲ ﺇﺳﺮﺍﺋﻴﻞ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺤﻜﻢ ﻭﺍﻟﻨﺒﻮﺓ ﻭﺭﺯﻗﻨﺎﻫﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻄﻴﺒﺎﺕ ﻭﻓﻀﻠﻨﺎﻫﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ‏( 16 ‏) ﻭﺁﺗﻴﻨﺎﻫﻢ ﺑﻴﻨﺎﺕ ﻣﻦ ﺍﻷﻣﺮ ﻓﻤﺎ ﺍﺧﺘﻠﻔﻮﺍ ﺇﻻ ﻣﻦ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﺟﺎﺀﻫﻢ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺑﻐﻴﺎ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﺇﻥ ﺭﺑﻚ ﻳﻘﻀﻲ ﺑﻴﻨﻬﻢ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻓﻴﻤﺎ ﻛﺎﻧﻮﺍ ﻓﻴﻪ ﻳﺨﺘﻠﻔﻮﻥ ‏( 17 )

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah (r) ya ce:

ﺍﻻﺧﺘﻼﻑ ﺍﻟﻤﺬﻣﻮﻡ ﻣﻦ ﺍﻟﻄﺮﻓﻴﻦ ﻳﻜﻮﻥ ﺳﺒﺒﻪ ﺗﺎﺭﺓ : ﻓﺴﺎﺩ ﺍﻟﻨﻴﺔ؛ ﻟﻤﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﻨﻔﻮﺱ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﻐﻲ ﻭﺍﻟﺤﺴﺪ ﻭﺇﺭﺍﺩﺓ ﺍﻟﻌﻠﻮ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ، ﻓﻴﺤﺐ ﻟﺬﻟﻚ ﺫﻡ ﻗﻮﻝ ﻏﻴﺮﻫﺎ، ﺃﻭ ﻓﻌﻠﻪ، ﺃﻭ ﻏﻠﺒﺘﻪ ﻟﻴﺘﻤﻴﺰ ﻋﻠﻴﻪ، ﺃﻭ ﻳﺤﺐ ﻗﻮﻝ ﻣﻦ ﻳﻮﺍﻓﻘﻪ ﻓﻲ ﻧﺴﺐ ﺃﻭ ﻣﺬﻫﺐ ﺃﻭ ﺑﻠﺪ ﺃﻭ ﺻﺪﺍﻗﺔ، ﻭﻧﺤﻮ ﺫﻟﻚ، ﻟﻤﺎ ﻓﻲ ﻗﻴﺎﻡ ﻗﻮﻟﻪ ﻣﻦ ﺣﺼﻮﻝ ﺍﻟﺸﺮﻑ ﻭﺍﻟﺮﺋﺎﺳﺔ ﻭﻣﺎ ﺃﻛﺜﺮ ﻫﺬﺍ ﻣﻦ ﺑﻨﻲ ﺁﺩﻡ، ﻭﻫﺬﺍ ﻇﻠﻢ .

ﻭﻳﻜﻮﻥ ﺳﺒﺒﻪ - ﺗﺎﺭﺓ - ﺟﻬﻞ ﺍﻟﻤﺨﺘﻠﻔﻴﻦ ﺑﺤﻘﻴﻘﺔ ﺍﻷﻣﺮ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺘﻨﺎﺯﻋﺎﻥ ﻓﻴﻪ، ﺃﻭ ﺍﻟﺠﻬﻞ ﺑﺎﻟﺪﻟﻴﻞ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﺮﺷﺪ ﺑﻪ ﺃﺣﺪﻫﻤﺎ ﺍﻵﺧﺮ، ﺃﻭ ﺟﻬﻞ ﺃﺣﺪﻫﻤﺎ ﺑﻤﺎ ﻣﻊ ﺍﻵﺧﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻖ : ﻓﻲ ﺍﻟﺤﻜﻢ، ﺃﻭ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻟﻴﻞ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻋﺎﻟﻤﺎ ﺑﻤﺎ ﻣﻊ ﻧﻔﺴﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺤﻖ ﺣﻜﻤﺎ ﻭﺩﻟﻴﻼ .

ﻭﺍﻟﺠﻬﻞ ﻭﺍﻟﻈﻠﻢ : ﻫﻤﺎ ﺃﺻﻞ ﻛﻞ ﺷﺮ، ﻛﻤﺎ ﻗﺎﻝ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ : } ﻭﺣﻤﻠﻬﺎ ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻇﻠﻮﻣﺎ ﺟﻬﻮﻻ }.

Ya ce:

"Mummunan sabani (na rabuwar kai) wanda yake abin zargi a tsakanin dukkan bangarorin guda 2, a wani lokacin sababinsa yana kasancewa ne a dalilin bacin niyya (mummunan nufi), saboda abin da ke cikin zukata na zalunci (wuce iyaka da ketare haddin Shari'a ta hanyar kin aikata wani abin da aka wajabta a lokacin sabanin ko aikata wani abin da aka haramta in sabanin ya auku), da hasada da son samun daukaka a bayan kasa da makamancin haka. Saboda wannan sai bangare ya so ya zargi ra'ayin daya bangaren, ko aikinsa, ya ki yarda da shi, ko neman ya yi galba a kansa don ya nuna ya fi shi, ko ya so ra'ayin wanda ya dace da shi a dangantaka ko mazhaba ko gari ko abokantaka da makamancin haka, saboda in ra'ayinsa ya tabbata ya tsayu to zai samu matsayi da shugabanci. Abin mamaki, akwai irin wannan kuwa masu yawa a cikin 'yan adam. Wannan kuwa zalunci ne (wuce iyakan Allah).

A wani lokacin kuwa sababin sabanin bangarorin yana kasancewa ne a dalilin jahilcin masu sabanin ne a kan hakikanin lamarin da suke sabani a kansa, ko jahilci game da dalilin da daya bangaren yake kafa hujja da shi ma daya bangaren, ko jahilcin daya bangaren da dalilin da yake tare da daya bangaren na gaskiya, a hukuncin ko a dalilin (imma yana da gaskiya a hukunci, amma ba shi da gaskiya a dalili, ko kuma yana da gaskiya a dalili amma kuma ba shi da gaskiya a hukunci), ko da kuwa shi yana da ilmi game da abin da ya rike nasa na gaskiya a hukuncin da dalilin.

JAHILCI DA ZALUNCI SU NE ASALIN KOWANE SHARRI, kamar yadda Allah ya ce:

{ ﻭﺣﻤﻠﻬﺎ ﺍﻹﻧﺴﺎﻥ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻇﻠﻮﻣﺎ ﺟﻬﻮﻻ }

"... Mutum ya kasance mai matukar zalunci da jahilci".

Duba Iqtidha'us Siradil Mustaqeem 1/ 131 - 132.

Abin lura:

1. Babban abin da yake haifar da rabuwar kai a cikin al'umma shi ne ZALUNCI DA JAHILCI.

2. Zalunci shi ne ketare iyakan Allah da dokokin Shari'arsa, ta hanyar kin aikata abin da ya wajaba a lokacin da sabani ya faru, ko aikata abin da ya haramta. Kamar kin yarda da SULHU, ko kin yarda da ZAMA TARE DON A TATTAUNA MAS'ALOLIN DA AKA YI SABANI A KANSU, ko KAURACE MA JUNA, ko KIN YIN SALLAMA DA YANKE ALAKA A TSAKANI, ko KIN KARBAN GASKIYA BAYAN TA BAYYANA da makamancin irin abubuwan da suke wajibi ne a aikatasu a lokacin da sabani ya auku a tsakanin bangarori guda biyu na Ahlus Sunna ko suka haramta a aikatasu.

3. Jahilci imma ya zama ta bangaren malamai, ko ta bangaren mabiya.

(a) Ta bangaren malamai shi ne wanda yake kasancewa a sakamakon gazawa wajen bincike a kan mas'alolin da aka yi sabani a kansu, ta yadda zai jahilci hakikanin mas'alolin a dalili ko a hukunci, ko ya jahilci na abokin sabanin nasa.

(b) Ta bangaren mabiya kuwa, a mafi yawan hali za ka samu mabiyan su mukallidai ne, ba su da ta cewa a mas'alolin ilmi, amma kuma su ne a kan gaba wajen zalunci da rura wutar fitina da haddasa gaba da kiyayya a tsakani, har su taimaka wa malamin nasu ko jagoran nasu wajen kin yarda da gaskiya bayan ta bayyana masa. Irin wadannan mabiya sun zama shedanu, masu haddasa fitina da raba kan al'umma, masu toshe hanyar Allah.

4. Mummunan nufi shi yake haifar da ta'assubanci (bin ra'ayi don biyan bukata ta kashin kai ko son zuciya) da kin karban gaskiya da aiki da ita.

5. Duka wadannan ababen tambaya ne a ranar kiyama, Allah ya yi gargadi a kan sabani na rabuwar kai da sabubansu, kuma ya tanadi azaba mai girma a kansu.

Ya Allah ka yi mana afuwa ka kubutar da mu.

Continue reading...

IDAN MIJI YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA BATUN GADO DA TAKABA?

*_IDAN MIJI YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA BATUN GADO DA TAKABA?_*

*Tambaya:*

Assalam pls an daura auren wasu yau ba'a dauko amarya ba sai gobe, amma Allah yayi wa angon rasuwa..tambayata anan wai shin za tayi takaba? Kuma tanada gadonshi?

*Amsa:*

To dan'uwa idan miji ya mutu bayan an daura aure kafin ya tare da amryarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa takaba, kuma a bata gadonta cikakke, kamar yadda Annabi ﷺ ya yi hukunci da hakan ga Barwa'u 'yar Washik lokacin da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai lamba ta: 1145, wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi.

Allah ne mafi sani.

5\1\2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

INA CIKIN IDDA, SAI WANI YA YI ZINA DA NI ! YAYA ZAN YI ?

INA CIKIN IDDA, SAI WANI YA YI ZINA DA NI ! YAYA ZAN YI ?

Tambaya :

Malam mijina ya sake ni, bayan na yi tsarki daya, sai rikici ya kaure tsakanin arna da musulmai a garinmu, sai wani crister, ya dauke ni ya yi zina da ni, yanzu malam yaya zan yi game da idda ta ?

Amsa :

To 'yar'uwa ina rokon Allah ya kawowa musulmi dauki a Nigeria, wannan mas'alar ta ki malamai sun yi sabani akanta, akwai malaman da suka tafi akan dole sai kin yi istibra'i bayan kin gama idda, saidai maganar da tafi zama daidai ita ce : kawai za ki karasa iddarki ne, ba sai kin yi istibra'i ba bayan kin kammala, saboda babbar manufar istibra'i ita ce kubutar mahaifa, hakan kuma zai tabbata idan kika karasa jinane biyun da suka rage miki na iddarki.

Yana daga cikin saukin addinin musulunci kasancewar duk ibadojin da za su iya shiga cikin juna kuma manufarsu daya ce, jinsinsu guda ne, to daya za ta shiga cikin daya, kamar wacce ta yi jima'i sai kuma haila ta zo mata, wanka guda daya ya ishe ta a karshen hailarta.

Allah ne mafi sani.

Duba : Majmu'ul fawa'id na Sa'ady shafi na : 141.

Jameelu Yusuf Zarewa

25/12/2014

Continue reading...

MANYAN LADUBBA AKAN MUSULM GUDA 10 A RANAR JUMA'A

MANYAN LADUBBA AKAN MUSULM GUDA 10 A RANAR JUMA'A.


Hakika Annabi s.a.w ya kebe ranar juma'a da wadansu Ladubba masu yawa,ga kadai daga cikinsu:


*1-Karanta suratul Sadaja da suratul Insan Acikin Sallar Assuba ta ranar Juma'a*.


Domin Annabi s.a.w ya kasance yana karantasu a Sallar assubar ranar Juma'a.

@Bukhari da Muslim.


*2-Yawaita Yin Salati ga Annabi s.a.w*


Annabi s.a.w yana cewa:

"Ranar juma itace mafificiyar rana daga cikin ranakunku acikinta ne aka halicci Annabi Adamu................. Kuma ka yawaita yimin Salati acikinta......"

@Ahmad Kuma Albany yace Hadisine HASAN

@Ana fara yawaitawa


Annabi s.a.w Salatine na ranar juma'a tun daga daran juma'ar wato yau alhamis da dare kamar yadda wani Hadisin ya bayyana.


*3-Yin wanka ranar juma'a*


Saboda Fadar Annabi s.a.w:

"Idan ranar juma'a ta riski dayanku to yayi wanka".

@Bukhari da Muslim


*4-Sanya Turare Da Yin Aswaki*.


Annabi s.a.w yana cewa:

"Wankan ranar juma'a wajibine akan duk wanda ya balaga,da yin Aswaki da Sahafa abinda ya saukaka na Turard".

@Muslim


*5-Zuwa Masallacin Juma'a da wuri*.


Manzon Allah s.a.w yana cewa:

"Idan Ranar juma'a tazo Mala'iku suna tsayawa abakin kofar Masallaci suna rubuwa wanda yazo dawuri sannnan wanda ya biyo bayansa................ idan kuma liman ya hau kan minbari yafara khudiba sai su nade takardun su saurari khudibar liman".

@Bukhari da Muslim


*6-Karanta Suratul Kahfi*.


An samu daga aikin wadansu Sahabbai R.A sunayin Hakan.

@Saheehul Jami'i


*7-Yin Shiru da Sauraran Khudiba idan liman Yanayin Khudiba*.


saboda fadar Annabi s.a.w:

*"Idan kacewa dan uwanka yayi shiru alokacin da liman yake huduba,to kayi Lagawu"*.

@Bukhari da Muslim


*8-Kada ka riqa ketara mutune dan Kazauna asahun gaba,ka zauna idan sahu ya tsaya*


Daga Jabir Dan abdillahi yana cewa wani mutum yashiga Masallaci ranar juma'a alokacin Annabi s.a.w yana yin khuduba sai ya riqa qetara mutane, sai Annabi s.a.w yace dashi

*"Zauna hakika ka cutar ka cutar"*.

@Ibn Majah ya ruwaitoshi kuma Albany ya Ingantasa.


*9-Yin Nafila raka'a guda biyi,idan kashiga Masallacin koda liman yana Hudubane*


Annabi s.a.w yana cewa:

"Idan dayanku yazo sallar juma'a sai ya tarar da Liman yana huduba,to kada ya zauna har sai yayi sallah raka'a biyu sannan ya zauna".

@Muslim


*10-Yawaita rokon Allah aranar Juma'a*


Manzon Allah s.a.w yana cewa:

"Ku yawaita rokon Allah aranar juma'a domin akwai wani lokaci acikinta wanda babu wani bawa da zai dace da wannan lokaci ya tsaya yana rokon Allah acikinsa face Allah ya bashi abinda yaroka".*sai yayi nuni da hannunsa akan lokacin dan kadanne*.

@Bukhari da Muslim


Amma malamai sunfi rinjayar da lokuta guda biyu:

√Daga Hawan Liman kan mimbari zuwa kare Sallah.


√Daga Bayn Sallar La'asar zuwa Faduwar rana.

Amma magana mafi inganci kuma mafi rinjaye awajan Malamai shine daga bayan Sallah La'asar zuwa faduwar Rana.

@Zadul-Ma'ad


    Allah ne mafi sani.

Continue reading...

YADDA AKE SALLAR GAWA A SAUKAKE

YADDA AKE SALLAR GAWA A SAUKAKE


1-Kabbara ta Farko:

*Idan yayi kabbara ta farko,za'a karanta suratul Fatiha da sura a sirrance.batare da addu'ar bude sallah ba*

@ ﺃﺧﺮﺟﻪ اﻟﺒﺨﺎﺭﻱ (3/ 158) ﻭﺃﺑﻮ ﺩاﻭﺩ (2، 68) ﻭاﻟﻨﺴﺎﺋﻲ (1/ 281) ﻭاﻟﺘﺮﻣﺬﻱ (2/ 142) ﻭاﺑﻦ اﻟﺠﺎﺭﻭﺩ ﻓﻲ " اﻟﻤﻨﺘﻔﻰ " (264) ﻭاﻟﺪاﺭﻗﻄﻨﻲ (191) ﻭاﻟﺤﺎﻛﻢ (1/ 358 - 386)


Kabbara ta biyu 

*2-Sannan yayi kabbara ta biyu,sai yayi Salati ga Annabi Muhammad ﷺ ,satul Ibrahimiyyah*. 

@ﺃﺧﺮﺟﻪ اﻟﺸﺎﻓﻌﻲ ﻓﻲ " اﻻﻡ (1/ 239 - 240) ﻭﻣﻦ ﻃﺮﻳﻘﻪ اﻟﺒﻴﻬﻘﻲ (4/ 39) ﻭاﺑﻦ اﻟﺠﺎﺭﻭﺩ (265) .

Wato shine:

‏«ﺍﻟﻠﻬﻢَّ ﺻﻞِّ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤَّﺪ، ﻛﻤﺎ ﺻﻠﻴﺖَ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؛ ﺇﻧَّﻚ ﺣﻤﻴﺪٌ ﻣﺠﻴﺪ . ﺍﻟﻠﻬﻢَّ ﺑﺎﺭِﻙ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤَّﺪ، ﻛﻤﺎ ﺑﺎﺭﻛﺖَ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؛ ﺇﻧَّﻚ ﺣﻤﻴﺪٌ ﻣﺠﻴﺪ »

*Allahumma salli 'ala Muhammad,wa-'ala ali Muhammad,kama sallayta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed, allahumma barik 'ala  Muhammad,wa-'ala ali Muhammad,kama barakta 'ala Ibraheema wa-'ala ali Ibraheem, innaka Hameedun Majeed*. 


Kabbara ta Ukku 

*3-Sannan sai kayi kabbara ta Ukku,Bayan kabbara ta ukku kuma sai kayi addua ga mamacin ka kyautata yimasa addua da jumawa kana yin addua agareshi*

@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩاﻭﺩ (2/ 68) ﻭاﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ (1/ 456) ﻭاﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺤﻪ " ﻭ (754 - ﻣﻮاﺭﺩ) ﻭاﻟﺒﻴﻬﻘﻲ (4/ 40) ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺚ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻭﺻﺮﺡ اﺑﻦ اﺳﺤﺎﻕ ﺑﺎﻟﺘﺤﺪﻳﺚ ﻋﻨﺪ اﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ.


Ga misalin wasu daga cikin Adduar Manzon Allah ﷺ yayiwa mamaci-

(اﻟﻠﻬﻢ اﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﻭاﺭﺣﻤﻪ، ﻭﻋﺎﻓﻪ ﻭاﻋﻒ ﻋﻨﻪ، ﻭﺃﻛﺮﻡ ﻧﺰﻟﻪ، ﻭﻭﺳﻊ ﻣﺪﺧﻠﻪ، ﻭاﻏﺴﻠﻪ ﺑﺎﻟﻤﺎء ﻭاﻟﺜﻠﺞ ﻭاﻟﺒﺮﺩ، ﻭﻧﻘﻪ ﻣﻦ اﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻛﻤﺎ ﻧﻘﻴﺖ ﻛﻤﺎ ﻳﻨﻘﻲ اﻟﺜﻮﺏ اﻻﺑﻴﺾ ﻣﻦ اﻟﺪﻧﺲ، ﻭﺃﺑﺪﻟﻪ ﺩاﺭا ﺧﻴﺮا ﻣﻦ ﺩاﺭﻩ، ﻭﺃﻫﻼ ﺧﻴﺮا ﻣﻦ ﺃﻫﻠﻪ، ﻭﺯﻭﺟﺎ ﺧﻴﺮا ﻣﻦ ﺯﻭﺟﻪ، ﻭﺃﺩﺧﻠﻪ اﻟﺠﻨﺔ، ﻭﺃﻋﺬﻩ ﻣﻦ ﻋﺬاﺏ اﻟﻘﺒﺮ، ﻭﻣﻦ ﻋﺬاﺏ اﻟﻨﺎﺭ) 

@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ (3/ 59 - 60) ﻭاﻟﻨﺴﺎﺋﻲ (1/ 271) ﻭاﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ (1/ 4256) ﻭاﺑﻦ اﻟﺠﺎﺭﻭﺩ (264 - 265) ﻭاﻟﺒﻴﻬﻘﻲ (4/ 40) ﻭاﻟﻄﻴﺎﻟﺴﻲ (999) ﻭﺃﺣﻤﺪ (6/ 23 ﻭ 28) ﻭاﻟﺴﻴﺎﻕ ﻟﻤﺴﻠﻢ،


(اﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻪ ﻋﺒﺪﻙ ﻭاﺑﻦ ﻋﺒﺪﻙ ﻭاﺑﻦ ﺃﻣﺘﻚ:ﻛﺎﻥ ﻳﺸﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺃﻻ ﺃﻧﺖ، ﻭﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪا ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺭﺳﻮﻟﻚ، ﻭﺃﻧﺖ ﺃﻋﻠﻢ ﺑﻪ،اﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﺤﺴﻨﺎ ﻓﺰﺩ ﻓﻲ ﺣﺴﻨﺎﺗﻪ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﺴﻴﺌﺎ ﻓﺘﺠﺎﻭﺯ ﻋﻦ ﺳﻴﺌﺎﺗﻪ، اﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﺗﺤﺮﻣﻨﺎ ﺃﺟﺮﺓ، ﻭﻻ ﺗﻔﺘﻨﺎ ﺑﻌﺪﻩ) 

@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺎﻟﻚ (1 - 227) ﻭﻋﻨﻪ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ اﻟﺤﺴﻦ (164 - 165) 


Kabbara ta Hudu 

*4-Sannan kayi kabbara ta hudu,bayan kayi kabbara ta hudu sai ka sakeyiwa mamaci addua ko kayiwa sauran muslmai addua.sannan kayi sallama*


Allah ne mafi sani.


NB

Ana daga hannune kadai sau daya ne a cikin sallar gawa, wato lokacin kabbarar Harama,sannan sai mutum ya dora hannunsa na dama akan na hagu abisa kirjinsa.

@Tirmizy da Darul Qadhny da Baihaqy


Mafi yawan mutane munayin asarar rashin sallar ga mamatan mu,yana da kyau a sami jama'a masu yawa sun sallace gawa saboda samun gafarar ga mamacin.


Annabi ﷺ yana cewa:

(Idan aka sami mutane arba'in wadanda basu shirka suka sallaci gawa suna neman citonaa awajan Allah,face Allah ya basu cetonsa).

@Duba littafin Ahkamul Jana'iz na Sheikhu Albany.


Allah ka bamu ikon yawaita yin sallah ga mamatan mu kuma kayi rahama da gafara a garesu baki daya.

Continue reading...

DUK CINIKAYYAR DA ZA'A YANKE RIBA KAFIN A FARA, BATACCIYYA CE !

*DUK CINIKAYYAR DA ZA'A YANKE RIBA KAFIN A FARA, BATACCIYYA CE !*

*Tambaya*

Assalamu alaikum.

Malam akwai wani cinikayya na hadin-guiwa da ake yi a DANTATA SUCCESS AND PROFITABLE COMPANY, ga yadda abin yake:

1- Zaki sa kudin ki tsawon wata shida ana biyanki duk wata, Zaki sami 40 percent (kaso arbain cikin Dari) duk wata tsawon wata shida. Misali in kin sa *N300,000* duk wata Zaki sami *N120,000* tsawon wata 6, Uwar kudin ki da riba Zaki sami *N720,000*

2- tsari Na Biyu Zaki sa kudin ki tsawon shekara Zaki dinga karbar 25 percent (kaso 25 cikin Dari Na abinda kikasa) . misali kinsa *N300,000* duk wata Zaki dinga karbar *N75,000* har tsawon wata goma sha biyu, gaba daya Uwar kudi da riba Zaki sami *N900,000*

Idan kin zabi biya daya Ne in kudin ki suka shekara zaa biyaki *N 960,000

Don Allah malam muna so a taimaka mana da hukuncin sharia game da wannan tsari, saboda mutane da yawa suna shiga ?

*Amsa*

Wa alaikum assalam

Irin wannan ciniki shi ake cewa (Mudharaba) ko kuma (Kiradh)a wajan Malikiyya, wato mutum ya bada kudi wani ya juya masa.

Saidai Wannan sigar da aka yi bayani batacciya ce kuma haramtacciya a wajan malaman musulunci saboda ta kunshi zalunci da kuma rashin tabbas wato (Garar), da yiwuwar cutar da daya daga cikin abokan tarayya, saboda an sanya ribar ne ta Uwar-kudi ba daga ribar da za'a samu ba.

Duk lokacin da aka shardanta riba daga cikin Uwar kudi za'a cutar da daya daga cikin abokan tarayya a ciniki saboda ribar in ta yi yawa an zalunci mai uwar kudin, idan kuma ribar ta karanta an zalunci mai juya kudin, Ibnu Taimiyya a cikin Majmu'ul fatawa (28/83) ya nakalto Ijma'in Malamai akan haramcin duk Mudharabar da ta kunshi shardanta riba daga Uwar kudi.

Ingantaccen hadin guiwa a wannan tsarin shi ne wanda za'a cimma daidaito wajan bada wani sashe na daga abin da aka samu na riba, ba daga Uwar kudi ba.

Duk wanda ya ji tsoran Allah, tabbas zai azurta shi ta inda ba ya zato kamar yadda Allah ya fada a suratu Addalak aya ta:( 3)

Don neman karin bayani duba Al-mugni (5/28) da kuma Almausu'a Alfiqhiyya (8/116).

Allah ne mafi sani

*Amsawa*

*DR.JAMILU YUSUF ZAREWA*


Continue reading...

YADDA MUSULMI ZAI YI TA'AMULI DA BUKIN KIRSIMETI - Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

YADDA MUSULMI ZAI YI TA'AMULI DA BUKIN KIRSIMETI:


✅ Rubutawar:

Dr. Ibrahim Jalo Jalingo


Da yake a Nigeria ana zaman cakuda ne tsakanin al'ummar Kirista da al'ummar Musulmi. Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya shafi rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi, ko ta hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da iimaai. Sannan da yake akwai karkatattu  da dama da suke halatta abin da Shari'ah ba ta halatta ba, ko haramta abin da Shari'ah ba ta haramta ba, lalle ya dace a yi wa al'ummar Musulmi bayanin hukuncin abin da ya shafi wannan Idi na Kirsimeti ta bangarorinsa da ke iya shafar wasu al'ummar Musulmi.


To amma kafin mu shiga bayanin wadannan hukunce-hukunce ya kamata Musulmi su san abubuwa kamar haka:-

1. Shi dai bukin kirsimeti wata bidi'ah ce da bata da Kiristoci suka kirkira sannan suka maida ita wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta kamar dai yadda wasu Musulmi suka kirkiri bidi'ar idin Maulidi, Kiristoci sun kirkiri wannan bidi'ar ce kuwa a shekarar Miladiyyah ta 360, watau a cikin karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis salam.


2. Ya kamata kowa ya san cewa ba ya halatta Musulmi ya yi tarayya da wadanda ba musulmi ba cikin bukukuwansu na idi, watau ta hanyar halartan wasu tarurruka da za su kira, ko ta hanyar ba su wani taimako domin karfafa idodin nasu, wannan dai shi ne hanyar Salafus Salih: Sahabbai, da Taabi'ai, da Taabi'uttaabi'in; dalili kuwa shi ne:-

Imamul Baihaqiy ya ruwaito cikin As-Sunanul Kubraa hadithi na 19,334 cewa Sayyidina Umar Dan Khattab Allah Ya kara masa yarda ya ce: ((اجتنبوا اعداء الله في عيدهم)). Ma'ana: ((Ku nisanci makiya Allah cikin idinsu)). 

Sannan Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah ya ce -kamar yadda ya zo cikin Al-Mustadrak Alaa Fataawaa Ibnu Tamiyyah 1/108, da Mukhtasarul Fataawaa Misriyyah1/517 :-

((وليس للمسلمين ان يعينوهم على أعيادهم لا ببيع ما يستعينون به على عيدهم ولا باجارة دوابهم ليركبوها في عيدهم لان أعيادهم مما حرمه الله تعالى ورسوله صلى الله عليه وسلم لما فيها من الكفر والفسوق والعصيان)). انتهى.

Ma'ana: ((Musulmi ba su da damar su taimaka musu cikin idodinsu, ko  dai ta hanyar sayar musu da abin da za su karfafu da shi, ko ta hanyar ba da hayar dabbobinsu domin su hau su cikin idinsu, saboda idodinsu na daga cikin abin da Allah Madaukakin Sarki da kuma manzonSa mai tsira da amincin Allah suka haramta, saboda abin da yake cikinsu na kafirci da fasikanci da kuma sabo)). 


3. Babu wani wanda ya isa ya bugi kirji a duniyan nan ya ce: ga tabbatacciyar wata da rana da aka haifi Annabi Isa alaihis salam a cikinta, sai dai kowa ya fadi abin da yake zato kawai, wannan shi ya sa ma Kiristoci masu yin bukin ranar Kirsimeti watau ranar haifuwar Annabi Isa alaihis salam suka yi sabani dangane da ranar da za a yi wannan bukin zuwa mazhabobi biyu:-


Mazhabar farko: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 25 ga watan December, wannan ita ce mazhabar da Catholic, da Protestant, da kuma mafi yawan bangarorin Kiristoci ke bi.


Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 7 ga watan January, wannan ita ce mazhabar da bangarorin Orthodox ke bi.


4. Kiristoci kafurai ne kamar yadda Yahudawa da Majusawa da sauran masu bautar gumaka suke kafurai, babu sabani cikin wannan mas'ala cikin  shari'ar Musulunci.


5. Ya kamata a san cewa akwai wasu kafuran da Musulunci ya kebanta su da wasu hukunce-hukunce saboda tabbatar wa Musulmi wata maslaha, wadannan kuwa su ne: Yahudawa da Kiristoci, su wannan nau'i na kafurai Musulunci ya halatta wa Musulmi cin yankansu, da auren matansu, sabanin mabiya addinin majusu, ko mabiya addinin Hindu, ko mabiya addinin Budha, ko mabiya sauran addinai na bautan gumaka. 

Idan masu karatu sun fahimci wannan to sai mu shiga bayanin mas'alarmu da muke son yi wa jama'a bayaninta.


HUKUNCIN KARBAN KYAUTUTTUKAN KAFURAI A RANAR IDINSU:


Su kyaututtukan da kafurai -Ahlul kitabi ko wasun Ahlul kitabi- ke ba wa Musulmi a ranakun idinsu na kafurci da bidi'ah sun kasu kashi biyu ne:-


1. Kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ake bukatar yankawa, watau kamar irinsu: halawa, da tufafi, da kayan marmari da sauransu.


2. Kyaututtukan da suke nama ne da ke bukatar a yi masa yanka irin ta Shari'ah.


To shi na farkon, watau kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ke bukatar yanka irin ta Shari'ah, babu sabani tsakanin Salafus Salih -a dai iya saninmu- cikin halaccin karbarsu, saboda dalilai kamar haka:-


1- Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 18,644 daga Muhammad Dan Siiriin cewa:-

((أتي علي رضي الله بهدية النيروز، فقال: ما هذه؟ قالوا: يا امير المؤمنين هذا يوم النيروز. قال: فاصنعوا كل يوم فيروز)) .

Ma'ana: ((An zo wa Sayyidina Aliyyu Dan Abii Taa'lib Allah Ya kara masa yarda da kyautar (idin) Nairuuz, sai ya ce: mene ne wannan? Sai suka ce: Ya Amirar Muu'miniin! Wannan ranar Nairuuz ce. Sai ya ce: (in haka abin yake) ku rika yin Fairuuz a ko wace rana)). 


2- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito cikin Musannaf athari na 24,371, da Imam Ishaq Ibnu Raa'huyyah cikin Musnad athari na 1,606 daga Qaa'bus Dan Zibyaan daga shi mahaifin nasa cewa wata mace ta tambayi Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:-

((ان لنا اكارا من المجوس وانه يكون لهم العيد فيهدون لنا، فقالت: اما ما ذبح لذلك اليوم فلا تأكلوا ولكن كلوا من أشجارهم)) 

Ma'ana: ((Muna da 'yan kodago daga cikin Majusawa, sannan kuma suna da ranar idin da suke aika mana da kyaututtuka. Sai ta ce: Amma abin da aka yanka saboda wannan ranar to kada ku ci, to amma ku ci daga 'ya'yan itatuwansu)). 


3- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito a cikin Musannaf athari na 24,372 daga Abuu Barzah cewa:-

((كان له سكان مجوس فكانوا يهدون له في النيروز والمهرجان فكان يقول لأهله: ما كان من فاكهة فكلوا وما كان من غير ذلك فردوه)).

Ma'ana: ((Yana da wasu mazauna Majusawa, kuma sun kasance suna aika masa da kyautuka a lokacin Nairuuz da Mihrajan, sannan ya kasance yana gaya wa iyalansa cewa: Kyautar da ta kasance ta kayan marmari ne to ku ci, wacce kuma ta kasance ba hakan ba, to ku mayar da ita)). 


Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi taliki a kan wadannan hujjojin a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqiim 2/554-555 ya ce:-

((فهذا يدل على انه لا تأثير للعيد في المنع من قبول هديتهم، بل حكمها في العيد وغيره سواء؛ لانه ليس في ذلك إعانة لهم على شعائر كفرهم)). 

Ma'ana: ((Wannan duka yana nuni ne a kan cewa: Idi ba yi da wani tasiri a kan hana karban kyautarsu, a'a hukuncin karban kyautarsu ba yi da wani bambanci tsakanin lokacin Idi da kuma lokacin da ba na Idi ba, saboda babu wani abu na taimakon addininsu a cikin karban kyautarsu)). 


TALIKI:

Da wannan ne za mu fahimci cewa: Maluman Musulunci sun hana cin yankan da Majusawa suka yi domin bukukuwan idinsu, to amma fa ba wai sun hana cin yankan ba ne saboda kasancewarsa yankan da aka yi domin bukin idin kafurai ba, a'a an hana cin yankan ne saboda kasancewarsa yankan Majusawan da ba sa cikin mutanen nan ne da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci, dukkan kuma kafurin da ba ya cikin abin da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci to ba a cin yankansa.


HUKUNCIN CIN NAMAN DABBAR DA YAHUDAWA KO KIRISTOCI SUKA YANKA DA HANNAYENSU SABODA YIN BUKUKUWAN IDINSU:


Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi bayani game da cin abin da Yahudawa ko Kiristoci suka yanka saboda bukukuwan idinsu, a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/555,558 ya ce:-

((وانما يجوز ان يؤكل من طعام اهل الكتاب في عيدهم بابتياع او هدية او غير ذلك مما لم يذبحوه للعيد. فأما ذبح المجوس فالحكم فيها معلوم فإنها حرام عند العامة. وأما ما ذبحه اهل الكتاب لاعيادهم وما يتقربون بذبحه الى غير الله نظير ما يذبح المسلمون من هداياهم وضحاياهم متقربين بها الى الله تعالى، وذلك مثل ما يذبحون للمسيح والزهرة، فعن احمد روايتان: اشهرهما في نصوصه: انه لا يباح اكله وان لم يسم غير الله تعالى. ونقل النهي عن ذلك عن عائشة وعبد الله بن عمر.....والرواية الثانية ان ذلك مكروه غير محرم))انتهى

Ma'ana: (Cin abincin Ahlul Kitabi a lokacin idinsu ga abin da dama ba su yanka shi saboda Idi ba, yana halatta ne ta hanyar saye da kudi, ko kuwa kyauta, ko wanin haka. Amma abin da Majusawa suka yanka hukuncinsa sananne ne, watau haramun ne a wurin dukkan malamai, to amma abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda idinsu, da kuma abin da suke yin ibada ta hanyar yanka shi ga wanin Allah' kamar abin da suke yankawa saboda Almasihu, da Zahrah, irin dai abin da Musulmi suke yankawa na Hadaya, da Layya, domin neman kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad yana da fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta a ci shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a kansa ba. An nakalto hana cin wannan yankan ma daga Nana A'isha, da Abdullahi Dan Umar.. Fatawa ta biyu ita ce: Cin wannan yankan makruuhi ne ba haramun ba. Wannan ita ce mazhabar Malikiyyah, Imam Malik ya kyamaci cin abin da Ahlul Kitabi suka yanka saboda Coci-Cocinsu, ko saboda idinsu amma ba tare da ya haramta hakan ba)). 


Sannan har yanzu Sahikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/559 :-

((ونقلت الرخصة في ذبائح الأعياد ونحوها عن طائفة من الصحابة رضي الله عنهم، وهذا فيما اذا لم يسموا غير الله، فان سموا غير الله في عيدهم او غير عيدهم حرم في اشهر الروايتين، وهو مذهب الجمهور، وهو مذهب الفقهاء الثلاثة فيما نقله غير واحد، وهو قول علي بن ابي طالب وغيره من الصحابة، وهو قول اكثر فقهاء الشام وغيرهم. والثانية: لا يحرم وان سموا غير الله، وهذا قول عطاء ومجاهد ومكحول والاوزاعي والليث)).

Ma'ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-yanken idodin (Yahudawa da Kiristoci) da makamantansu (su yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai Allah Ya kara musu yarda amma fa wannan sai idan ba su ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in kuma har sun ambaci wanin Allah a lokacin yankan to cin sa ya haramta a cikin fatawa mafi shahara daga cikin fatawowi biyu da Imam Ahmada yake da su a cikin mas'alar, wannan kuwa shi ne mazhabar jumhur, kuma shi ne mazhabar Fuqaha'un nan guda uku, kamar yadda mutane da yawa suka ruwaito, kuma shi ne maganar Aliyyu Dan zabii Taa'lib da waninsa a cikin Sahabbai, daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa, da Abu Umamah, da Irbadh Dan Saa'riyah, da Ubaa'dah Dan Saa'mit, kuma shi ne maganar maluman Sham da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta biyu ita ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne koda kuwa sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin yankan, wannan kuwa shi ne maganar Ataa'u, da Mujaa'hid, da Makhuul, da Auzaa'ii, da kuma Laith)).


Taliki na farko:-

Za mu fahimta daga maganganun malaman da suka gabata cewa: Abin da Yahudawa da Kiristoci suke yankawa saboda bukukuwan idinsu yana kasuwa ne zuwa kashi biyu:-


Na farko: Abin da suka ambaci sunan Allah yayin yanka shi.

Na biyu: Abin da suka ambaci sunan wanin Allah yayin yanka shi.


To ita dabbar da aka ambaci sunan Allah lokacin yanka ta, Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cin ta.


Mazhabar farko: Sahabbai da yawa sun ba da damar cin wannan nama. Maluman Malikiyyah, da Imam Ahmad cikin ruwayah sun halattar da cinsa amma tare da nuna kyama.


Mazhaba ta biyu: Nana A'isha, da Abdullahi Dan Umar, da kuma Maluman Hanaa'bilah sun ce cin wannan nama haramun ne.


Sannan ita kuma dabbar da aka ambaci sunan wanin Allah lokacin yanka ta, watau kamar wacce aka ambaci sunan Yesu Almasihu lokacin yanka ta, wannan ma Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cin wannan dabbar:-


Mazhabar farko: Cin wannan dabba bai halatta ba, wannan shi ne abin da Aliyyu Dan Abii Taa'lib, da Abud Dardaa'i, da Abuu Umamah, da Irbadh Da Saa'riyah, da Ubaa'dah Dan Saa'mit, da Hanafiyyah, da Malikiyyah, da Shafi'iyyah, da Hanaa'bilah, da mafi yawan maluman kasar Sham, suk fada.


mazhaba ta biyu: Cin wannan dabba halal ne, wannan shi ne abin da Ataa'u, da Mhjaa'hid, da Makhul, da Auzaa'ii, da Laithu Dan Sa'ad, da kuma Imam Ahmad cikin ruwaya suka fada.


Taliki na biyu:-

Za mu iya fahimta daga maganganun da suka gabata cewa: Naman kasuwa da Musulmi ke yankawa da hannayensu idan Kiristoci suka saya suka dafa a matsayin abincin Kirsimeti, to wannan abincin halal yake ga dukkan wanda suka ba da shi gare shi. Wallahu A'alam.


HUKUNCIN CIN YANKAN KIRISTOCI DA YAHUDAWA A MAZHABAR MALIKIYYAH:

A karshen wannan makala tamu za mu yi bayanin mene ne mash'hurin mazhabar Malikiyyah game cin yankan Kiristoci da Yahudawa, saboda Musulmin wannan kasa tamu Nigeria su kara fahimtar irin banbancin da yake tsakanin abin da ke rubuce cikin littattafan Mazhabar Malkiyyah, da kuma abin da wasu jahilan 'yan bidi'ah da suke ikirarin cewa su masu bin Mazhabar Malikiyyah ne, alhali kuwa hayaniyarsu kawai suke yi, son zuciyarsu ne kawai suke bi, duk abin da jahilan shaihunansu suka ce to shi ne addini a wurinsu. Allah ya tsare mu da sharrin Shaidan.

Babban malamin Malikyyah Imamul Qurtubii ya ce cikin littafinsa Aljaami'u Li Ahkaamil Qur'an 6/53:-

((وقال جمهور الامة ان ذبيحة كل نصراني حلال سواء من بني تغلب او غيرهم، وكذلك اليهود)).

Ma'ana: ((Jumhuurin Al'ummah sun ce: Lalle yankan ko wane kirista halal ne, babu banbanci daga kabilar Taglib ne ko daga wasunsu, haka nan su ma Yahudawa)). Intaha.

Khalil Dan Ishaq ya ce cikin Mukhtasar Khalil shafi na 90 

((وان سامريا او مجوسيا تنصر وذبح لنفسه مستحله، وان اكل الميتة ان لم يغب)) 

Ma'an: ((koda ya kasance wani basaamire ne, ko bamajuse ne da yazama kirista ya yanka abin da yake halal a gare shi saboda kuma kan shi, koda kuwa yana halatta cin mushe ne, matukar dai musulmi na sane da cewa shi din ne ya yi yankan)).

Sannan ya zo cikin littafin As'halul Madaarik 2/92:-

((يجوز للمسلم نكاح حرائر اهل الكتاب .. وكان الصحابة بتزوجون من اليهود والنصارى كثيرا زمن الفتح .. ونكح عثمان نصرانية، ونكح طلحة يهودية)).

Ma'ana: ((yana halatta ga musulmi auren 'yantattun matan Ahlul Kitaabi.. Sahabbai sun kasance da yawa suna auren matan Yahudawa da Kiristoci a lokacin da ake cin kasashe da yaki.. Sayyidina Uthman ya auri wata kirista, Sayyidina Talhah ya auri wata bayahudiya)). Allah muke roko da Ya taimake mu. Ameen.

Continue reading...

ILLOLI GUDA SHIDA NA SABAWA MAHAIFA ISL

ILLOLI GUDA SHIDA NA SABAWA MAHAIFA 


Hakika Annabi SAW ya yi mana umarni kamar yadda Allah da kansa yayi mana umarnin akan yin biyayya da kuma kyautata mahaifa,da kuma hani akan sabawa masu da kuma cutar dasu,sabawa mahaifa da rashin kyautata masu yana cikin mafi girma zunubai da akewa yiwa Allah anan duniya. 


Annabi SAW ya baiyana mana illa da  girman laifin mai sabawa Mahaifansa, ga kadan daga cikin su:-


*1-Mai Cutar da mahaifansa Tsinanne ne inji Manzon Allah SAW*. 


Daga Abu Hurairaita R.A yana cewa :-

"Annabi s.a.w yana cewa:-

*(La'antacce ne mai cutar da mahaifansa ko mai sabawa  mahaifansa)*

@ﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﻓﻲ" ﺍﻷﻭﺳﻂ

" ‏( 8497 ‏)

@ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ " ‏( 2420 ‏)



*2-Allah bawa kallon mai sabawa Mahaifansa a ranar alqiyama*. 


Daga Ibn Umar R.A yana cewa:-

 " Manzon Allah s.a.w yace:

(Mutane guda ukku Allah bazai kallesu ba a ranar alqiyama:-

*Mai sabawa mahaifansa*

*Wanda baya kishin iyalinsa

...............)*.

@ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ‏( 2562 ‏)

 @ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ

ﺳﻨﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ 



*3-Mai sabwa mahaifa baya shiga aljanna*. 


Daga Ibn Umar R.A yana cewa:-

 " Manzon Allah s.a.w yace:

(..............Mutane guda ukku bazasu shiga aljanna ba a gobe alqiyama:-

*Mai sabawa mahaifansa*

*Mai kwankwadar giya*

*Mai yin gorin abinda ya bada)*. 

@ﻭﺭﻭﻯ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ‏( 2562 ‏)

@ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ

ﺳﻨﻦ ﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ " .


*4-Babu mai shiga aljanna sai wanda kasance yana biyayya ga mahaifansa kuma baya saba masu*. 


Wani mutum yazo wajan Annabi s.a.w sai yace Ya Manzon Allah s.a.w:

"Na shaida babu abin bautawa bisa hakki da gaskiya sao Allah kuma kai Manzon Allah ne, kuma nayi salloli biyar na farilla,kuma na bada zakka kuma nayi azumin watan Ramada?? Sai Annabi s.a.w ya ce:

*(Wanda ya mutum akan haka yana tare da Annabawa da Shahidai Siddiqai a ranar alqiyama matuqar bai sabawa Mahaifansa ba)*

@ﻭﺭﻭﻯ ﺃﺣﻤﺪ ‏(24299 ‏)

@ﻭﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ " ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ " ‏( 2515 ‏)


*5-Allah baya karbar aiyuka na mai sabawa mahaifansa inji Manzon Allah s.a.w*. 


Daga Abi Umamah R.A yana cewa:

Manzon Allah s.a.w yace:

(Mutanan guda ukku Allah baya karbar aiyukan su na farilla da na nafila:-

*Mai sabawa Mahaifansa*

*Mai gorin abinda ya bayar*

*Wanda yake karyata Qaddara)*.

@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﻋﺎﺻﻢ ﻓﻲ "

ﺍﻟﺴﻨﺔ " ‏( 323 ‏) 

@ﺳﻠﺴﻠﺔ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ " ‏( 1785 ‏) ،


*6-Sabawa mahaifa yana cikin mafi giraman zunubai inji Annabi s.a.w*. 


(ﺃﻻ ﺃﻧﺒﺌﻜﻢ ﺑﺄﻛﺒﺮ ﺍﻟﻜﺒﺎﺋﺮ ؟ ﻗﻠﻨﺎ : ﺑﻠﻰ ﻳﺎ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ؟ ﻗﺎﻝ : ﺍﻹﺷﺮﺍﻙ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻭﻋﻘﻮﻕ ﺍﻟﻮﺍﻟﺪﻳﻦ . ﻭﻛﺎﻥ ﻣﺘﻜﺌﺎً ﻓﺠﻠﺲ ، ﻭﻗﺎﻝ : ﺃﻻ ﻭﻗﻮﻝ ﺍﻟﺰﻭﺭ. ﺃﻻ ﻭﺷﻬﺎﺩﺓ ﺍﻟﺰﻭﺭ ‏) ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻰ ﺻﺤﺘﻪ.


Allah ka nisantar da mu daga aikata abinda zai sanya mu sabawa Mahaifanmu.Allah ka jikansu kamar yadda suka kulamu lokacin muna yara.



*Allah ka gafarta ma mahaifan mu baki daya*.

Continue reading...

MAFI SOYUWAR MUTANE AWAJAN ALLAH DA MAFI SOYUWAR AIKI A WAJAN ALLAH

MAFI SOYUWAR MUTANE  AWAJAN ALLAH DA MAFI SOYUWAR AIKI A WAJAN ALLAH


Daga Ibn Umar رضي الله عنهما yana cewa,wani mutum yazo wajan Annabi ﷺ,sai Yace;-

"Ya Manzon Allah;-


*Acikin mutane wanene mafi soyuwa a wajan Allah??*.

Kuma acikin aiyuka;-

*Wani aikine yafi soyuwar aikin awajan Allah??*


Sai Manzon Allah ﷺ yace;-

*(Mafi soyuwar mutane a wajan Allah,shine wanda yafi amfanar da mutane,ko wanda mutane sukafi amfanu da shi,kuma mafi soyuwar aiki a wajan Allah*


*-Farin ciki da zaka sanya azuciyar musulmi*


*-Ko kuma ka yaye masa bakin ciki ko wata damuwa*


*-Ko ka biya masa bashi*


*-Ko magance masa yinwa dake damunsa*


*Wallahi nayi tafiya tare da dan uwana cikin baya masa buqatarsa,shi yafi soyuwa a gareni fiye da nayi i'itikafi a Masallaci na tsawon wata guda,kuma dukkan wanda ya kame daga fishinsa,to Allah zai rufa masa al'aurarsa "wato zai rufa masa asirinsa"*


*Duk wanda ya hadiye fishinsa kuma ina da ikon daukar mataki,Allah zai cika masa zuciyarsa farin ciki a ranar alqiyama*


*Dukkan wanda yayi tafiya cikin buqatar dan uwansa har buqatarsa ta biya,to Allah zai tabbatar da dugadiginsa a ranar da dugadigi suke zamewa*


*Kuma lallai munanan halaye suka bata aiyuka,kamar yanda Khallu yake bata zuma)*

@صححه الألباني في

 السلسلة الصحيحة - رقم : (906)


ابن رجب الحنبلي رحمه الله:

Yana cewa;-

"A jumlace wannan Hadisin yana tabbar mana mafi alkhairi aciki mutane,shine wanda yafi amfanar mutane,da wanda yafi hakuri acikin cutarwar da mutane sukeyi masa,kamar yanda Allah ya siffanta bayinsa masu Taqwa da fadarsa":-

*﴿الَّذِينَ يُنْفِقُونَ فِي السَّرَّاءِ وَالضَّرَّاءِ وَالْكَاظِمِينَ الْغَيْظَ وَالْعَافِينَ عَنِ النَّاسِ وَاللَّهُ يُحِبُّ الْمُحْسِنِينَ﴾*

@لطائف المعارف:(٢٣١)


الحسن البصري رحمه الله:

Yana cewa;-

"Wallahi na biyawa musulmi wata buqatarsa shi yafi soyuwa a gareni fiye da nayi sallah raka'a dubu ta nafila".

@قضاء الحوائج:(٤٨)


Allah ne mafi sani.


hakika akwai samun matsayi da lada mai tarin yawa cikin taimakon dan uwanka musulmi cikin biya masa buqatarsa da kuma amfanar da mutane da janyo masu wani abu mai amfanar da su.


Manzon Allah ﷺ yafi kowa janyoma al'umma amfani da alkhairi sannan Sahabban yardaddun Allah.


Allah ya bamu ikon koyi da su baki daya.

Continue reading...

MAGANI DAGA MANZON ALLAH ﷺ

MAGANI DAGA MANZON ALLAH ﷺ


Yana cikin sunnar Manzon Allah ﷺ neman waraka daga cutuka ta hanya guda ukku;-


1-Hanyar farko

*"Dogaro ga Allah tare da yin Addu'ar neman waraka wadda ta kun shi ayoyin Alqurani mai girma kamar suratul Fatiha ko falaqi da Nasi ko Qulhawa,ko kuma addu'oin neman waraka wanda suka tabbata a sunnar Manzon Allah ﷺ"*


2-Hanya ta biyu;

*"Dogaro ga Allah tare da shan maganin wanda Manzon Allah ﷺ yayi bayanin yana warkar da cuta kaza,kamar shan zuma dan maganin matsalar ciki,ko wani magani da angwada yana maganin cuta"*


Misali:

"Manzon Allah ﷺ yana cewa:

*(Ina uwarninku da shan Nonan saniya,domin nonanta maganine,da kuma kitsenta shima warakane,kuma ku nisanci cin namanta,domin a cikin namanta akwai cuta)*

@الألباني رحمه الله صحيح الجامع الصفحة أو الرقم: 4061


3-Hanya ta Ukku

*"Dogaro ga Allah sannan da aikata wani Ibada wanda sanadiyyarta manzom Allah ﷺ yace ana samun waraqa saboda aikatawa kamar yin sadaka ko gina rijiya"*


Allah ne mafi sani


Allah ka baima dukkan marar sa lafiya daga cikin musulmai lafiya amin.

Continue reading...

SUNNONIN MANZON ALLAH ﷺ GUDA BIYAR-5 LOKACIN TASHI DAGA BARCI

*SUNNONIN MANZON ALLAH ﷺ GUDA BIYAR-5 LOKACIN TASHI DAGA BARCI*


*1-Farawa da Ambaton Allah*


Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya tashi daga barci yana cewa;-

*(ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﺣﻴﺎﻧﺎ ﺑﻌﺪ ﻣﺎ ﺃﻣﺎﺗﻨﺎ، ﻭﺇﻟﻴﻪ ﺍﻟﻨﺸﻮﺭ*


"ALHAMDU LILLAHIL LAZI AHYANA BA'ADA MAA A MATANA A ILAIKAL NUSHUR"


Manzon Allah ﷺ yana cewa;-

*(Dukkan wanda ya farka cikin dare sai yace:-*

" ﻻ ﺍﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ، ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ،ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﺊ ٍﻗﺪﻳﺮ . ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ،ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ،ﻭﻻ ﺍﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ،ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ ﻭﻻ ﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ"

*La ilaha illal-lahu wahdahu la shareeka lah,lahul-mulku walahul-hamd,wahuwa ala kulli shay-in kadeer, subhanal-lah,walhamdu lillah,wala  ilaha illal-lah wallahu akbar,wala hawla wala kuwwata illa billahil-aliyyil azeem*Rabbi ghfir li*


Sannan yace;

" ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ "

*(Ko yayi addu'a,za'a amsa masa addu'a,kuma idan yayi alwala yayi Sallah an karbin Sallarsa)*

@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 1154 )


*2-Farawa da yin Aswakin bayan ambaton Allah*.


Manzon Allah ﷺ ya kasance,baya barci face Aswakinsa yana tare da shi,idan ya tashi daga barci sai ya fara da yin Aswaki.

@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻟﻮﺍﺩﻋﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﺤﻴﺢ ﺍﻟﻤﺴﻨﺪ - ﺭﻗﻢ : ‏( 775 ).


*3-Goge alamar barci daga idonsa da hannunsa*.


Acikin wani Hadisi mai tsawo Daga Ibn Abbas ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻬُﻤَﺎ yace;-

*"... Sai Manzon Allah ﷺ ya tashi daga barci,sai ya zauna yana goge alamar barci daga fuskarsa"*

@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ - ﺭﻗﻢ : ‏( 4572 ).


*4-Wanke hannu sau ukku*


Daga Abi Hurairata ﺭَﺿِﻲَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻨْﻪُ ,Lallai Manzon Allah ﷺ yace;-

*(Idan dayanku ya tashi daga barcinsa, Kada ya sanya hannunsa acikin mazubi,har sai ya wanke hannunsa sau ukku,domin shi bai san inda hannunsa ya kwana ba)*

️@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ - ﺭﻗﻢ : ‏( 278 ‏)


*5-Shaqa ruwa da facewa sau ukku*


Manzon Allah ﷺ yana cewa;-

*(Idan dayan ku ya tashi daga barci,to ya shaqa ruwa ya face sau Ukku,domin Shaidan yana barci acikin hanncinsa)*

@ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ - ﺭﻗﻢ:( 238 )


     Allah ne mafi sani


*Allah ka bamu ikon koyi da Manzon Allah ﷺ a dukkan rayuwa baki daya*.

Continue reading...

SHIN JA'AFAR ASSADIQ DAN SHI'A NE?

*_SHIN JA'AFAR ASSADIQ DAN SHI'A NE?_*

*Tambaya*

Assalamu alaikum Don Allah malam wai Imamussadiq dan shi'a ne, kuma ba zan dau wani abu daga iliminsa, wanda nake da tabbacin gaskiya ne, na yi amfani da shi ba, dan yana dan shi'a?

*Amsa*

Wa'alaikum assalam To 'yar'uwa Ja'afar Assadiq ba shi da alaka da shi'a, yana cikin Ahlul-baiti, ya barranta kansa daga ayyukan shi'a a wurare da dama, ga abin da yake cewa akan mutu'a, "Ba wanda yake aikata mutu'a a cikinmu sai fajirai" duba biharul anwar shafi na 318 saidai yana daga cikin limaman shi'a guda goma sha biyu, wadanda suke riyawa, duk a cikin limaman guda goma sha biyu, babu wanda suka yiwa karya kuma suka kirkiri hadisai suka danganta masa kamar shi, wannan yasa sai manyan manazarta ne za su iya gano hadisan gaskiya daga na karya a cikin littattafan shi'a wadanda suke dangantawa wannan babban malami kuma jinin anabta, kuma hatta malaman shi'a sun tabbatar da hakan a maganganunsu, kamar yadda ahlussunnah suka tabbatar, ga wasu daga cikin bayanai akan haka:

*1.* Kisshi ya rawaito hadisi daga Yunus yana cewa: Na je Irak sai naga sahabban Ja'afar Assadiq sun taru, sai na ji hadisai daga wajansu bayan na gama ji sai na dauki littatafansu na je na nunawa Aliyu Arridha, (daya daga cikin Ahlul-baiti) sai ya musa da yawa daga cikin hadisan, ya ce ba zai yiwu ace Ja'afar assadiq ne ya fade su ba, sannan ya ce Abul-kaddab ya yiwa Ja'afar Assadiq karya, Allah ya tsinewa Abul-khaddab, kamar yadda ka gani haka almajiran Abul-khaddab suke shigar da karya a cikin littattafanmu, suna cewa Ja'afar Assadiq ne ya fada, don haka duk abin da suka gaya muku daga wajanmu kar ku amsa in har ba Qur'ani ba ne" Rijalu- Alkishhi 3\298.

*2.* Sannan Majlisi ya fada a cikin Bihar Al'anwar cewa "Abu-abdillah –wato Ja'afar Assadiq- yana cewa : Mutane sun zurfafa wajan yi mana karya" Bihar Al'anwar :2\246.

*3.* Ja'afar Assadiq yana cewa: "Allah ya jikan wanda ya sanyawa mutane son mu, bai yi abin da mutane za su ki mu ba, amma za ka ga daya daga cikinsu zai ji kalma daya a wajanmu, sai ka ji ya kara guda goma na karya" Al-kafy 8\192.

*WADANNAN DALILAI NE DAGA MANYAN LITTATTAFAN 'YAN SHIA WADANDA SUKE NUNA CEWA: 'YAN SHIA SUNA YIWA JA'AFAR ASSADIQ KARYA..*

Wannan yasa Ibnu Taimiyya yake cewa: "Babu wanda aka yiwa karya kamar Ja'afar Assadiq" Duba Minhaj assunnah 7\391

Saboda dalilan da suka gabata ina baki shawarar cewa kada ki dauki maganar da kika gani daga Ja'afar Assadiq a cikin littattafan shi'a ko kuma kananan littatafan Ahlussunah wadanda ake siyarwa a kasuwa, mutukar ba ki tabbatar da tabbatuwar malamin a ilimin sunna da sanin isnadi ba, saboda yawan karyar aka yi masa.

Allah ne mafi sani

12/12/2014

Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa

Continue reading...

MATSAYIN MALAMAI A CIKIN AL'UMMA

MATSAYIN MALAMAI A CIKIN AL'UMMA

Dr. Aliyu Muh'd Sani

Lallai kamar yadda kowa ya sani; Malamai suna da matsayi mai girma a cikin al'umma, su ne magada Annabawa, masana Addini, masu dauke da shi, kuma masu isar da shi da bayaninsa ga mutane, saboda haka wajibi ne mutane su so su, su girmama su, su jibince su, su taimake su a kan mabarnata masu kokarin rusa Addini da wasa da shi, da masu sukansu da aibanta su balle kuma zaginsu.

Allah Madaukaki ya ce:

{ ﻗُﻞْ ﻫَﻞْ ﻳَﺴْﺘَﻮِﻱ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻟَﺎ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ { ‏[ ﺍﻟﺰﻣﺮ : 9 ]

"Ka ce: Shin wadanda suke da ilimi za su daidaita da wadanda ba su da ilimi?".

Kuma ya ce:

{ ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻳَﺨْﺸَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻣِﻦْ ﻋِﺒَﺎﺩِﻩِ ﺍﻟْﻌُﻠَﻤَﺎﺀُ { ‏[ ﻓﺎﻃﺮ : 28 ]

"Malamai ne kawai suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa".

Annabi (s.a.w) ya ce:

ﺇﻥ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﻭﺭﺛﺔ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ

"Lallai Malamai magada Annabawa ne".

Shaihul Islami yana bayanin matsayin Malamai da hakkinsu a kan Musulmai sai ya ce:

ﻳﺠﺐ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺑﻌﺪ ﻣﻮﺍﻻﺓ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ ﻣﻮﺍﻻﺓ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻛﻤﺎ ﻧﻄﻖ ﺑﻪ ﺍﻟﻘﺮﺁﻥ ﺧﺼﻮﺻﺎ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻫﻢ ﻭﺭﺛﺔ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ، ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺟﻌﻠﻬﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻤﻨﺰﻟﺔ ﺍﻟﻨﺠﻮﻡ ﻳﻬﺘﺪﻯ ﺑﻬﻢ ﻓﻲ ﻇﻠﻤﺎﺕ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺒﺤﺮ ﻭﻗﺪ ﺃﺟﻤﻊ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﻫﺪﺍﻳﺘﻬﻢ ﻭﺩﺭﺍﻳﺘﻬﻢ ﺇﺫ ﻛﻞ ﺃﻣﺔ ﻗﺒﻞ ﻣﺒﻌﺚ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻓﻌﻠﻤﺎﺅﻫﺎ ﺷﺮﺍﺭﻫﺎ ﺇﻻ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﻓﺈﻥ ﻋﻠﻤﺎﺀﻫﻢ ﺧﻴﺎﺭﻫﻢ؛ ﻓﺈﻧﻬﻢ ﺧﻠﻔﺎﺀ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﻓﻲ ﺃﻣﺘﻪ ﻭﺍﻟﻤﺤﻴﻮﻥ ﻟﻤﺎ ﻣﺎﺕ ﻣﻦ ﺳﻨﺘﻪ ﺑﻬﻢ ﻗﺎﻡ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺑﻪ ﻗﺎﻣﻮﺍ ﻭﺑﻬﻢ ﻧﻄﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺑﻪ ﻧﻄﻘﻮﺍ .

ﻣﺠﻤﻮﻉ ﺍﻟﻔﺘﺎﻭﻯ ‏( /20 231 - 232 )

"Ya wajaba a kan Musulmai su jibinci Muminai bayan jibintar Allah da Manzonsa kamar yadda Al- Qur'ani ya fada, MUSAMMAN MALAMAI WADANDA SU NE MAGADA ANNABAWA, wadanda Allah ya sanyasu a matsayin taurari da ake shiryuwa da su a cikin duhun doron kasa da cikin teku. Hakika Musulmai sun yi Ijma'i a kan shiriyarsu da iliminsu, saboda kowace al'umma kafin aiko Annabi Muhammad (s.a.w) malamanta su ne mafi sharrinta sai al'ummar Musulmai kawai, su kam Malamansu su ne zababbunsu, saboda su ne halifofin Manzon Allah a cikin al'ummarsa, masu raya abin da ya mutu na Sunnarsa, da su Al-Qur'ani ya tsayu kuma da shi suka tsaya, da su Al-Qur'a ya yi furuci kuma da shi suka yi furuci".

Saboda haka abin da muke gani na sukan Malamai masu raya Sunnar Manzon Allah (s.a.w) da zaginsu da aibanta su, musamman in ya zama daga wajen jahilai to ya fita daga fagen hankali.

Saboda haka, lallai hakkin malamai a kanmu shi ne; girmamawa da soyayya da jibinta tare da kare hakkinsu da matsayinsu daga mabarnata, masu nufin rusa Addini ta hanyar zubar da wadanda suke dauke da shi wato Malamai.

Allah ya kara daukaka Malamanmu na Addini, halifofin Manzon Allah wajen raya Sunnarsa.

Continue reading...

SHIN WANDA YA YI SALLAH BABU ALWALA KAFIRI NE ?

*SHIN  WANDA YA YI SALLAH BABU ALWALA KAFIRI NE ?*


*Tambaya*


Assalamu Alaikum  dan'uwa kuma malamina ga tambaya naji wata fatawa wacce ba ni da ilimi akanta, wai idan mutun ya yi sallah babu Alwala wai hukuncinsa sai ya sake kalmar shahada ta shiga musulunci,  menene ingancin wannan maganar ? Allah ya taimaka Amiin.


*Amsa* 


Wa alaikum Assalam To malam wannan maganar ta shahara a  wajan mutane, saidai a wajan malamai yin sallah babu alwala ya kasu kashi biyu : 

Idan ya aikata, amma bai halatta hakan ba, ya san ba daidai ba ne, kamar ya aikata saboda  kasala, wannan kam bai kafirta ba, saidai ya aikata babban zunubi.

idan ya aikata yana mai halatta hakan, ko kuma saboda izgilanci ga addini,  sannan  ba jahili ba ne, ba shi kuma da wani ta'awili, tabbas wannan aikin kafirci ne, har ma malamai da yawa sun hakaito ijma'i akan kafircin wanda ya yi hakan, saboda akwai karyata shari'a  a ciki, da kuma wulakantata .

Allah ne mafi sani


Duba : Almajmu'u na Nawawi 2\84  da Minhajussunah 5\204.


*Amsawa*✍🏻


*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*


11/12/2014

Continue reading...

ZAN IYA RIKE HANNUN BUDURWATA?

*_ZAN IYA RIKE HANNUN BUDURWATA?_*



                        *Tambaya:*

Malam Ya Hukunchin Wanda ya rike Hannun wata mace Kuma ba matarsa ba ce, amma Budurwarsa ce?



                            *Amsa:*

Wa'alaikumus salam, Bai hallata mutum ya rike hannun wacce ba muharramarsa ba, kuma ba matarsa ta aure ba. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance ba ya Musafaha (hada hannu) da mata yayin da zai musu mubaya'a, yana yi musu mubaya'a ne da Magana, kamar yadda ya tabbata a hadisi.


Taba hannun budurwa hanya ce da take kaiwa zuwa ga Zina saboda yana tayar da sha'awa, Allah Madaukaki ya haramta kusantar zina a aya ta 32 a suratul Isra'i, Zina tana daga cikin manyan zunuban da babu kamar su bayan shirka da Allah.

Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas Allah zai kiyaye shi, wanda ya bı son zuciyarsa, to Allah yana nan a madakata.                 


Allah ne mafi sani.


20/7/1437

28/4/2016


Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

FALALA GUDA 10 GA WANDA YA HARDACE ALQURANI MAI GIRMA

*FALALA GUDA 10 GA WANDA YA HARDACE ALQURANI MAI GIRMA.*

Hakika babu wani abu da zuciya zata hardace mafi falala da daukaka ta sami matsayi mafi girma kamar hardace maganar Allah ,alqurani shine yake raya zuciya ya sanya ta samu nitsuwa da rabauta anan duniya da lahira,hardace alqurani ba karamar falala bace da matsayi wanda babu wanda yashan iyakar falalar da matsayinsa sai Allah,amma ga kadan daga cikin falalar guda goma;-

*1-Allah yayi yabo na musamman ga bayinsa masu hardace littafinsa alqur'ani,sai Allah yace:*

( ﺑﻞ ﻫﻮ ﺁﻳﺎﺕ ﺑﻴﻨﺎﺕ ﻓﻲ ﺻﺪﻭﺭ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﺃﻭﺗﻮﺍ ﺍﻟﻌﻠﻢ ).

*2-Ana daukaka daraja da matsayin wanda ya hardace alqurani acikin aljanna.*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

((Za'ace ga ma'abucin alqurani karanta ka rera kamar yadda kake karantawa a duniya,domin matsayinka a aljanna yana tsayawa akan ayar karshe da ka karanta).*

@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .

*3-Ana sanyawa Mahardacin alqurani kayan ado na karama da yardar Allah agareshi.*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

*(Alqur'ani zaizo a ranar alqiyama,sai yace: ya Ubangiji kayi masa ado wanda ya hardaceni, sai a sanya masa kambi na Karama,sannan sai Alqurani yace,ya Ubangiji ka kara yi masa ado,sai a sanya masa kayan ado na karama,sai Alqurani yace ya Ubangiji ka yarda da shi,sai ace da mahardacin alquranin karanta ka rera kana da kyakkyawan aiki ga kowace aya).*

@ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .

*4-Mahardacin Alqurani yana tare da tawaga ta Mala'iku ma'abuta karamci da daukaka.*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

*(Misalin wanda yake karanta alqurani yana mai hardacesa, yana tare da tawagar Mala'iku Ma'abuta karamci da daukaka awajan Allah).*

@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .

*5-Wadanda sukayi kowa hardar Alqurani su sukafi cancanta da limanci a cikin al'umma.*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

*(Wanda zai limanci mutane shine wanda yafi so karatun littafin Allah......).*

@Muslim

*6-Mahardata alqurani sune ma'abuta kwamitin Shura"wato masu tattawa abinda za'a zartar ga al'umma".*

Daga Ibn Abbas R.A yana cewa:

*"Mahardata alqurani sune yan majalissar sayyadina umar kuma sune masu bashi shawara....".*

@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .

*7-Mahardata alqurani su ake fara gabatarwa awajan binnewa a qabari.*

Annabi s a.w ya kasance yana hada tsakanin mutum biyu a qabari ga wadanda sukayi shahada a yakin Uhudu,sai yace:

(Wa yafi yawan hardace surar alqurani?) Sai ya fara gabatar da shi acikin qabari".

@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ .

*8-Mahardata alqurani sune mutanan Allah kuma zababbun bayinsa.*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

(Lallai Allah yana da mutanansa zababbu daga cikin mutane, ma'abuta alqurani sune mutanan Allah zababbansu).

@ ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .

*9-Ku riqa girmama Mahardata alqurani saboda girmamasu yana cikin girmama Allah.*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

*(Lallai yana cikin girmama Allah girmama wanda yayi furfura daga cikin musulinci,da mahardacin Alqur'ani,wanda baya karkacewa da alquranin...... da girmama shugaba mai adalci).*

@ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .

*10-Wuta bata qona mahardata alqurani a ranar alqiyama idan sun mutu da imani.*

Manzon Allah s.a.w yana cewa:

*(Da alqurani zai kasance acikin wani abu to da wuta bata kona saba).*

@ ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ .

*Abinda ake nufi da ace akwai wani abu da yake tare da alqurani da wuta bata konasa ba saboda albarkar alqurani,to ina ga mai imanin da yake jibintar alqurani??.*

@ ﺍﻧﻈﺮ : ﻓﻴﺾ ﺍﻟﻘﺪﻳﺮ .

Wannan shine mafi fatan dukkan wanda ya hardace alqurani a zuciyarsa kuma ya mutu da imani wuta bazata konasaba.

@ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺃﺣﻤﺪ - ﺍﻵﺩﺍﺏ ﺍﻟﺸﺮﻋﻴﺔ .

Allah ne mafi sani.

*Allah ka sanyamu cikin bayinki ma'abuta alqurani da hardarsa da aiki da shi,kuma ka sanya mu cikin wadanda alqurani zai cece su a gobe alqiyama.*

Continue reading...

IZALA ta kaddamar da taron koyawa Al'umma sana'oin dogaro da kai

IZALA ta kaddamar da taron koyawa Al'umma sana'oin dogaro da kai.

Daga Baffa Maina Hadejia

Kungiyar wa'azin Addinin Islama ta (JIBWIS) reshen jihar jigawa, Ta bude taron koyawa matasa maza da mata sana'oin da zasu dogara da kansu.

Da yake bayani yayin bude taron Shugaban kungiyar na jaha, Malam Abubakar Jibrin Hadejia, yace kungiyar ba iya wa'azi ta tsaya ba, Tana shirya irin wanna taruka domin zakulo matasanmu a koya masu sana'oin da zasu dogara da kansu, Wanda wannan ne na farko da, kungiyar ta fara kuma zataci gaba insha Allah.

Inda ya karkare da, Inda kungiyar taci gaba da irin wanna za'a kawo karshen shaye-shaye daya addabi matasanmu maza da mata.

Shima Shugaban Kwamittin Shirya taron Sheikh Dr. Abdul'qadir Saleh Kazaure yayi bayanin irin sana'oin da za'a koya wadanda suka hada da, GYARAN WAYAR HANNU, SARQA DA DANKUNNE da sauransu, Inda yace zuwa yanzu kowace karamar hukuma a fadin jihar Jigawa ta aiko da wakilanta kuma za'aci gaba da koyar dasu har zuwa kwana biyar din da'aka tsara insha Allah.

Taron yasamu halattar Shugababanin kungiyar a mataki na jaha da kananan hukumomi da sauran jama'a

Allah ya sakawa dukkanin wadanda suka temaka da Alkhairi Amin.

JIBWIS JIGAWA

11/December/2018.

Continue reading...

JINI YANA ZUBO MINI, BAYAN CIKINA YA KAI WATA HUDU?

*_JINI YANA ZUBO MINI, BAYAN CIKINA YA KAI WATA HUDU?_*

*Tambaya:*

Assalamu Alaikum Dr dan Allah inada tambaya akan matar da keda ciki yakai wata hudu sai jini ya rinka xubar mata daga baya kuma sai ya dauke bayan kwana guda ko biyu yakan iya dawowa ko bayan wasu awoye shin ya hukuncin sallar ta? xata jinkirta sallah sai jinin ya dauke ko xata rika yin wanka duk sanda ya dauke tayi rankon sallolin baya ne.

Nagode

*Amsa:*

To 'yar'uwa mutukar cikin ya kai wata hudu kuma jinin da yake fita yana hade da ciwon haihuwa, to ya zama jinin biki, kuma zai hana sallah, amma Idan babu ciwon haihuwa to mutukar ya zo da sifar jinin haila (baki ko karnı) to zai zama haila, tun da a zance mafi inganci mai ciki tana iya yin haila.

In ya fita daga wadannan biyun zai zama jinin cuta ta yadda ba zai hana sallah ba, in har jinin kusa-kusa yake fita, za ki iya jinkirta salloli, sai ya dan tsagaita, sai ki rama sallaolin da aka yi su kina da tsarki, saboda addinin musulunci addini ne mai sauki, babu kunci da damuwa a cikinsa, kamar yadda aya ta karshe a suratu Al-hajj ta yi bayanin haka.

Allah ne mafi Sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA

*_WURAREN DA YA HALATTA A SAKI MACE MAI HAILA_*

*Tambaya*

Akaramakallah na ji an ce haramun ne a saki mace mai haila, to amma wani lokacin za ka ga kun samu rashin jituwa da matarka ta yadda baza ka iya jiran lokacin tsarkinta ba, to malam akwai wasu lokuta ne da aka halattawa mutum ya saki matarsa ko da tana haila?

*Amsa*

To dan'uwa tabbas Allah ya yi umarni da kar asaki mace sai tana da tsarki kamar yadda yake cewa "Idan za ku saki mata to Ku sake su afarkon iddarsu) ma'ana a tsarkin da baku take su ba, Addalak aya ta: (1) saidai akwai wurare guda uku da ya halattta a saki mace mai haila:

*1*. Idan sakin ya kasance kafin ya kadaita da ita ko kafin ya sadu da ita, to anan ya halatta ya sake ta tana haila.

*2*. Idan ta yi hailar ne tana da ciki.

*3*. Idan ya sake ta ne bayan ta fanshi kanta, to anan ya halatta ko da tana haila, saboda Annabi (S.A.W) bai tambayi matar Thabit ba shin tana haila ne ko tana da tsarki, lokacin da zata yiwa mijinta kul'i, kamar yadda Bhukari ya rawaito ahadisi mai lamba ta: 5273.

Duba: Dima'uddaabi'iyya shafi na: 33.

In ban da wadannan wurare, to bai halatta a saki mai haila ba, kuma in har an sake ta, to sakin bai auku ba a wajen wasu malaman.

Allah shine mafi sani.

21/04/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Continue reading...

GANIN ALLAH A LAHIRA - Dr. Kabir Asgar ( Hafizahullah )

GANIN ALLAH A LAHIRA

Al-Imamu Muslim da wasunsa sun ruwaito hadisi daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: “An tambayi Manzon Allah (SAW) cewa ko za mu ga Ubangijinmu a ranar tashin alqiyama? Sai ya ce: Shin kuna yin turereniya wajen kallon rana da rana tsaka sanda ba girgije? Sai suka ce: A’ah. Sai ya ce: Ko kuna turereniya wajen kallon farin wata a daren haskensa sanda babu girgije?. Sai suka ce: A’ah. Sai ya ce: “Na rantse da Allah wanda raina ke hannunsa ba za ku yi turereniya ba a wajen ganin Allah ba sai gwargwadon turereniyar da kuke yi wajen kallon wata ko rana. Sannan ya ce: [Ranar alqiyama] Allah zai gana da bawa, sai ya ce masa: Kai wane! Ashe ban girmama ka ba? Ashe ban ba ka shugabanci ba? Ashe ban ba iyali ba? Ashe ban ba ka damar sarrafa dawaki da raquma ba? Ashe ban ba ka damar zama jagora ba? Ashe ba kai ne ka ke dauke daya bisa hudun ganima ba? Sai [bawa] ya amsa da cewa: An yi haka. Sai [Allah] ya ce masa: To dama kana tsammanin gamuwa da ni? Sai [bawa] ya ce: A’ah! Sai [Allah] ya ce masa: ba ruwana da kai kamar yadda ka yi halin ko-in-kula da ni.

Sannan sai Allah ya gana da [mutum] na biyu, sai ya ce masa: Kai wane! Ashe ban girmama ka ba? Ashe ban ba ka shugabanci ba? Ashe ban ba iyali ba? Ashe ban ba ka damar sarrafa dawaki da raquma ba? Ashe ban ba ka damar zama jagora ba? Ashe ba kai ne ka ke dauke daya bisa hudun ganima ba? Sai [bawa] ya amsa da cewa: An yi haka. Sai [Allah] ya ce masa: To dama kana tsammanin gamuwa da ni? Sai [bawa] ya ce: A’ah. Sai [Allah] ya ce masa: ba ruwana da kai kamar yadda ka yi halin ko-in-kula da ni.

Sannan kuma sai Allah ya gana da [mutum] na uku, sai yai masa tambayoyi irin wadanda suka gabata. Sai ya ce: Ya Ubangiji! Na yi imani da kai, na yi imani da littafinka, na yi imani da manzanninka, na yi Sallah da Azumi da Sadaka. [haka] zai ta bayyana alherinsa gwargwadon iyawarsa. Sai [Allah] y ace: Anan ma karyar za ka yi?. [Sai Manzon Allah (SAW)] ya ce: Sa’annan sai a ce da shi: yanzun za a kawo shaidan da zai yi bayani akan ayyukanka. Sai [mutumin] ya fara tunani a zuciyarsa yana cewa: Oh! Ko waye zai zo ya ba shaida kaina? Daga nan sai a rufe bakinsa, kuma a ce da cinyarsa da namansa da qasusuwansa ku yi magana. Sai cinyarsa da namansa da qasusuwansa su yi magana su bayyana ayyukansa, [an yi hakan ne] don a kafa masa hujja. Wannan shine munafiki, wancan kuwa shine wanda Allah yai fushi da shi”.

Rubutawa: Dr. Kabir Asgar

Continue reading...

HUKUMCIN SHAN MAGANIN TAURI !

_*HUKUMCIN SHAN MAGANIN TAURI !

*Tambaya*

Assalamu alaikum Allah ya karawa Dr. Lafiya.

Mene ne hukuncin shan maganin tauri wato Maganin karfe ko kauranci a musulunci ?

*Amsa*

Wa alaikum assalam

Mutukar babu abin da ya sabawa sharia a ciki, ana iya amfani da shi saboda neman kariya, saboda duk mua'amalolin da mutane suke yi, in har ba'a samu nassin da ya haramta ba, to sun halatta saboda Ka'idar: ﺍﻷﺻﻞ ﻓﻲ ﺍﻷﺷﻴﺎﺀ ﺍﻹﺑﺎﺣﺔ .

Da yawa daga cikin magungunan tauri akwai kauce hanya a ciki, akwai wadanda ake barin sallah idan an sha, ka da aje garin-neman-gira a-rasa- IDO.

Mutukar maganin tauri ya kunshi abin da sharia ta haramta, bai halatta ayi amfani da shi ba, Biyayya ga Allah maganin KAU-DA-BARA.

*Amsawa*

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*

25/03/1440

03/12/2018

Continue reading...

HARAMCIN ZUWA WAJAN BOKA KO DAN DUBA

HARAMCIN ZUWA WAJAN BOKA KO DAN DUBA


      Wanene Boka?? 


*A larabci ana kiransa da ALKUHHAAN,boka shine Wanda ikirarin sanin gaibun abinda zai faru nan gaba kuma yake baima mutane labarin abubuwan gaibu wadanda bai faruba sai nan gaba,kamar yace wane zai ci zabe ko wane zai fadi,ko wane zai auri wance ko wani zai saki matarsa*.


Wanene Malamin Duba;

*Da larabci ana kiransa da ARRAF, wato mai duba ko bugon kasa,shine wanda ya baima mutane labarin gurin da wani abu nasu ya bata ko abinda aka sace masu yace yana waje kaza,daga cikin abubuwan mutane da suke bata,yana ikirarin sabin gaibun abun da ya faru*.


Boka da Mai Duba dukkan su kafuraine sun kafirta saboda ikirarinsu akan cewa sunyi tarayya da Allah acikin sanin gaibu bayan Allah yana fadar cewa;

*(Babu wanda ya san ghaibu sai Allah shi kadai)*. 


Kuma saboda kayarda Allah cikin abinda Allah ya fadar cewa babu wanda ya san ghaisu sai shi kadai,amma su suna cewa sun sani

Allah yana cewa

*(قُلْ لَا يَعْلَمُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ ۚ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ)*


Ma'ana;

(Kace babu wanda ya san ghaibu cikin sammai ko kassai sai Allah shi kadai....)

@النمل 65]


*HARAMUNNE ZUWA WAJAN BOKA KO MAI YIN DUBA*


Daga Safiyyah bntu Abi Uzaid daga Daya daga cikin Matan Manzon Allah ﷺ ورضي الله عنهن daga Manzon Allah ﷺ yace:

*(Wanda yaje wajan malamin duba ko Boka,sannan ya tambayesa wani abu kuma ya gaskatsa akansa,baza'a karbi sallolinsa ba na kwana arba'in)*

@رواه مسلم.


Awata riwayar yana cewa;

*(Duk wanda yaje wajan mai yin duba ko Boka,kuma ya gaskata abinda ya fada masa,hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa da Manzon Allah SAW)*

@وفي مسند الإمام أحمد ،وأبو دَاوُدَ والحاكم والذهبي والألباني والترمذي وابن ماجه وغيرهم :


Daga daya daga cikin Matan Manzon Allah ﷺ tace;Manzon Allah  ﷺ yace;

*(Wanda yaje wajan malamin duba sai ya tambaye shi wani abu,baza'a karbi sallarsa ba ta kwana arba'in)*

@أخرجه مسلم[2230].


‏‏

  Allah ne mafi sani


Allah ka karemu da imanin mu baki daya.

Continue reading...
 

Random Posts

3/random/post-list
X

Contact Form

Name

Email *

Message *